NASIHOHINMU AYAU
MU LE'KA MAKABARTA )>
.
AWANNAN GURIN-
Wasu Rahama Suke Sha,
Wasu Kuma Dũkan Tsiya Suke Ci.
.
AWANNAN GURIN-
Wasu Sun 'Kosa A Tashi Alqiyamah, Sabo da Ni'mar da Suka hango A Gidansu Na Aljannah.
Wasu Kuma Roko Sukeyi Kada A Tashi Qiyamar Sabo da Azabar da Suka Hango Tafi Wacce Suke Ciki Bala'i,
.
AWANNAN GURIN-
Mutanan Kirkin da Ke Cikinsa dana Banzan dake Cikinsa, Suna yin Nadamar Lokacin da Sukayi Hasarar Sa,
.
NA KIRKIN CUKINSU:
Suna Yin Nadamar Ina ma Ace Gaba daya Lokutansu Sun Qarar dashi Akan Bautar Allah, Sabo da Sakamakon Alkairin Aikinsu da Suka fara Gani.
.
NA BANZANSU KUMA:
Suna Yin iihu, da Kururuwa, da Cizon Yatsa, da Takaicin Qarar da Rayuwarsu da Sukayi Akan Aikin Banza.
.
NI, DA KAI AYANZU-
Zãbi ya Rage Agremu, ga Irin Rayuwar da Muke Son yi Bayan Mutuwar Mu,
.
Ko dai Mu Zabi Rayuwar da Mala'iku Zasu yi ta Jibgan Mu, Kunamu da Macizai Suyi ta Saran Jikin Mu.
Ko Kuma Mu Zabi Rayuwar da Zamu Samu Nishadi da Natsuwa Acikin Qabarin Mu.
.
Kada Dai Mu Manta Zamu Mutu,
Me yiwu wa Anjima ko Gobe.
.
Yaa Allah Kayi Rangwame da Yafiya Ga Musulmin da Suke Cikin Uqubar Ka, yaa Allah Rahamarka ta Rinjayi Fushinka, Allah Ka Yafe Musu ka Sanya su Acikin Rahamarka.
Mu kuma Allah ka Kyautata Qarshen Mu.
#Fatan_Alkairi
*ƁARAYIN CIKIN WATAN RAMADANA*
-
🍃"WAYA, tana ɗaya daga cikin manya-manyan ɓarayin cikin watan Ramadana, a daɗe ana amsa kiranta, ana gulma da ita, ana chatting da ita, ana ɓata lokaci akanta, da haka sai ta zamto matattarar tara zunubai masu yawa, kuma take yashe ladan azumin mai azumi"
-
🍃"TV wata babbar hatsabibiyar ɓarauniya ce wacce take illata azumin mai azumi, kuma ta rage masa ladan azuminsa ba tareda ya ankara ba, domin takan ɓata lokacinsa, takan hana shi yin sallah akan lokaci, takan sa mutum ya kalli ƙar-yace-ƙar-yace"
-
🍃"KASUWA, itama kasuwa ɓarauniyar cikin watan Ramadana ce, domin takan kange mutane daga ambatõn Allah, takan hana wasu yin ibadu akan lokaci, kuma takansa wasu su cuzgunawa ƴan-uwansu ta hanyar ƙara musu farashi"
-
🍃"ƁATA LOKACI, shima yana ɗaya daga cikin manyan ɓarayin cikin watan Ramadana wanda yake da tasiri wajen sace ladan mai azumi, babu karatun alƙur'ani, babu addu'a, saidai surutu, wanda kuma hakan yana rage ingancin azumin mai azumi"
-
🍃"KITCHEN, shima babban ɓarawo ne wanda yake sacewa mata lokutansu musamman acikin wannan watan na Ramadana, ya hanasu yin karatun alƙur'ani, ya kange su daga ambatõn Allah, duk sun ɓata lokacinsu a wajen girke-girke acikinsa"
-
🍃"MAJALISA, taruwa a wani majalisi wanda zai haifar da rashin ambaton Allah, da kuma salati ga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama, wannan shima babbar asara ne ga mai azumi"
-
🍃"SOCIAL MEDIA, wannan shine babban ɓarawon da yake yashe ladan azumin mai azumi, domin nan ce kafar kowace fitnar zamani, wanda guri ne da ɗinbim mutane suke raunata azuminsu acikinsa, ta hanyar kallace-kallace, da rubuce-rubucen irin abubuwan da basu dace ba"
LOKACI MAFI TSADA NA KARANTA ALQURANI A CIKIN WATAN RAMADHANA
Karanta alqurani acikin Daren watan Ramadhana shine mafi alkhairi da falala fiye da karanta shi a yinin Ramadhana,musamma dararen goman karshe na Ramadhana.
