Posts

Showing posts from March 18, 2022

SANIN COMPUTER DA SANA'O'IN CIKINTA

 Book 1 Daga Ismail Hussaini Alpholtawy Email 📧 hussainiismail257@gmail.com Nomban Waya📲 09047858802 Alpholtawy.Blogspot.com Ismaihussaini.code.blog Alpholtawy.Jw.Lt SANIN COMPUTER DA SANA'O'IN CIKINTA Gabatarwa Dukkan dangin Yabo da Godiya Sutabbata Ga Ubangiji Madaukakin Sarki ﷻMai kowa Mai Komai, Tsira da Aminci Su Tabbata ga Fiyayyen Halitta ﷺ Zababben Zababbu Mai Mukamin Ceto Abin Godewa Sha Yabo Annabi Muhammad (S.a.w). Da iyalan Gidansa Da Matayensa da Sahabbansa, da Masu binsa Cikin kyautata Ayyuka Har izuwa Ranar Sakamako. Ina Gode wa Ubangiji Daya bani Dama zan Wallafa Wannan Dan karamin Littafi, domin Amfanin al'uma Yakuma Zamo guziri Gamai Karatu Wannan Shine Littafi na Daya Zuwa Wani lokacin, Zan cigaba da Rubuta wani Makamancin Wannan Wanda Zai iya zama Cigabansa. ina Rokon Allah Yataimakeni. Ya Kasuwar Application Manhaja take Ita wannan kasuwar ta apps tana daya daga cikin hanyoyin samun kudi na...

WASIYAR WANI MAI HIKIMA GA DANSA A ZAMANIN INTERNET:

Yana cewa a cikinta: Lallai Google da Facebook da Twitter da Whatsapp da dukkan tsare-tsare (Platforms) ɗin sadarwa: Rafine mai zurfi, halayen mutane sun bace acikinsa. Hankulan Matasa sun gushe a cikinsa! igiyarsa ta tafiyar da kunyar yan mata, Jama’a da daama sun halaka! Ka kiyayi yawo a cikinsa, Kazama tamkar ƙudan zuma a cikinsa, kada ka tsaya ashafi sai mai kyau, domin ka amfanar da kanka dashi sannan ka amfani wasu. . Yakai Dana: Kada ka zama kamar ƙuda, wanda ke tsayawa akan komaai, mai kyau da mara kyau, sai ya dauki cuta ba tareda ya sani ba. . Ya kai Dana: Lallai Internet kasuwa ce mai girma, babu wanda ke bada kayansa kyauta, kowa nason wani abu kafin ya bada kayansa. A cikinsu akwai wanda ke son bata halaye amadadin kayansa! Acikinsu akwai wanda ke fitar da fikira rikitacciya, cikinsu akwai mai neman shahara, acikinsu akwai na ƙwarai, don haka kada kayi wata mu’amala da Mutum har sai ka bincika sosai. . Yakai Dana: ina kashedinka da kunce ƙulle-ƙulle, domin wasunsu tarkon...

TAYA ZA ASAMU ZAMAN LAFIYA ATSAKANIN AL'UMA

Dolene Sai Mun Tabbatar da Adalci A Tsakaninmu Cikin Ayyuka da Maganganun Mu, Sannan Kowa Yatsaya Iya Matsayinsa Mudaina Kutsawa Cikin Al'amuranda Basu Shafemuba Walau A Addinan ce Ko Azamanan ce, Anayiwa Al amura Kutse Tayadda hakan ke janyo AKasa Gane Hakin Menene Mafi Dacewar Al`amuranmu na Rayuwa, Har yazamto Munkasa gane Ina karya take damu gujemata ko kuma ina gaskiyar take Dan Mubi Sau dayawa Duk Al Amari inba afanninka Zakayi jawabi ba Anasa Ran Barbarka zatafi Gyara yawa. ALLAH Kasa mu iya da Bakinmu mufi karfin Zuciyarmu. 📝📃Alpholtawy

MASHAHURAN MUSULMAI DA SUKA FARA KIRKIRAN AIKIN LIKITANCI A DUNIYA

Kamar yadda nayi bayani a rubutu na farko Wani abin haushi da Turawan yamma na yanzu suke yi shi ne, na boye sunayen Musuluncin waɗannan mutane, suna sa musu nasu na Turanci, wai don a ce su ma nasu ne. Ga kadan daga cikin irin wadannan mashahuran Musulmin da suka fara kirkiro abubuwan da har yanzu ake amfani da su: An ba da duka sunayensu na ainihi da na Turancin da kuma zamanin da suka zo: ~ Muhammad bin Zakariyya Al-Rhazi: Rhazes (865-925AD):Mutumin kasarFarisa (kasar Iran ta yanzu), wanda ya ba da gudunmowar da har a yau ba wanda ya ba da irinta a harkar lafiya. Domin ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya sha kawo bayanai na canjin tunani da hujjoji masu gamsarwa a harkar lafiya. Misali, shi ne wanda ya fara bambance ciwon Agana (mai sa cin zanzana, wanda kuma aka riga aka ga bayanta a yanzu) da Bakon Dauro, wanda duka kwayar cutar birus ce ke kawowa. Shi ne kuma wanda ya kirkiro kayan aikin likita da dama irinsu. Ya rubuta littattafai a kan harkar lafiya fiye da guda dari. Fitacce a...

YIN AIKI DOMIN ALLAH* {1}

*SHEIKH ALBANY DA'AWA GROUP* * Yaku bayin Allah, kusani cewa Allah ba ya karbar aikin bayi sai idan an yi aikin dominsa. Duk wanda ya aikata aiki ya yi tarayya da Allah a cikin wannan aiki, to Allah ya wadatu ga barin karbar wannan aikin, duk kuwa yadda wannan aiki yake da yawa. Allah yana cewa: ( إِنَّا أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ فَاعْبُدِ اللَّهَ مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ 2أَلَا لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ3) [الزمر: ٢ – ٣]. *Haqiqa mun saukar maka da littafi da gaskiya, ka bautawa Allah Shi kadai kana mai tsarkake aiki dominsa. Ku saurara tsarkakakken addini na Allah ne”.* Hakanan yake cewa: (قُلْ أَمَرَ رَبِّي بِالْقِسْطِ وَأَقِيمُوا وُجُوهَكُمْ عِنْدَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ29) [الأعراف: 29] *(Ka ce da su, Ubangijina ya yi umarni da tsayar da adalci. Kuma tsayar da fiskokinku a kowane masallaci. Kuma ku bautawa masa kuna masu tsarkake bauta dominsa).* Ya kuma cewa a wani wurin: (فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ ال...