SUNNAH TAFARKIN TSIRA
MAFAKAR SUNNAH AYAU!!!
Daga 🖊📝Ismail Hussaini Adam
+2349047958802
Haqiqah Babu batun Sonkai, Salafawa da 'yan izala sune ke da'awar sunnah Haqiqanin ta zallar madarar sunnah babu gauraye.
Dalilin wannan rubutu nawa:
Shine nuna mecece koyarwar aqeedar sunnah. Da manufar Izala da Salafawa akan sunna dakuma mecece asalin haqiqanin aqidar sunnah
********MECECE AQIDAH********
Aqidah: amahangar Arufai (Malamai)_ wata hanyace wacce mutane suka kebance yadda zasu yi addini karkashin wata mazhaba bisa fahimtar magabata na farko, Bugu da kariaqidah takasance abace wacce take a aikace da furincin baka banda qudirin zuci. Ma'ana Azuci ni musulmine kuma nayarda da dukkan shika_shikan musulunci ina aikatasu amma bisa mazhabar malikiyya. To idan hakane madogarata bani da Ikon tilasta maibin mazhabar shafi'iyyah ko ko hanafiyya. Bani damar cewa sai sunbi Hambaliyya
Idan mukayi duba danganeda yanayi nayanzu yadda rayuwa tashige rudani yadda Ake kawo abubuwa daban daban acikin addini. Dasunan addini.
Maluma na gaskiya suna iyakacin iyawarsu wajen wayar wa mutani kai dan ganeda hanyar tsira na addini, Amma saidai kuma akasi.
Anasamun wasu miyagu da suke juya hankulan jama'ah suna b'ata Da'awar tasu.
Danganeda hakane Aka rarraba addini gida_gida aka kuma kirmiro aqidoji iri daban_daban hakika koda yahudu da nasarah suma abinda yararraba kawunansu kenan rabuwar kan maluma.
******Mafakar sunnah dai sune****
Marubuta da wa'azi da walima Wadannan sune hanyoyin da. Sunnah suke yada da'awarsu. Sabanin sufaye Shi'awa da 'Yan dariqu. Su suna yada aqidun sune da sha'irai (mawaqa) da Majalisi dakuma Mawalid, idan akace mawaali shine jam'in maulidi.
To A inda gizon ke saqa kuma, shine: Akan samu sa'bani dan ganeda wasu al'amuran na Hanyoyin yada da'awoyin nasu.
Misali
'Yan izala Da Salafawa sukan soki mauludi da zaman da'ira da Majalisi, dama kuma wake waken da yan dariqu sukeyi. Su kuma yan dariqu Basuda hanyar dasuke yada manufofi da da'awoyinsu sama da wadannan hanyoyi, Dan hakane suma suka sha AlwasAnfagdaura kambun yaqi da dukkannin wanda zai munantawa hanyar da'awarsu.
******Tasirin tarbiyyar aqidu******
IZALAH SALAFAWA
Yan izala da salafawa mafiya yawancin makarantunsu haddane da hadisai sai Tauhidi saikuma wasu littattafan addini a matakin farko kuma suna Anfanine da mashabobin makka da madina. Yawancin littattafansu wallafar can ne da sharhohin magabatansu.
SHI'AH DA DARIQU
Su kuma yawancinsu suna anfanine da mazhabobin iran da iraqi kuma afannin ilimin farko yawancinsu karatun tsangaya sukeyi. Sai agaba sunfi bada karfi wajen ilimin tarihi da baitoji yabo dana dafawa wannan dalilin ne ma yasa ake samun mawaka dayawa acikinsu.
*****"Nuni sananne dan gane da da'awar sunnah""""""""
Maganar Gaskiya izala da salaf munada kyakkyawar manufa akan addinin musulunci kama daga maluman mu dama marubutan mu dama Mu dalibai bakidaya . Burinmu Azauna da juna lafiya da lumana.
Yan uwana masu karatu kusani cewa manufar wannan rubutun nawa shine in bayyana mecece haqiqanin Sunnah
Kuma suwaye Ahlussunnah na gaskiya
Danhaka na rarraba rubutun kaso uku
Wannan shine nafarko agaba zakujini da wasu kamar haka:
******Haske Akansu******
###Suwaye Ahlussunnah?..............)
Dukkan wanda yariqi sunnah ta annabi kuma yake kokarin dabbaqata kuma yake nesanta daga barna da rarraba kan al"umar musulmi.
Dakuma
###Sunnah ba Aqida bace!.............)
Ahlussunnah yana suffantuwane da kyawawan dabi'u baya neman ilimi domin muqabala ko dan.yakare aqidah ba.
Comments