Posts

Showing posts with the label kissa

My picts

Image
Rayuwar duniya watarana Sai labari Alpholtawy Alpholtawy

MASHAHURAN MUSULMAI DA SUKA FARA KIRKIRAN AIKIN LIKITANCI A DUNIYA

Kamar yadda nayi bayani a rubutu na farko Wani abin haushi da Turawan yamma na yanzu suke yi shi ne, na boye sunayen Musuluncin waɗannan mutane, suna sa musu nasu na Turanci, wai don a ce su ma nasu ne. Ga kadan daga cikin irin wadannan mashahuran Musulmin da suka fara kirkiro abubuwan da har yanzu ake amfani da su: An ba da duka sunayensu na ainihi da na Turancin da kuma zamanin da suka zo: ~ Muhammad bin Zakariyya Al-Rhazi: Rhazes (865-925AD):Mutumin kasarFarisa (kasar Iran ta yanzu), wanda ya ba da gudunmowar da har a yau ba wanda ya ba da irinta a harkar lafiya. Domin ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya sha kawo bayanai na canjin tunani da hujjoji masu gamsarwa a harkar lafiya. Misali, shi ne wanda ya fara bambance ciwon Agana (mai sa cin zanzana, wanda kuma aka riga aka ga bayanta a yanzu) da Bakon Dauro, wanda duka kwayar cutar birus ce ke kawowa. Shi ne kuma wanda ya kirkiro kayan aikin likita da dama irinsu. Ya rubuta littattafai a kan harkar lafiya fiye da guda dari. Fitacce a...

YIN AIKI DOMIN ALLAH* {1}

*SHEIKH ALBANY DA'AWA GROUP* * Yaku bayin Allah, kusani cewa Allah ba ya karbar aikin bayi sai idan an yi aikin dominsa. Duk wanda ya aikata aiki ya yi tarayya da Allah a cikin wannan aiki, to Allah ya wadatu ga barin karbar wannan aikin, duk kuwa yadda wannan aiki yake da yawa. Allah yana cewa: ( إِنَّا أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ فَاعْبُدِ اللَّهَ مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ 2أَلَا لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ3) [الزمر: ٢ – ٣]. *Haqiqa mun saukar maka da littafi da gaskiya, ka bautawa Allah Shi kadai kana mai tsarkake aiki dominsa. Ku saurara tsarkakakken addini na Allah ne”.* Hakanan yake cewa: (قُلْ أَمَرَ رَبِّي بِالْقِسْطِ وَأَقِيمُوا وُجُوهَكُمْ عِنْدَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ29) [الأعراف: 29] *(Ka ce da su, Ubangijina ya yi umarni da tsayar da adalci. Kuma tsayar da fiskokinku a kowane masallaci. Kuma ku bautawa masa kuna masu tsarkake bauta dominsa).* Ya kuma cewa a wani wurin: (فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ال...

Muhimman Tambayoyi

Tambayoyi Muhimmai Wanda ALLAH yafara Halitta A Mutane Shine....? Mafificin Rana Aranakun sati itace....? Azumin Litinin da Alhamis Suna Rukunin....? Sallama Yayin Idar da Sallah Rukunine na....? Wanke mamaci Rukunin sa Shine....? Asuwaki a Alwala Matsayinsa....? Cin Abinci da Hannun dama umarnin Na....? Mutunci Yana sa mutum Yasamu....? Azumin Alhamis da Juma'a Matsayin sa shine....? Farillan Alwala guda....? Wanke fuska A Alwala matsayinsa Shine....? Niyya A Sallah Matsayinsa Shine....? Niyya a Wankan Gawa Matsayin sa Shine....? Malamin makaranta Aikin sa shine....? Cin Naman Alade matsayin sa amusulunci shine....? Zakkan Fidda Kai Matsayin sa....? Likita Aikinsane....? Salloli nawa Akeyi akullum....? Azumin Ramadan anayinsane....? Tsarki itace....? Wanda Wajiban Wanka guda....? Farillan Wanka....? Sunnonin Alwala guda....? Ranar da aka Haini Annabi Muhammad (S. A. W) shine....? Dare lokaci ne na....? Juriya alamu na....? Ilimi shine....? Za...

