MUSULMI GA SAKO

 MUSULMI ATASHI AKAFA DAULA DAN SAMUN INGANTACCEN RAYUWA


inji Shahararren malamin salafiyyannan Sheikh Muhammad Adam Albany Zaria.

   Hakika shugaba yayi wadannan maganganu da shawarwarin agurare Ma bambanta da majalisai dadama. Domin nuni garemu ga hanyar tsira. Dakuma koyi da magabata. Don samun rayuwa Mai inganci, da zamantakewar rayuwa Mai tsafta. Ba kamar yadda wasu ke daukar zancen awata mahanga. Da tunani irinta miyagun mutani ba. 

Ga zancen malam; 

Tsokaci kan batun malam:

    Saidai haryanzu banji wani shahararren mutum daga cikin malamai ko shugabanni daga cikin musulmiba wanda ke karfafa Zancen. Duk da cewar maganan maganice na ciwon dayake damun musulmin duniya baki daya. Saidaima wasu daga cikin miyagun mutane dasuke fassara zancen da wani salo nadaban, tayadda suke kokarin cire ma'anar maganan na hakika su shigoda wani al'amari nadabam. 

    Gadai Maganan da malam yayi;

Mal. Yace ''Yakamata musulmi su kafa daula Dan gujewa hadarin dake gabansu, na miyagun hare_haren yahudawa"

Abinda malam ke nufi anan shine. 

Shi cigaban addini dole saida kafa  daula dakuma tabbatar da Shari'ah. domin tabbatar da Shari'ah shiyake saukakewa mutani  hanyar rayuwa Mai inganci. Shi Kuma kafa daula shine hanya mafi sauki Wanda zai tabbatarwa da mutani yancinsu. Tayadda gudanarwar rayuwar Musulmi zaizamto tsararrene, Ga Shugabanninsu. Koda aharkar da'awace da karantarwa, zai kasancene karkashin wannan hukumace, matukar lamarin addini za'a karantar. 

   Ko kataba tunanin meyasa Turawan yamma suke gaba da Musulunci? To ga ansarka;

  Burinsu aduniya yazamto babu Mai iko saisu, tayadda zasuyi dukkan abinda sukeso batareda wani yayi musu inkariba. 

   Shi kuma musulunci akodayaushe Adalci yake tabbatarwa ga mutane. Haka kuma idan akace za'a kaddamar da Shari'ah za agusar da Al'adunsu asanya abinda Allah yahukunta Wanda kuma yasha bamban da son Zuciyarasu. Kuma Shine ainihin adalci, duk mai inkari akan haka yadauki Alqur'ani yakaranta, Zaiga tsagwaran adalci. Sa'banin son zuciya dakuma Zalincin turawa na constitution, wanda muke anfani dashi amatsayin hukunci ayanzu. Dashi suke amfani su saka dukkan wata son zuciyar na burin dasuke so su cimma akasanku saisu fake dacewa sunkawo muku tsarin hukuman, dana shugabanci kuma wai Afadinsu shine dokokin kasa wadanda za'ayi amfani dasu. Wanda ahakikanin gaskiya akwai duk abinda muke bukata acikin Alqur'ani da Bible. Nadaga tsarin rayuwa dana shugabanci, domin wannan shine dokar Allah wanda ya shinfidasu ga bayinsa.


Idan mukayi dubi ga maslahar kafa daula kuwa. Misali mafi sauki Shine Inda zamuyi dubi ga Al'umomin damuke rayuwa acikinta. 

        Abinda zamu lura anan dai shine Kowace kasa tanada sojoji dasuke karkashinta tareda shugabanni mabambanta. Shugabannin nan sune ke tsara dukkannin doka da tsarukan cigaban kasar. To inaga musulunci. Wanda danshi mukazo duniyar kuma yatara makiya kota ina. Inbabu shugabanci bazamu Taba sanin ina muka dosaba. Saidai muta dimuwa da fagabniya tayadda zasu cigaba da kashemu dakuma kiranmu dasunan yan ta'adda. Idan da zakayi bincike kashi saba'in da biyar cikin Dari (75%) Na mutanen da yan ta adda ke kashewa ayanzu Musulme ake kashewa. Amma kuma musulmi ake daura wa Alhakin kisan, dakuma Kiran musulunci da Sunan addinin ta'addanci da 'yan ta'adda. Domin Akan samu wasu lalatattu da basusan mecece hakikanin addiniba, Suna fakewa da sunan jihadi Suna ta'addancinsu abisa son zuciyarsu. Don wata maslahar rayuwarsu ta duniya. Kuma suna kiran kansu musulmi, Sabida Musulmi basuda manya hukumance waanda dazata karyata wannan al'amarin yasaka, ake tafiya ahaka batare da angyaraba.


     Indagaske musulmaine yan ta addan danme za ake kashemu Kamar kisan kiyashi. Adasa boma_bomai akona masallatanmu dasunan ta addanci. Kawai Rashin Tabbatar da daulane dakuma Rashin samar da daularma gabaki daya. Tayadda wasu zasu fake dasunan jihadi suna kashemu sa'Annan akuma daura alhakin kisan agaremu. Don rashin samun wadanda zasuyi jagora gurin fada da Al'amarin acikin hukumomin duniya.

        Kada rayuwar holewa na turawan yamma yaburgeka ka manta da addininka ko police kasamu amatakin hukuma, Matukar kai musulmine kaji aranka aikin musulunci zakayi. Inzamu dukufa dakawunanmu duk yawan kafiran duniya koda sun nunkamu sau dubune basu isa suyimana abinda Allah bai So Ba, Sai abinda Allah yanufa akanmu shine zai samemu. Kada abin duniyarsu ya tsole maka ido har ka aminta da wani mummunar manufarsu akan Al'umar musulmi. Koda Kai ba musulmi bane to inba ayankinsu kakeba to hakika Kai abin Hari ne garesu kuma sai sunyakeka ta kowani bangare na rayuwa. 

   Abin Lura garemu musulmi.

Allah yafada mana acikin Alqur'ani. Wadannan mutane bazasu gusheba suna yakarmu ta kowani 'bangare harsai munyi ridda munbar addininmu. Kuma kada mumanta da Cewa Su wadannan kosu kyautata ko Akasin Hakan, Allah yayi alkawarin basu duniya Don ita duniya ta kowace, Lahirace ta Wanda Allah yazaba. Kuma duk Wanda yanemi duniya zaisamu. Amma abinda muka sani Su musulmi sunada iyaka awajen nemansu. ba nema mukeyi ta kowani bangareba. Tayadda mukan bambance halal da Haram wannan yasa arzikin musulmi yasha bamaban da turawan yamma dama sauran Al'umomin duniya. haka tsarin rayuwarmu shima ya bambanta dasauran wasu addinai. 

Daga Alqalamin 

✍️📝Ismail Hussaini Adam Assalafy

Whatsapp: 09047958802

Instagram: ismailhussein511

Email: hussainiismail257@gmail.com

     ALLAH kadaukaka musulunci da musulmi, ka qasqantar da kafirci, da kafirai, ka dirkake maqiyanka maqiya addininka kataimaki bayinka na qwarai. 

4/Ramadhan/1442 Hijiri

16/April/2021 Miladi

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage