KAZAMO MAI YAFIYA
KA YAFEWA MUTANE!
-
"Sau da yawa ɗaukar fansa akan abinda akayi maka na kuskure yakan zo da nadama tun a wannan duniyar, koda kuwa ganganci akayi maka to lallai yafiya itama alkhairi ce gareka har zuwa ranar lahira"
-
"Kayi ƙoƙari ka zamto mai yawan yafiya da kawaici ga jama'a, bayyanar da yafiya da nuna tausayin ka ga jama'a, shine zaisa kaima Allah ya yafe maka, amma da zarar ka zamto mara tausayi da imani ga bayin Allah, shima Allah sai ya cire tausayinsa daga gareka ya barka da baƙin halinka, ƙarshe kuma kaje ka haɗu dashi yayi maka hisabi abisa abinda ka aikata ga bayinsa anan duniya"
-
"Ka yafewa mutane waɗanda suka yi maka ba daidai ba koda kuwa su ɗin basu nemi yafiyar ka ba abisa laifin da suka aikata maka, riƙe fushi acikin zuciyarka babu abinda zai haifar maka face cutarwa, da zarar ka yafe, kaima zaka sami sauƙin raɗaɗin abinda suka yi maka na laifin, gwargwadon riƙonka dasu acikin zuciyarka gwargwadon cutarwar da zakayi ga zuciyarka, amma idan ka yafe, sai kaima Allah ya yafe maka sannan ya sauƙaƙa maka ƙuncin dake cikin zuciyarka, Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace: ku yafewa junanku, kuma sai Allah ya yafe muku"
Musnad Ahmad (7001) Sahih
Comments