HA'DIN KANMU HARYAR TSIRARMU

HADIN KANMU HANYAR TSIRARMUN   Rayuwa ta ishemu Wa’azi Malamai kuji tsoron Allah wajen Karantarwa kada kusa Son Zuciya. Domin tsira da mutuncinku aduniya da tsira da imani aran Qiyama. Dalibai muji tsoron Allah, Mufahimci junananmu Yayin Sa’bani, Kada Muce komai Malam  wane yafada Gaskiya ce, Binciken Yafi Sauraron Mu yawa. Muyi riko da Tsarin Allah Mugirmama junan mu kada Murarraba, Rabuwa A Al’uma fitinace, Yawan jayayya yanasanya Masu Son zuciya yad’a ‘Barna kuma yakan sa Wasu gaba da juna Bisa Rashin Dalili. Mukula Da amanar junan mu gun jaddada Sa’bani, Muyawaita zantawa da juna domin warware Sa’bani mukula da Wadanda ke son tada fitina a Addini Sud’in wawayene kuma jahilai, danganeda Harkokin Addini Basusan komai ba Sai musu da Cinzarafin Malamai. Akowace aqeeda akan iya Samun masu mummunar manufa da Kuma Son zuciya. Babbar matsalar rayuwa Shine aiki da Jahilci, dakuma Son Zuciya. Mu Janye Gaba da juna danganeda bambamcin aqeedah. Meyin hakan Bai fahimci addini ba, Son dun...

MATASA!!! MUKOMA GA ALLAH

 `YAN UWANA MATASA!!! MU KOMA GA ALLAH Rayuwar Matashi abin tausayine, Kana fama da Quruciya Ga kuma bakin Al`uma akanka. Idan za`afadi Damuwar Al`uma dubu, Kaso ´Dari Tasa da Hamsin (950) Na Matasa ne. Qalubale Garemu Matasa, Ban cire kainaba domin nima cikin Quruciya nake. Tabbas Muna Fuskantar Qalubalen rayuwa daga ´Bangaren zamantakewa, Har da Ibada. Saidai Raunin zuciya kuwa ya danganta da Yadda mutum yataso, Wahala ko Qunci, Tarbiyya ko Akasin hakan (Garari), Riskar iyaye da Rai ko Tashin Maraici. Idan Kasamu yin Makaranta Fani'ima (Haka akeso) In MA bakasamu ba Kaidai kada Kabar Neman ilimin Addini Domin Shidin Yalwatacce NE. Ako Ina akwaishi Amma kayi Takatsan_tsan Maluman da Kake Saurara. KADA kabi Maison Zuciya. Dukkan Wadannan Matsololin Rayuwa ce, Kirata Agaremu Shine, Mugane inane hanyar tsira kuma mecece mafita ta rayuwar mu, Ina Muka fito, Ina Zamuje, Me zamu Riska, Ina Tafiyar zata Tiqe? MATASA BAYIN ALLAH NE Kada Mushagaltu da Rudin Rayuwar ...

HA'DIN KANMU HANYAR TSIRARMU

HA'DIN KANMU HANYAR TSIRARMU Fitowa ta Hudu (¡v) Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy Yau zanyi maganane danganeda tasirin Aqidu acikin Zuqatan Mabiya, Lokaci Yanausa Abubuwan Sun Gur'bata Amma kowa gani Yake Shine Akan Tafarkin Gaskiya Dukda Cewar Wasu Abubuwan Mun Tabbatar dacewa Kuskurene Tsantsa, Amma Ginuwa Akan Aqidar damukayi, Shi yahanamu Hawa Kan Shari'ar Asali, Duk dacewa Itace tafi Zama Matsera garemu A Lahira. Misali; Zuwan Izala tafito Da gyararraki A Addinin Musulunci Sosai, Amma Ganin cewa idan Munbita Menene makomar Iyayenmu Shiyasaka Dayawan mu Suka Kauracemata, Saidai kuma Ana Samun Masu Son Zuciyar dasuke Jifanta da Munanan Qazafi, da Isgili, (da Sunan Cewa Anzo da Sabon Addini) Wadda Azahirin Gaskiya Bahakan bane, Alkawarin ALLAH ne Yazo Nacewar Duk Sadda Lokaci Yayi Nisa ALLAH Zai Tada Wani Wanda Zai Jaddada Koyarwar Addini Yakuma 'Dabbaqa Shari'ar Masoyin Sa Annabi Muhammad (s. a. w). Tabbas Dukkan Wanda yazo da Sabon Al...

