MAJOR DA MUQARRABANSA AN KYAUTATA MUSU ZATO
ASHE SUNE SANADIN HADA BANGARORIN BOKO HARAM YAKI DA JUNA Jama'a ku nutsu ku karanta wannan bayanan da kyau Tsarki ya tabbata ga Allah, rikicin bangarorin kungiyar Boko Haram abin boye ya fara fitowa fili, marigayi shugaban sojoji Janar Ibrahim Attahiru da shugaban leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaro na rundinar sojin Nigeria marigayi Birgediya Janar Abdulrahman Kuliya sune sanadin haddasa tsoho da sabon rikici tsakanin 'yan Boko Haram wanda ake kyautata tsammanin Shekau yayi mushe A cikin wani sabon rahoto wanda jaridar PR Nigeria ta wallafa jaridar da take da kusanci da rundinar sojin Nigeria, tace marigayi Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya shine yake jagorantar tawagar mayaka sojojin kundunbala a lokacin da marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru yake matsayin babban kwamandan rundinar Operation Lafiya Dole a Arewa maso gabashin Nigeria Kafin a cire shi, a lokacin wasu tawagar mayakan Boko Haram sun tuba sun mika kai wato sun yanke shawaran ajiye makamansa wa run...