'YAN MATAN ZAMANI GA SA'KO
'YAN MATAN ZAMANI KO 'YAN SON ZUCIYA? A duk sanda naji mata na kukan wahalar samun miji, ko aurensu na yawan mutuwa nakan girgiza kai na wuce kawai, domin kuwa hausawa na cewa" kowa ya sayi rariya yasan zata zubar da ruwa." Da zaka ce musu laifinsu ke janyo musu wannan matsala, da yawansu inkari zasu yi, koda yake ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai wacce kaddara ke fadawa, akwai kuma wacce ta hadu da abokin zama bana gari ba, amma dai mafi yawa laifin daga wajen matan ne. Duk wacce tace maka bata sami miji ba, kace da ita bata sami wanda take so ba kawai, domin Allah ya jarrabi matan wannan lokaci da son auren maikudi wanda za'a dinga buga misali a cikin kawaye, mafi yawan matan dake kokawa da rashin samun miji akwai mazan dake zuwa da niyyar aurensu wanda suke ganin kamar ba ajinsu bane, ta sanadin hakan sai mace ta kusan tsufa a gidansu babu aure, wasu Allah kan tarfawa garinsu nono su sami irin mijin da suke son aura, amma sai zaman auran ya gagara ayi ...