AL'UMAR MUSULMI AYI HATTARA

AL'AMARIN SA'IDU MAIKWANO MAI DA'AWAR 'YAN BAZATA ABIN TSORO NE      Daga Datti Assalafy  Allah Ya jarrabi Musulunci a Nigeria da wani irin Malami mai suna Sa'idu Aliyu Maikwano wanda yake da'awar wai Salafiyyah a Gusau jihar Zamfara, yana kafirta Manyan Malamai tare da bidi'antar dasu, yana kuma jifansu da kalmar khawarijanci, wato halasta zubar da jininsu Na saurari tsokacin da Maikwano yayi akan Khadimul Qur'an Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu (Rahimahullah) da kuma su Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar Izala na duniya Sa'idu Maikwano ya kafurta Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu, har ma ya soki Sheikh Abdullahi Bala Lau don ya yiwa marigayi Sheikh Isyaka Rabi'u addu'ah na samun rahamar Ubangiji Sa'idu Maikwano yace Sheikh Isyaka Rabiu kafuri ne, kuma mushriki, wai Sheikh Isyaka Rabiu yayi hidima wa kafurci da shirka ne kafin ya mutu, wai bai kamata Izala ta masa addu'ah ba Na girgiza matuka da jin wannan munanan kalamai da suka ...

NASIHA

  KA ZAMTO TAMKAR BAKO A DUNIYA. - "Duniya ba gidan dauwama bace ita gidan ci-rani ce, kada ka bari ruɗun cikinta ta yaudare ka yakai ka ga saɓawa Allah maɗaukakin sarki, domin lallai duk soyayyar da duniya take nuna maka a yanzu, to wallahi watarana sai ta sake ka" - "Kullum kada ka sake ka mayar da wannan duniyar tamkar wata madauwamar ka, babban mai hankali shine wanda yake yiwa duniya tamkar gidan ci-rani, wato gidan wani ɗan zama ne ƙan-ƙani ba mai dogon lokaci ba, da zarar ka gama rayuwarka sai ka tafi ka barta"  - "Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya bamu shawara da cewa "mu zamto a wannan duniyar tamkar baƙi ko kuma masu ƙetarar hanya" wato irin mutanen da basa sakankance wa a duk inda suka je burinsu kawai suyi abinda ya kawo su su koma inda suka fito, to mu kuma bautar Allah ce ta kawo mu duniyar, da zarar rayuwar mu ta ƙare zamu koma ga mahaliccin mu Allah"

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYAS

 Tarihin Shehu Ibrahim Inyas  Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy    Dafarko dai Mai Karatu Zanfara da sunan ALLAH ﷽ Mun manta da tarihi Saikawai Labaran Duniya dakuma Kallace_Kallacen Film, Har wasu daga cikin Daliban Wannan bawan Allah din Sheikh Ibrahim Inyas mabiyansa Na Tijjaniyya Da Faidha. Basusan Tarihin Nasaba Saidai kawai Sunsan Littattafansa Wadanada yarubuta Kamarsu Kashiful Ilbasi, Dama Dawawinu_Ssittah. dama Sauran Littattafansa na Abyat.                              ﷽ اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎ Dafarkodai Sheikh Ibrahim inyas dai Asalinsa dan kasar Sanganiyane Agarin Kaulaha. Bayan Rasuwar Mahaifinsune alokacin da Sheikh Amadu Tijjani yazo yimasu Ta'aziyya, Sai Yanemi da da abashi dakin Soro domin Larabawa basa juran Zafi.      Yayansa Muhammadu Khalifa wanda Shine Magajin Mahaifinsu a fannin Khalifanci na Wannan Zawiyyan, Sai yace dashi ga ...

