Yana cewa a cikinta: Lallai Google da Facebook da Twitter da Whatsapp da dukkan tsare-tsare (Platforms) ɗin sadarwa: Rafine mai zurfi, halayen mutane sun bace acikinsa. Hankulan Matasa sun gushe a cikinsa! igiyarsa ta tafiyar da kunyar yan mata, Jama’a da daama sun halaka! Ka kiyayi yawo a cikinsa, Kazama tamkar ƙudan zuma a cikinsa, kada ka tsaya ashafi sai mai kyau, domin ka amfanar da kanka dashi sannan ka amfani wasu. . Yakai Dana: Kada ka zama kamar ƙuda, wanda ke tsayawa akan komaai, mai kyau da mara kyau, sai ya dauki cuta ba tareda ya sani ba. . Ya kai Dana: Lallai Internet kasuwa ce mai girma, babu wanda ke bada kayansa kyauta, kowa nason wani abu kafin ya bada kayansa. A cikinsu akwai wanda ke son bata halaye amadadin kayansa! Acikinsu akwai wanda ke fitar da fikira rikitacciya, cikinsu akwai mai neman shahara, acikinsu akwai na ƙwarai, don haka kada kayi wata mu’amala da Mutum har sai ka bincika sosai. . Yakai Dana: ina kashedinka da kunce ƙulle-ƙulle, domin wasunsu tarkon...