KAWA TAGARI
KA KYAUTATA ZATO GA ALLAH! - "Rashin kyautata zato ga Allah ba ƙaramin sharri bane ga al'ummar musulmi, domin haƙiƙa hakan na iya haifarwa bawa saɓon mahaliccinsa Allah" - "Shi ɗan Adam gaggawa ke gareshi, kullum burinsa da zarar ya nemi abu, ya same shi nan take, da zarar ya samu jinkirin biyan buƙatarsa, sai kaji ya fara riya mummunan zato acikin zuciyarsa, kuma wannan lamarin har akan ubangijinsa yana riya hakan" - "Sau da yawa bayan kayi addu'a, ka roƙi Allah biyan buƙatar wani abu, a dalilin jinkirin amsuwar ibadar taka, sai kaji tamkar addu'ar taka bata amsu ba a gurin Allah buwayi, sai kaji tamkar ma ka haƙura ka ɗebe tsammani daga samun nasara a addu'ar taka, amma baka sani ba, Allah shine yasan daidai gareka, kuma yana amsa addu'ar bayinsa ta hanyoyi masu yawa, a kuma lokacin da yaso, sannan wani lokacin kuma abinda kake roƙonsa ɗin ba alkhairi bane gareka, sai ya sauya maka da mafi alkhairi gareka fiyeda abinda ka roƙeshi ɗin, to ...