MATASA!!! MUKOMA GA ALLAH
`YAN UWANA MATASA!!! MU KOMA GA ALLAH
Rayuwar Matashi abin tausayine, Kana fama da Quruciya Ga kuma bakin Al`uma akanka. Idan za`afadi Damuwar Al`uma dubu, Kaso ´Dari Tasa da Hamsin (950) Na Matasa ne.
Qalubale Garemu Matasa, Ban cire kainaba domin nima cikin Quruciya nake.
Tabbas Muna Fuskantar Qalubalen rayuwa daga ´Bangaren zamantakewa, Har da Ibada. Saidai Raunin zuciya kuwa ya danganta da Yadda mutum yataso, Wahala ko Qunci, Tarbiyya ko Akasin hakan (Garari), Riskar iyaye da Rai ko Tashin Maraici. Idan Kasamu yin Makaranta Fani'ima (Haka akeso) In MA bakasamu ba Kaidai kada Kabar Neman ilimin Addini Domin Shidin Yalwatacce NE. Ako Ina akwaishi Amma kayi Takatsan_tsan Maluman da Kake Saurara. KADA kabi Maison Zuciya.
Dukkan Wadannan Matsololin Rayuwa ce, Kirata Agaremu Shine, Mugane inane hanyar tsira kuma mecece mafita ta rayuwar mu, Ina Muka fito, Ina Zamuje, Me zamu Riska, Ina Tafiyar zata Tiqe?
MATASA BAYIN ALLAH NE
Kada Mushagaltu da Rudin Rayuwar duniya, Ko kuma Yanayin juyin Rayuwa yasanya Mu ´Bata Rayuwar mu da Shaye_shaye, ko Ta`addanci, ko Daba, Da zama `Yan Iskan gari.
Mugyara Rayuwarmu tahanyar kaucewa had`arurrukan da Shuka shafi aikata Munanan Laifuka, Mutuna Cewa Allah yake bada arziki, kuma Shike bada lokaci dakuma damar Amfanar Arzikin namu. Zamu iya tarawa ahanyar 'Barna (Haram) Amma mu mutu, bamu ciba kuma Hisabinta Nanan Akan mu.
Zamu iya shiga Matsalar Rayuwa, Mugur´bata Rayuwar mu da Shaye_shaye ko garari Sanadiyyar wani, ko wata Mattsala, Mun manta cewa ga Allah za a koma kuma akwai hisabi, Shifa Allah ako ina Mukayi kuka Yana jinmu. Idan Ka Shiga Mummunar Hali Mu tuna da ALLAH. Sannan Mu dunga Yawan Ambaton Allah d`in kada Muce zamu Sha kwaya, ko Mu Kunna Sigari, Yi Hakan kamar An watsa maka Kashine ka Wanke da Kwata. 'Barna bata Kawar da 'Barna.
Mu waita yin Istigfari, Wata Qila Jarrabawace ta Yawan zunubin mu, Allah yakeso ya kankare mana. Allah ya yafe mana Yakuma ´Dauramu akan Shiriyar Addininsa, Yakuma Tseratar damu daga Tabewa da Halaka, Allah ka Albarkanci Iyayenmu, da Malumanmu, da Yayunmu, da Kannen mu, Damu kanmu, Wadanda Suka Rasu a Gafartamasu Musamman Mahaifina Allah kajikansa Da Rahama.
Sakon Barka da SALLAR ADHHA ( Eidin Layya) Kutayani Yad'a wannan Sa'kon.
daga Alqalamin ✍️ Ismail Hussaini Alpholtawy
Comments