Posts

Showing posts from May 20, 2021

MATSALAR TSARO A NIGERIA Post 1 (!)

BABA YAKASA MATASALAR TSARO AKASATA Leave the issue that he has doing well kawai muce Baba yakasa. Abin na Bu'katar Tunani ne. Idan zamuyi adalci wa kanmu kuma mufadi gaskiya, Wallahi matsalar tsaro a nigeria, kasawar kayan aikin Jami'an tsaron governati ce. bawai ina nufin bata da karfin yaqarsu ba, kawai taki tayi abinda yadacene dan ganeda lamarin. Tahanyar nazari dakuma bawa jami'ai kayan aiki dakuma da nauyi da bada tallafi ga iyalin duk wanda yarasa Ransa akan yaki da 'Yan ta'adda. Kullum al'amuran kara rikicewa yakeyi, Tambayata anan itace: Waishin su 'yan ta'addannankam aljanune, kokuma aljanune suke basu kayan aikine. Wadanda dasuke amfani dasu, Kama daga ci shansu har zuwa makamai dasuke amfani dasu, dakuma man da suke sakawa a ababen hawansu. da'akwai alamar tambaya anan gun! Shin anya acikinmu babu masu daukan nauyinsu? kokuma makiyanmu ne ke basu mafaka da tallafi? Idan akwai kuwa suwaye wadannan mataimakan nawu? Kuma...

MATSALAR TSARO AKASATA post 2

MATSALAR MANYANMUNE!!  Matsalar tsaro A'kasata Fitowa ta biyu  (!!) ✍️Ismail Hussaini Adam Matsalar tsaro akasar Nigeria abune mai matukar wuya amaganceta da hanzari, Domin Al'amuran Sun jima Da Cakud'ewa cikin mummunar qaddara da muka samu kanmu aciki musanman Mu Al'umar Arewa. Ansamu akasi tahanyar wasunmu suna goyon bayan ta'addanci aboye, bincki da akeyi ana kin bayyana gaskiya, Shine babban Al'amarin daya gur'bata Al'amuran tsaro A'kasarnan. Wai sai ace anrufa asiri akwai 'yan Alfarma. Shifa d'an ta'adda, ko mai goyon bayan ta'addanci, Koda uwarsace data haifeshine yasan zata fallasheshi, Wallahil aziim zai aikata lahira, komai Son da takemai, balle jami'an tsaro ko Masu fad'a aji na gari Wad'anda aganinsu sune Cikas d'insu aharkar dasuke ciki. Yazama wajibi akan hukumomi, Da Shuwagabannin Al'uma ta ayyadar da hukunci, akan dukkan wani mai laifi data kama, takuma yi bincike akan dukkan wanda take zargi da ta...

HANYAR KUTSE TA SIYASAR YAHUDAWA

Image
Gabatarwa Dukkan Yabo ya Tabbata ga Allahﷻ Wanda yayi Rana, Da wata, yayi Halittun Duniya da Dukkan Abinda Yafaru Iyawarsane. Muna yabamasa, Muna Godiya Agareshi, Daya Sanyamu Cikin Al`uma wacce take Mafificiya. Wacce tazamo Mafi daraja daga Cikin Al`umomin da Allah Yake Sanyawa adoron Kasa, Karkashin Manzo Mafi Daraja Cikin Manzanninsa Mafiya Daukaka Annabi Muhammadﷺ. Muna Godemasaﷻ daya Sanyamu Musulmi Kuma Masu Kokarin Neman Sanin Gaskiya Dakuma Bincike Akan abinda Zai Zama Hanyar Tsira Agaremu. Bayan haka; hakika Ban Wallafa Wannan Rubutu nawa Domin Cin Zarafin Kowa ba Sai Dan Fayyace Haqiqanin Abinda Allah ne Yamana Ishara Cikin Littafinsa Mai Tsarki Karkashin Ayoyi dayawa Amma Zangina Rubutuna akan Wannan ayoyine Guda biyu Wadanda Suke Bayani Karara Akan Siyasar Dunya watau Dilomasiyya Fadisa ``Yahudu da Nasara Basa Yarje Muku Harsai kunbi Tafarkinsu`` Dakuma Fadinsa ´´Bazasu Gujeba Suna Yakarku Harsai Kunbar Addininku Insun Samu Iko`` Amma Kuma Ubang...

BABU UZRI BAYAN MUTUWA*

  - "Duk wani uzrin da bawa yake ƙunshe dashi a lokacin rayuwarsa ne kaɗai yake da ikon aiwatar dashi, yana mutuwa shikenan uzri ya ƙare, abinda mutum ya shuka shi zai girba" - "Bayan mutuwarka a lokacin da aka ɗauke ka izuwa makwancin ka, komai yana jin abinda kake faɗa ga masu ɗaukar ka, amma saidai su mutanen da suka ɗauke ka ɗin basa taɓa jin abinda kake faɗa" - "Ya kai miskĩni! Lallai ka sani cewa fa, a lokacin da ka mutu shikenan taka ta ƙare, bayan an ɗauke ka acikin makara babu wanda yake fuskantar halin da kake ciki balle ya karɓi ƙorafinka, face dabbobi ko bishiyoyi, sai kuma ubangijin taliƙai, to ka gabatarwa da kanka wani alkhairi wanda ba za kayi nadama ba baJyan mutuwarka"

Nasiha Zuwaga Yan Mata

"TSAYA KI JI ƘANWATA       GA SHAWARA Ƴan mata nasan tabbas kina da masaniya cewar a duniyar da muke rayuwa ta zahiri ba ta Facebook ba, mazan aure sun yi ƙaranci saboda tsarin Allah na yawaitar mata, tsadar rayuwa da kuma talaucin da muke ciki. To ki rufawa kanki asiri kar ki ɗauki zugar "kar ki auri wanda ba zai barki ki yi karatu da aiki ba". Mai kulawa da addinin da zai bayar da abinci uku da kulawa daidai gwargwado kaɗai a ke nema. In kin ƙi kuma, to akwai wata magana. Biyo ni ki ji batu. Akwai ƴan banzan maza waɗanda ba auren za su yi ba, amma suna yawon rage zafin balaga da yara irinki . Ƙanwata kina da zaɓin tsayawa ki kame mutuncinki, ki yi addu'ar samun me hankali da rufin asiri ko da zai hana ki karatun boko da aiki, ko kuma ki ci gaba da zaman benci a gidanku tare da rage gafin balagarki kema da balagaggun yaran can masu tara suma da gaisuwar "ya kike"! Ya ke ƙanwata ki dubi gidajen unguwarku kaf ki ƙirga ƴan matan kowane gida. Fara daga ƴan sh...