ILLOLIN SANYA HOTO GA ƳA MACE A SOCIAL MEDIA
___________________________________ • Haƙiƙa babu Mace mafi Girman Kuskure kamar macen da zata Ɗauki Surar jikinta sanye da Kaya masu Bayyana Tsiraicinta sannan ta ɗorashi a Social Media, Mace mai irin wannan Tabbas ta kuka da kanta matukar bata daina ba Akwai Ƙalubale da zai rinƙa fuskantarta da Sannu zata Gane hakan daga Ƴan Iskan Samarin Social Media. • • Mafi Ganganci mace ita ce Wacce Take yin Post na Hotunanta ko wane kalan Mutum yaga Hoton da Abinda zai furta na Albarkacin Bakinsa, wani yace kinyi Kyau, wani kuma ya Tsine miki Albarka, ke ana yabonki a ganinki Kyakkyawace kina Washe baki ke Gaki mai Tarin Followers to ki sani duk abinda kika Ɗora da Hannunki Wallahi sai Ubangiji yayi miki Hisabi a Kansa. • • Yana daga cikin Illolin Ɗora Hoton Mace a Social Media shine, a yayin data Dora duk wanda yaga Post ɗin da Hoton dake jiki idan Abin ya bashi Sha'awa yakan yi Save a Wayarsa, daga nan ne zai samu yayi Post na Batsa da iskanci ya ɗora Hotonki a zuwan kece kuma duk Duniy...