TARBIYYA Fitowa ta biyu
MATAKAN TARBIYYA Daga. Alqalamin Ismail Smart Dasunan ALLAH Mai RAHAMA Mai JINKAI. Haqiqa tarbiyya dolece a addinin mu na musulunci musan man ma na iyalanka/ki Domin ALLAH MADAUKAKI yana cewa: ﷽ یا أیهاالذین آمنو قو أنفسکم وأهلیکم نارا وقودها الناس والحجارة Awannan aya ALLAH yayi umarni ga Muminai dasu Kare kansu da iyalansu daga wata wutta Wanda yakasance makamashinta mutane ne dakuma duwatsu. ALLAH UBANGIJI katsaremu amin ya RABBI. Awannan 'Bangaren Nakeson nayi rubutu domin yan uwa musulmai su anfana. ALLAH MADAUKAKIN SARKI ya dafamin MATAKIN FARKO (Neman Aure zuwa da yakai 5yrs) Dole Akan kowa Idan yazo neman aure Yanemi Mai addini Da hali nagari Da kakkyawar zuciya. Ba kawai kyawun fuskaba ko wani martaba ko nasabar Abokin zama ba. Kuma yazamto anyi auren tanasonsa yana sonta. Domin hakanne Zaisa suji dadin zamantakewarsu ta Aure Kuma hakan Zaisa yayansu sutaso dason junansu Da Bin doka ko umarnin Da akayi masu. Domin kada yazamto uwa tace fari uba yace...