TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYAS

 Tarihin Shehu Ibrahim Inyas 



Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy


   Dafarko dai Mai Karatu Zanfara da sunan ALLAH ﷽


Mun manta da tarihi Saikawai Labaran Duniya dakuma Kallace_Kallacen Film, Har wasu daga cikin Daliban Wannan bawan Allah din Sheikh Ibrahim Inyas mabiyansa Na Tijjaniyya Da Faidha. Basusan Tarihin Nasaba Saidai kawai Sunsan Littattafansa Wadanada yarubuta Kamarsu Kashiful Ilbasi, Dama Dawawinu_Ssittah. dama Sauran Littattafansa na Abyat.

 

                           ﷽


اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎


Dafarkodai Sheikh Ibrahim inyas dai Asalinsa dan kasar Sanganiyane Agarin Kaulaha. Bayan Rasuwar Mahaifinsune alokacin da Sheikh Amadu Tijjani yazo yimasu Ta'aziyya, Sai Yanemi da da abashi dakin Soro domin Larabawa basa juran Zafi. 


    Yayansa Muhammadu Khalifa wanda Shine Magajin Mahaifinsu a fannin Khalifanci na Wannan Zawiyyan, Sai yace dashi ga dakin Ibrahim Shine Soro kuyi masa Iso dashi, Bayan Ankaisa ga Dakinne Sai Ibrahima Inyas yanemi Zai fita daga dakin.


    Ananne ya qaddamar Masa da Quudirinsa na zaban dakin Soro. Dominsane shi Inyas. Sunyi Maganganu dai awannan daren Ahmadu Tijjani da Ibrahim inyas Amma na bibiyi tarihohin Marubuta banga abubuwan da suka tattauna ba azancen su na wannan daren. Sai dai wasu Suna Cewa Awannan Darenne yabashi Khalifanci na Qadmin Gausiyya.


     Allahu akbar! Bayan Lokacin Maulidi yazagayo🕦 kowa ya hallara an dagashi (inyas) domin Gabatar da Yabo sai yayi Magana  kamar haka.

ومن یحبنی ومن یرانی فی الجنة


Fassara:

Dukkan wanda yasoshi ko ya ganshi To dan Aljannah ne. 



  Hmm Tabdijam, Gaskiya Wannan Zance yayi Nauyi dayawa, Idan Har ya Tabbata ya fadi Wannan zance to Gaskiya ba maganan ajizanci wannan Son Zuciyane. Inkuma Qage akayi masa to malaman Dariqu kaf dinsu Makaryatane domin Wannan Zantuka nacikin Littattafan Dariqu dadama. 


Bari Muci gaba da Tarihi.


Bayan Wannan zancen Nasane fa Ruwa yafara kaiwa rana, tsakaninsa da yayansa Muhammad khalifa inda yayi masa inkari gamida fusata Yace dashi. Banine khalifan Baban kuba.


Saiyace kwarai kuwa kai kahlifan Baban mune, Nikuma khalifan Amadu Tijjani, Kuma Khalifan Manzon Allah.


 Daganan fa aka fara gwabza rikici cikin Sabani da rikicin Khalifanci. Wasu marubutan Suna cewa har Guba Ansakawa Inyas a Abinci kuma yaci amma bai mutuba.

     An koreshi daga Garin Kaulaha ta Kasar Sanganiya, Inda yakoma Koci yakafa daular Zawiyyarsa awannan Sauran ta Gonar Koci. Sheik Ibrahima Yasha gwagwarmaya Arayuwa Sosai duk asanadin wannan muqamin nasa na Gausiyya. Amma Allah ya tseraddashi daga dukkan tuggu.


ZUWANSA NIGERIA


Sheikh Ibrahim Inyasy yazo Nigeriyane ta sanadin wani Sarkin Kano Dan Tijjaniyya wanda dayayi Rokon Allah yabashi damar Zuwa hajji Sannan yahadashi da Gausin Zamani.

Bayan Allah ya cika masa Burinsa na Zuwa Saudiyyane Sai yahadu da Sheikh Ibrahim inyas Na Kaulaha. Dagan suka Gaisa Yakuma rokeshi da Neman Alfarma na cewa yazo kasar sa ta Nigeria.


Awannan lokacin yaso zuwa Amma sai aka samu akasi akan Rikicin da duniya takeyi Na yakin duniya na biyu.

Sai bayan wannan lokacin kafin yazo Sannan yazo tareda Littattafai yarabawa malamqn Tijjaniyya na Nijeriya. Malamai Sun Sallama masa Saida malami guda dayane yayi mar tawaye. 

 Amma shima daga baya ya sallama.


  Daga wannan lokacinne Sunansa yakarade nigeria kuma yasamu Martaba da kuma Muqami sosai daga cikin maluman cikinta mabanbanta.


Wannan Shine kadan daga Tarihin Sheikh Ibrahim Inyas Shugaban Dariqar Tijjaniyya Khalifan Sheikh Amadu Tijjani.


   Muna Rokon Allah ya Dawwamar damu akan bin Tafarkin Sunnah da bin Sunnah duk wuya duk dadi Allah ka karamana ikhlasi da Istiqaama akan Shiryayyen addininka. Da bin Annabinka dakuma bin Sahabbansa Salafussalih. Allah kayi Tsira ga Manzonka Annabin Rahama. مُحَمَّد ﷺ


واَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage