Posts

Showing posts with the label Likitanci

MASHAHURAN MUSULMAI DA SUKA FARA KIRKIRAN AIKIN LIKITANCI A DUNIYA

Kamar yadda nayi bayani a rubutu na farko Wani abin haushi da Turawan yamma na yanzu suke yi shi ne, na boye sunayen Musuluncin waɗannan mutane, suna sa musu nasu na Turanci, wai don a ce su ma nasu ne. Ga kadan daga cikin irin wadannan mashahuran Musulmin da suka fara kirkiro abubuwan da har yanzu ake amfani da su: An ba da duka sunayensu na ainihi da na Turancin da kuma zamanin da suka zo: ~ Muhammad bin Zakariyya Al-Rhazi: Rhazes (865-925AD):Mutumin kasarFarisa (kasar Iran ta yanzu), wanda ya ba da gudunmowar da har a yau ba wanda ya ba da irinta a harkar lafiya. Domin ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya sha kawo bayanai na canjin tunani da hujjoji masu gamsarwa a harkar lafiya. Misali, shi ne wanda ya fara bambance ciwon Agana (mai sa cin zanzana, wanda kuma aka riga aka ga bayanta a yanzu) da Bakon Dauro, wanda duka kwayar cutar birus ce ke kawowa. Shi ne kuma wanda ya kirkiro kayan aikin likita da dama irinsu. Ya rubuta littattafai a kan harkar lafiya fiye da guda dari. Fitacce a...