Domin:~
☆Manzon Allah s.a.w da Mala’ika Jibrilu suna yin Darasin Alquranine a dararen Ramadhana ba yininsa ba.
☆Shi kansa Alqurani yana kafa hujja na neman citon bawane awajan Allah da cewa na hanashi barci saboda yawan karantani da yàke acikin dare,sai yace ya Allah ka bani cetonsa.
☆Alquranin kansa an saukar da shine acikin daren lailatul Qadri daga Lauhul Mahfuz zuwa baitun izza a saman duniya kamar yanda Ibn Abas R. A ya fada.
☆Mafi yawan sahabban Manzon Allah s.a.w da Tabi’ai da sauran Magabata na kwarai sunfi yin tilawar alqurani a watan Ramadhana ne da dare.
☆Sannan tilawar da dare yafi samun ikhlasy da kyakkyawar niyya da kuma nesa da riya da son nuna yawan ibada.
☆Sannan da dare anfi samun nutsuwa da nishadi na karatun alqurani sannan babu saurin gajiya da kasala.
☆Sannan yinsa daren yana sanyawa mutum ya dace da daren lailatul Qadri wanda ibada acikin wannan daren daya tafi alkhairi akan ibada a dararen watanni dubu wanda babu daren lailatul Qadri acikinsa.
☆Sannan akarshen kowane dare Allah yana saukowa samar duniya dan amsa addua da tuban bayinsa,sai kuma Allah ya sameka mutane suna barci kai kuma kana tilawar Maganarsa.mi yafi wannan alkhairi ga dan adam.
Yan uwa kada muyi barci mutashi mu rumgumi karatun alqurani mai girma a sauran dararen Ramadh*HUKUNCE-HUKUNCEN RAKA'A GUDA BIYU, BAYAN FITOWAR ALFIJIR*
Darasi na Daya-1
*Falalar Ra'atanul Fajir*
Hakika An ruwaito Hadisai Masu yawa da suke bayyan falalar,yin Sallar raka'a biyu bayan alfijir ya fito,daga bakin Annabi SAW ga kadan daga ciki:
1-Annabi SAW yafi san Raka'a biyu bayan fitowar alfijir,fiye da duniya gaba daya.
Aisha R.A ta ruwaito
@Muslim,Ahmad da Tirmizy.
2-Annabi SAW yana cewa:
"Kada kubar raka'a biyu bayan fitowar alfijir,ko da kuna tsammanin. Abokan gabanku".
Abi Hurairata R.A ya ruwaito shi.
@Ahmad da Abu Dauda
3-Babu wata Nafila da Manzon Allah SAW yake tsananin kiyayewa ba kamar yin. Raka'a biyu bayan alfijir Aisha R.A ta ruwaito
@Bukhari da Muslim da Ahmad da Abu Dauda
4-Annabi SAW yana cewa:Raka'a guda biyu bayan fitowar alfijir,sunfi duniya da abinda yake cikinnta,alkhai ri.
Aisha R.A ta riwaito
@Muslim da Ahmad.
5-Daga Aisha R.A tana cewa: Banga wani aikin Alkhairi wanda Annabi SAW yake gaggawar aikatawaba,kamar yin. Raka'a biyu bayan fitowar alfijir.
@Muslim.
*ANA TAKAITA SU*
yana cikin Sunnar Annabi SAW game da dayin Nafilar fitowar alfijir,yana takaita karatu,amma yana cikasa Ruku'u da Sujada:
1-Daga Hafsa R.A tana cewa:Annnabi SAW ya kasance yanayin Sallah raka'a guda biyu kafin Sallar Assuba a dakinta kuma yana takaitasu Matuka.
@Bukhari da Muslim.
2-Daga Aisha R.A tana cewa:Manzon Allah SAW yana Sallamar raka'a biyu kafin Sallar safiya(tana nufin kafin Sallar Assuba) a dakinta,yana saukakasu har nakanyi tsammanin ya karanta Fatiha ma ko bai
Comments