MATSALAR AQEEDAH

 GASKIYA AKWAI MATTSALA!!!!

Sau nawa kake zama domin Bincike ko sauraron Yadda zaka gyara Ibadarka?????

         Sau dadama idan na kadaita sai nayita tunani dan ganeda lammarin gudanar addini agun wasun mu. Zakaji mutum nakiran kansa musulmi amma farillan alwala ma bai sani balle in ta 'baci ya gyara farillan sallah ma bai saniba balle inyayi Rafkanuwa yagyara. Ko na wanka ballema ilimin gyaransu.

    Wayyoooni duniya ina zaki damune kowa kagani abinci kawai yake nema kokuma yadda zai huta ko yadda zaiji dadin duniya gaba. Saidai kash itakuma tafiyarnan da take gaban mu batta da rana. Kawai zuwa take kwatsam kara zube ba zato ba tsammani.

    To taya zamu tara guzirin komawa ga mahaliccin mu domin samun hujja garemu aranar sakamako?

    Ansa

    Mukoma munemi ilimin addini mugyara ibadu da mu'amalarmu kafinnan musami hanyar tsira. Wani abin ban takaici shine yawanci mukan jahilci lammarin addini bawai don rashinsaba sai don aqidanci. Mutum baida karatun komai jahilin kauye afagen addini amma saikaji na karyata abubuwan da malamai ke fada dan ganeda hukuncin halasci ko haramcin wani al Amarin addini. Dalili kuwa shine don aqidarsu ta banbanta, Alhali baida hujja ta aya ko hadisi data karyata al'amarin dalili kawai don malumansu basayi yan abiyari (inbasu wane bazamuyiba).

    Wannan shi ake kira da shi'anci ashari'ar musulunci ma'ana raba kan al'umar musulmi. Tahanyar sabawar fahimta ko mazhaba. Abubuwan da kejawo haka sune:

    _Jahilci

    _Son zuciya 

    _Son shahara

    _Munafinci

          ***JAHILCI***

    Idan jahilci yayi naso (katutu) azuciyar mutun saikaga na karyata koma mene ne addini ni kuma in yayi shugabanci zai dinga shirme yayita kawo jahilci alammuran dasunan gyara daga karshe zaiyita kokarin fada da malamai idan suna fada masa gaskiya. Jahilci nasa girman kai da hassada matukar maishi na tare da masu ilimi kuma akayi rashin sa'ah yawuce su wata daukakaka tarayuwa.

       ***SON ZUCIYA***

Idan mutum nada son zuciya komai aka fada bazaibiba sidai yakowo tasa abi. Koda tasa hanyar me raunice zai toge yadage akan sai anbi tasa daga karshe in anki zai fara neman mabiya daga baya saikaji ya Fidda tasa sabon kungiyar daban ko juma yafandare yayi reshe akungiyarsa daban.

    ****SON SHAHARA****

    Mafiya yawanci anfi samu daga wanda suka 'Danyi karatu amma bamai nisaba sunason taka hawa mai nisa amma kafarsu baikaiba. Burinsu dai komai zai wakana yazam anyishi harda furucinsu. Amma basuda cikakken ilimi abangaren irin wadannan ywanci akansamu masu kyakkyawar manufa amma rashin ilimi mai nisa yana wargaza manufar nasu.

    Yakai dan uwa shawarata gareka katsaya iya matsayin ka kabar abinda Bakasaniba. 

    Masu hikima nacewa Bansaniba shima wani yankin ilimine.

    

      *****MUNAFINCI****

    Akwai wasu burinsu kawai azagi musulunci da musulmai. Zasu tsaya kai da fata su tabo wannan aqidan da wata ta daban, Harsu haddasa wata rigima tsakanin musulmai wadannan basuda wata kyakkyawar manufa akan musulmai wasunma bamusulmai bane burinsu su wargaza wata shiri ko wata tanadi wacce musulmai sukeyi, ko don su raba kawunan al'umar musulmi.

    Allah katsaremu daga sharrin makirai da fajiran munakan addini. 

    Allah yamayar da makircin garesu dasu da wanda suke sasu.

    Allah kabudemana kwakwalenmu don gujewa afkawa rudanin addini.

    Allah  kabawa maluman mu damar isar mana da gaskiyar koyi na Addini.

    

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage