TARIHIN SAHABBAI Kashi na daya 001
TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR SADDIK ALLAH YA YARDA DA SHI, (manzon Allah S. A. W) "yace ya Abubakar kai ne farko wanda zai shiga Aljanna daga al'umma ta" Sayyidina Abubakar shi ne Abdullahi dan Abu kuhafatu " usman" usman dan Amir dan Amir dan ka"abu dan sa"adu da taimu dan murratu dan ka"abu dan lu"aayu, bakuraishe. Bataime. Nasabarshi ta hadu da manzon allah ta wajan murratu dan ka"abu kakansu na biyar. Sunan shi a lokacin jahiliya "Abdul ka" aba" daya musuluta sai manzon allah ( S. A. W) yakara shi "Abdullahi" An yi mishi alkunya da Abubakar saboda riganyenshi wajan dabi"antuwa da kyamara halaye. Kuma an yimasa lakabi da saddik sabo da saurin bayar da gaskiyar shi ga dukkan abunda manzon allah (S. A. W) ya fada kuma manzon allah (S. A. W) yakara shi da "Atiku" shine mutumin da yafara musuluta a manyan. Shi ne mutum na farko, da ya fara kira zuwa ga addinin musulunci. Bayan manzon Allah Annabi Mu...