MATSALAR TSARO AKASATA post 2
MATSALAR MANYANMUNE!!
Matsalar tsaro A'kasata Fitowa ta biyu
(!!) ✍️Ismail
Hussaini Adam Matsalar tsaro akasar Nigeria abune mai matukar wuya amaganceta da
hanzari, Domin Al'amuran Sun jima Da Cakud'ewa cikin mummunar qaddara da muka
samu kanmu aciki musanman Mu Al'umar Arewa. Ansamu akasi tahanyar wasunmu suna
goyon bayan ta'addanci aboye, bincki da akeyi ana kin bayyana gaskiya, Shine
babban Al'amarin daya gur'bata Al'amuran tsaro A'kasarnan. Wai sai ace anrufa
asiri akwai 'yan Alfarma. Shifa d'an ta'adda, ko mai goyon bayan ta'addanci,
Koda uwarsace data haifeshine yasan zata fallasheshi, Wallahil aziim zai aikata
lahira, komai Son da takemai, balle jami'an tsaro ko Masu fad'a aji na gari
Wad'anda aganinsu sune Cikas d'insu aharkar dasuke ciki. Yazama wajibi akan
hukumomi, Da Shuwagabannin Al'uma ta ayyadar da hukunci, akan dukkan wani mai
laifi data kama, takuma yi bincike akan dukkan wanda take zargi da ta'addanci,
ko goyon bayan 'yan ta'adda. Idan Tayi bincike inya tabbata kuma tazartar da
hukuncin daya dace. Hakan shine hanya mafi sauki, Ta hanyar da za'a gyara
matsalar tsaro acikin Al'uma. WANI ABINDA MUKA MANTA Wad'annan masu laifi da'ake
kamawa da sunan 'barayin gida da masu fasa shagunan, Idan ba'azartar masu da
hukuncin daya daceba Sune ake Sayansu Su girmama, Abasu Makamai sucigaba da
ta'addanci dakuma Kisan mutane, haka kurum ba gaira ba dalili. Dole ne acire
maganar Alfarma, Dukkan wanda hukunci ta haushi kawai azartar masa shine adalci.
Allah yafi kowa son bayinsa Amma yana hukumtasu idan sun aikata ba daidaiba.
Tayadda yakema 'Kona wasuma domin mummunar aiki dasuka aikata. Kuma yayi umarni
garemu akan mu zartar da hukunci da adalci akan dukkan wanda doka ta haushi.
Hakika Al'uma tana shiga firgici da mummunar yanayine tahanyar sakaci da'akayi
da hukunta masu laifin cikinta. A Nigeria mun sami kanmu cikin wannan yanayi
tahanyar Sakacin hukumominmu da shugabanninmu. RASHIN AIKINYI GA MATASA MA
QALUBALENE Matasa babu aikinyi a kasarnan dalili kuwa Shine, manyanmu basu
kishin kafa wadatattun masana'antu burinsu gina gidaje kawai da zuwa 'kasashen
waje. Taya 'Kasan wajen suka sami Cigabane Bayan samun nagartattun Shugabanni
masu kishi Suna kula da hakkin Talakawansu. Yakamata Asamarda wadatattun
masana'antu tayadda za'arage masu zaman banza dakuma yan Fasa 'kwauri akasarnan.
A'kasarnan akwai arzi'ki wanda yagirmi lissafi amma kuma munfi kowa Talakawa,
wannan yasamo asaline danganeda Rashin tallafin jari da aikinyi ga masu 'karamin
'karfi, Saudadama wasu na fara kasuwanci amma da zarar sunsami karayar arzi'ki
shikenan yazama abin tausayi. Mai iyuwa ma wanin daganan yakan koma goyan bayan
ta'addanci, domin yasamu dukiya koma yazamo member na 'yan ta'adda. ANA ZALUNTAR
'DALIBAN KARATU Harajin karatu awannan kasa nada wahalar Gaske, ga kuma ana
matukar Cin dunduniyar 'Dalibai tahanyar mugayen Lecturers. Kai harda keta
alfarmar (Mutuncin) 'yan mata. A iya Saninmu ga Manyanmu na yanzu Shine. Sunyi
karatune akyauta kokuma cikin sauki, Amma donme suke musgunawa Mutane ayanzu?
Mafiya yawan malaman yanzu burinsu shine su samu kudi Suma a'kirgasu acikin masu
Arzi'kin 'Kasa. Bawai su bada karatu ga d'alibai ba kamar yadda yake a hukunce.
Wannan yasa suke neman Kudi ido rufe a governati domin cimma burikansu dakuma
kirkiro wasu tsaruka mabambamta. wadanda suke da rauni da Da'kushe har'ko'kin
ilimi akasarnan. Strike da ake samu a jami'o'i da Colleges yasamo Asaline daga,
Son duniyar wasu daga cikin Malamai. Dolene Govrenati tasan hanyar da zata shawo
kan Wannan Al'amari. Mutane na kashe kud'ad'e masu yawa kuma Suna d'aukan dogon
Zango kafin su kammala karatunsu. Duk asadin matsalar Yajin aiki (Strike). Kuma
akarshe yazamo Sun gama karatu kuma sun rasa aikinyi, Tambaya anan itace, idan
mutum mai raunin imani yasha wannan wahalar kuma yarasa aikinyi, Me kuke tunani
Zai biyo baya? MATSALAR ASAMACE Manyanmu na sama Sune ke morar arzikin
'kasarnan. Manyan Nigeria mutum daya na d'aukan ma'kudan kud'i a governatin
tarayya fiyeda Lissafin mai tunani Amma Nakasansu kuwa suna shan wuya matu'ka,
Amma abinda suke samu ko na man mota baya wucewa, ballema aje ga Masarufi,
dakuma Suturar jikki da kayan 'Kawar ado. Don me corruption bazai Existing
atsakanin muba Alhali wasunmu naci da gumin wasu. Su kuma manta da Hakkin dake
tsakaninsu na zamantakewa. A'ka'idar Zamantakewa ta mususukunci dolene kasan Ci
da Shan ma'kocinka Kamar yadda zakasan na Iyalinka. Amma ayanzu babu ruwan wani
da Wani, Anyi watsi da karantarwar addini anbi yahudu kuma gashi an'bace ba
akamo yahuduba kuma Ambar Allah. Wadannan ma Suna daga cikin Hanyoyi mafiya
girma na sanadin Lalacewar Tsaro a Nigeria. Zanci gaba Insha Allah. Allah ya
tabbatar damu akan gaskiya da shiriya.
Comments