MATSALAR AQEEDAH
GASKIYA AKWAI MATTSALA!!!! Sau nawa kake zama domin Bincike ko sauraron Yadda zaka gyara Ibadarka????? Sau dadama idan na kadaita sai nayita tunani dan ganeda lammarin gudanar addini agun wasun mu. Zakaji mutum nakiran kansa musulmi amma farillan alwala ma bai sani balle in ta 'baci ya gyara farillan sallah ma bai saniba balle inyayi Rafkanuwa yagyara. Ko na wanka ballema ilimin gyaransu. Wayyoooni duniya ina zaki damune kowa kagani abinci kawai yake nema kokuma yadda zai huta ko yadda zaiji dadin duniya gaba. Saidai kash itakuma tafiyarnan da take gaban mu batta da rana. Kawai zuwa take kwatsam kara zube ba zato ba tsammani. To taya zamu tara guzirin komawa ga mahaliccin mu domin samun hujja garemu aranar sakamako? Ansa Mukoma munemi ilimin addini mugyara ibadu da mu'amalarmu kafinnan musami hanyar tsira. Wani abin ban takaici shine yawanci mukan jahilci lammarin addini bawai don rashinsaba ...