NASIHOHI

KADA KA DAMU DON AN ZAGEKA* - "Don wani ya zageka wannan ba wani abu bane da zakayi kumfar baki akansa, kuma ba wani abu bane da zaka ɗauki damuwa ka ɗorawa kanka akansa, domin lallai idan ka ƙyale wanda ya zageka ɗin, to shi da kansa zai dawo yayi nadama idan baka rama ba, ko kuma haushin zagin ya koma kansa" - "Aliyu bin abiy ɗalibin (r.a) yana cewa: ka rabu da wanda ya ya zageka, ka manta dashi kawai, domin lallai haƙiƙa hakan zai farantawa Allah mai rahama, kuma ya fusata shaiɗan, sannan kuma hakan zai azabtar da wanda ya zageka ɗin" تفسير القرطبي (٤١:٣٣) Allah yasan ya Mana hakuri a zukatan mu Ameen.*DUK ILMIN DA BABU ALLAH ACIKINSA:* - "Ilmi ilmi ne, amma ilimin sanin Allah shine yafi alkhairi, duk wanda zai mayar da ilmin da babu Allah acikinsa shine maƙurar neman ilminsa, to haƙiƙa bazai ga cikakkiyar nasara ba acikin ilmin nasa" - "Mutane sukan yawan ɓata lokacinsu akan ilmin da bashida cikakkiyar daraja, sai kuma su shagaltu daga neman wanda yake da cikakkiyar dajara ga rayuwar duniyarsu da kuma ta lahirarsu" - "Suna ganin tamkar sifantuwa da masu ilmin addinin musulunci tamkar ƙasƙanci ne da kuma ƙauyanci a garesu" - "Duk ilmin da babu Allah ﷻ acikinsa, kuma babu Manzon Allah ﷺ, acikinsa, to haƙiƙa kawai shirme da bankaura ne" -

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage