NASIHA
KA ZAMTO TAMKAR BAKO A DUNIYA. - "Duniya ba gidan dauwama bace ita gidan ci-rani ce, kada ka bari ruɗun cikinta ta yaudare ka yakai ka ga saɓawa Allah maɗaukakin sarki, domin lallai duk soyayyar da duniya take nuna maka a yanzu, to wallahi watarana sai ta sake ka" - "Kullum kada ka sake ka mayar da wannan duniyar tamkar wata madauwamar ka, babban mai hankali shine wanda yake yiwa duniya tamkar gidan ci-rani, wato gidan wani ɗan zama ne ƙan-ƙani ba mai dogon lokaci ba, da zarar ka gama rayuwarka sai ka tafi ka barta" - "Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya bamu shawara da cewa "mu zamto a wannan duniyar tamkar baƙi ko kuma masu ƙetarar hanya" wato irin mutanen da basa sakankance wa a duk inda suka je burinsu kawai suyi abinda ya kawo su su koma inda suka fito, to mu kuma bautar Allah ce ta kawo mu duniyar, da zarar rayuwar mu ta ƙare zamu koma ga mahaliccin mu Allah"