TARIHIN SAHABBAI Kashi na daya 001

  TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR SADDIK ALLAH YA YARDA DA SHI, (manzon Allah S. A. W) "yace ya Abubakar kai ne farko wanda zai shiga Aljanna daga al'umma ta" Sayyidina Abubakar shi ne Abdullahi dan Abu kuhafatu " usman" usman dan Amir dan Amir dan ka"abu dan sa"adu da taimu dan murratu dan ka"abu dan lu"aayu, bakuraishe. Bataime. Nasabarshi ta hadu da manzon allah ta wajan murratu dan ka"abu kakansu na biyar. Sunan shi a lokacin jahiliya "Abdul ka" aba" daya musuluta sai manzon allah ( S. A. W) yakara shi "Abdullahi" An yi mishi alkunya da Abubakar saboda riganyenshi wajan dabi"antuwa da kyamara halaye. Kuma an yimasa lakabi da saddik sabo da saurin bayar da gaskiyar shi ga dukkan abunda manzon allah (S. A. W) ya fada kuma manzon allah (S. A. W) yakara shi da "Atiku" shine mutumin da yafara musuluta a manyan. Shi ne mutum na farko, da ya fara kira zuwa ga addinin musulunci. Bayan manzon Allah Annabi Mu...

MATSALAR AQEEDAH

 GASKIYA AKWAI MATTSALA!!!! Sau nawa kake zama domin Bincike ko sauraron Yadda zaka gyara Ibadarka?????          Sau dadama idan na kadaita sai nayita tunani dan ganeda lammarin gudanar addini agun wasun mu. Zakaji mutum nakiran kansa musulmi amma farillan alwala ma bai sani balle in ta 'baci ya gyara farillan sallah ma bai saniba balle inyayi Rafkanuwa yagyara. Ko na wanka ballema ilimin gyaransu.     Wayyoooni duniya ina zaki damune kowa kagani abinci kawai yake nema kokuma yadda zai huta ko yadda zaiji dadin duniya gaba. Saidai kash itakuma tafiyarnan da take gaban mu batta da rana. Kawai zuwa take kwatsam kara zube ba zato ba tsammani.     To taya zamu tara guzirin komawa ga mahaliccin mu domin samun hujja garemu aranar sakamako?     Ansa     Mukoma munemi ilimin addini mugyara ibadu da mu'amalarmu kafinnan musami hanyar tsira. Wani abin ban takaici shine yawanci mukan jahilci lammarin addini bawai don rashinsaba ...

MUSULMI GA SAKO

 MUSULMI ATASHI AKAFA DAULA DAN SAMUN INGANTACCEN RAYUWA inji Shahararren malamin salafiyyannan Sheikh Muhammad Adam Albany Zaria.    Hakika shugaba yayi wadannan maganganu da shawarwarin agurare Ma bambanta da majalisai dadama. Domin nuni garemu ga hanyar tsira. Dakuma koyi da magabata. Don samun rayuwa Mai inganci, da zamantakewar rayuwa Mai tsafta. Ba kamar yadda wasu ke daukar zancen awata mahanga. Da tunani irinta miyagun mutani ba.  Ga zancen malam;  Tsokaci kan batun malam:     Saidai haryanzu banji wani shahararren mutum daga cikin malamai ko shugabanni daga cikin musulmiba wanda ke karfafa Zancen. Duk da cewar maganan maganice na ciwon dayake damun musulmin duniya baki daya. Saidaima wasu daga cikin miyagun mutane dasuke fassara zancen da wani salo nadaban, tayadda suke kokarin cire ma'anar maganan na hakika su shigoda wani al'amari nadabam.      Gadai Maganan da malam yayi; Mal. Yace ''Yakamata musulmi su kafa daula Dan gujewa ...

QALUBALE GA RAYUWAR 'YAN MATA

 📝  ✍️ ISMAIL HUSSAINI ADAM SMART DAN AREWA    ******* GABATARWA ******* Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu mai karatu.        Zanyi wannan rubutunne don nuni zuwaga yan uwana maza, domin kusan wa zaku auro ku kawo cikin gidanku, amatsayin abokiyar zama. Mata kuma su san dawa zasuyi qawance don gudun faďawa akomar halaka. Inda hali kutsaya kukaranta gabaki ďaya, domin zaka/zaki k'aru kuma inshaa Allahu zaku rabauta da waďannan zantuka nawa.       Ina bukatan addu'arku Allah ya haskaka qabarin mahaifina, dana mai karatu idan kuma suna raye, Allah yasa mugama dasu lafiya yakuma basu rabon cikawa da imani. Allah ka albarkaci rayuwar lahaifiyata da ayyukan alkhairi daku mumaďin gabaki ďaya. ******** 'YAN MATAN JAMI'A ********    Allah sarki rayuwarsu gwanin birgewane, saidai kuma abin tausayine awani bangaren, tayadda zaka samesu mafi yawancinsu akwai tsaftar jiki dana tufi. sannan sun san yakamata matuka, Saidai was...

NASIHOHINMU AYAU

 MU LE'KA MAKABARTA )> . AWANNAN GURIN- Wasu Rahama Suke Sha,  Wasu Kuma Dũkan Tsiya Suke Ci. . AWANNAN GURIN- Wasu Sun 'Kosa A Tashi Alqiyamah, Sabo da Ni'mar da Suka hango A Gidansu Na Aljannah. Wasu Kuma Roko Sukeyi Kada A Tashi Qiyamar Sabo da Azabar da Suka Hango Tafi Wacce Suke Ciki Bala'i, . AWANNAN GURIN- Mutanan Kirkin da Ke Cikinsa dana Banzan dake Cikinsa, Suna yin Nadamar Lokacin da Sukayi Hasarar Sa, . NA KIRKIN CUKINSU: Suna Yin Nadamar Ina ma Ace Gaba daya Lokutansu Sun Qarar dashi Akan Bautar Allah, Sabo da Sakamakon Alkairin Aikinsu da Suka fara Gani. . NA BANZANSU KUMA: Suna Yin iihu, da Kururuwa, da Cizon Yatsa, da Takaicin Qarar da Rayuwarsu da Sukayi Akan Aikin Banza. . NI, DA KAI AYANZU- Zãbi ya Rage Agremu, ga Irin Rayuwar da Muke Son yi Bayan Mutuwar Mu, . Ko dai Mu Zabi Rayuwar da Mala'iku Zasu yi ta Jibgan Mu, Kunamu da Macizai Suyi ta Saran Jikin Mu. Ko Kuma Mu Zabi Rayuwar da Zamu Samu Nishadi da Natsuwa Acikin Qabarin Mu. . Kada Dai M...

KAZAMO MAI YAFIYA

 KA YAFEWA MUTANE! - "Sau da yawa ɗaukar fansa akan abinda akayi maka na kuskure yakan zo da nadama tun a wannan duniyar, koda kuwa ganganci akayi maka to lallai yafiya itama alkhairi ce gareka har zuwa ranar lahira" - "Kayi ƙoƙari ka zamto mai yawan yafiya da kawaici ga jama'a, bayyanar da yafiya da nuna tausayin ka ga jama'a, shine zaisa kaima Allah ya yafe maka, amma da zarar ka zamto mara tausayi da imani ga bayin Allah, shima Allah sai ya cire tausayinsa daga gareka ya barka da baƙin halinka, ƙarshe kuma kaje ka haɗu dashi yayi maka hisabi abisa abinda ka aikata ga bayinsa anan duniya" - "Ka yafewa mutane waɗanda suka yi maka ba daidai ba koda kuwa su ɗin basu nemi yafiyar ka ba abisa laifin da suka aikata maka, riƙe fushi acikin zuciyarka babu abinda zai haifar maka face cutarwa, da zarar ka yafe, kaima zaka sami sauƙin raɗaɗin abinda suka yi maka na laifin, gwargwadon riƙonka dasu acikin zuciyarka gwargwadon cutarwar da zakayi ga zuciyarka, amma ...

SUWAYE AHLUSSUNNAH

 MAFAKAR SUNNAH AYAU!!!         Haqiqah Babu batun Sonkai, Salafawa da 'yan izala sune ke da'awar sunnah Haqiqanin ta zallar madarar sunnah babu gauraye.  Dalilin wannan rubutu nawa: Shine nuna mecece koyarwar aqeedar sunnah. Da manufar Izala da Salafawa akan sunna dakuma mecece asalin haqiqanin aqidar sunnah    ********MECECE AQIDAH******** Aqidah:  amahangar Arufai (Malamai)_ wata hanyace wacce mutane suka kebance yadda zasu yi addini karkashin wata mazhaba bisa fahimtar magabata na farko, Bugu da kariaqidah takasance abace wacce take a aikace da furincin baka banda qudirin zuci. Ma'ana Azuci ni musulmine kuma nayarda da dukkan shika_shikan musulunci ina aikatasu amma bisa mazhabar malikiyya. To idan hakane madogarata bani da Ikon tilasta maibin mazhabar shafi'iyyah ko  ko hanafiyya. Bani damar cewa sai sunbi Hambaliyya  Idan mukayi duba danganeda yanayi nayanzu yadda rayuwa tashige rudani yadda Ake kawo abubuwa daban daban aciki...

SUNNAH TAFARKIN TSIRA

MAFAKAR SUNNAH AYAU!!! Daga 🖊📝Ismail Hussaini Adam +2349047958802 Haqiqah Babu batun Sonkai, Salafawa da 'yan izala sune ke da'awar sunnah Haqiqanin ta zallar madarar sunnah babu gauraye. Dalilin wannan rubutu nawa: Shine nuna mecece koyarwar aqeedar sunnah. Da manufar Izala da Salafawa akan sunna dakuma mecece asalin haqiqanin aqidar sunnah ********MECECE AQIDAH******** Aqidah: amahangar Arufai (Malamai)_ wata hanyace wacce mutane suka kebance yadda zasu yi addini karkashin wata mazhaba bisa fahimtar magabata na farko, Bugu da kariaqidah takasance abace wacce take a aikace da furincin baka banda qudirin zuci. Ma'ana Azuci ni musulmine kuma nayarda da dukkan shika_shikan musulunci ina aikatasu amma bisa mazhabar malikiyya. To idan hakane madogarata bani da Ikon tilasta maibin mazhabar shafi'iyyah ko ko hanafiyya. Bani damar cewa sai sunbi Hambaliyya Idan mukayi duba danganeda yanayi nayanzu yadda rayuwa tashige rudani yadda Ake kawo abubuwa daban ...

MATSALAR TSARO A NIGERIA Post 1 (!)

BABA YAKASA MATASALAR TSARO AKASATA Leave the issue that he has doing well kawai muce Baba yakasa. Abin na Bu'katar Tunani ne. Idan zamuyi adalci wa kanmu kuma mufadi gaskiya, Wallahi matsalar tsaro a nigeria, kasawar kayan aikin Jami'an tsaron governati ce. bawai ina nufin bata da karfin yaqarsu ba, kawai taki tayi abinda yadacene dan ganeda lamarin. Tahanyar nazari dakuma bawa jami'ai kayan aiki dakuma da nauyi da bada tallafi ga iyalin duk wanda yarasa Ransa akan yaki da 'Yan ta'adda. Kullum al'amuran kara rikicewa yakeyi, Tambayata anan itace: Waishin su 'yan ta'addannankam aljanune, kokuma aljanune suke basu kayan aikine. Wadanda dasuke amfani dasu, Kama daga ci shansu har zuwa makamai dasuke amfani dasu, dakuma man da suke sakawa a ababen hawansu. da'akwai alamar tambaya anan gun! Shin anya acikinmu babu masu daukan nauyinsu? kokuma makiyanmu ne ke basu mafaka da tallafi? Idan akwai kuwa suwaye wadannan mataimakan nawu? Kuma...

MATSALAR TSARO AKASATA post 2

MATSALAR MANYANMUNE!!  Matsalar tsaro A'kasata Fitowa ta biyu  (!!) ✍️Ismail Hussaini Adam Matsalar tsaro akasar Nigeria abune mai matukar wuya amaganceta da hanzari, Domin Al'amuran Sun jima Da Cakud'ewa cikin mummunar qaddara da muka samu kanmu aciki musanman Mu Al'umar Arewa. Ansamu akasi tahanyar wasunmu suna goyon bayan ta'addanci aboye, bincki da akeyi ana kin bayyana gaskiya, Shine babban Al'amarin daya gur'bata Al'amuran tsaro A'kasarnan. Wai sai ace anrufa asiri akwai 'yan Alfarma. Shifa d'an ta'adda, ko mai goyon bayan ta'addanci, Koda uwarsace data haifeshine yasan zata fallasheshi, Wallahil aziim zai aikata lahira, komai Son da takemai, balle jami'an tsaro ko Masu fad'a aji na gari Wad'anda aganinsu sune Cikas d'insu aharkar dasuke ciki. Yazama wajibi akan hukumomi, Da Shuwagabannin Al'uma ta ayyadar da hukunci, akan dukkan wani mai laifi data kama, takuma yi bincike akan dukkan wanda take zargi da ta...