HA'DIN KANMU HARYAR TSIRARMU
HADIN KANMU HANYAR TSIRARMUN
Rayuwa ta ishemu Wa’azi
Malamai kuji tsoron Allah wajen Karantarwa kada kusa Son Zuciya. Domin tsira da mutuncinku aduniya da tsira da imani aran Qiyama.
Dalibai muji tsoron Allah, Mufahimci junananmu Yayin Sa’bani, Kada Muce komai Malam wane yafada Gaskiya ce, Binciken Yafi Sauraron Mu yawa.
Muyi riko da Tsarin Allah Mugirmama junan mu kada Murarraba, Rabuwa A Al’uma fitinace, Yawan jayayya yanasanya Masu Son zuciya yad’a ‘Barna kuma yakan sa Wasu gaba da juna Bisa Rashin Dalili.
Mukula Da amanar junan mu gun jaddada Sa’bani, Muyawaita zantawa da juna domin warware Sa’bani mukula da Wadanda ke son tada fitina a Addini Sud’in wawayene kuma jahilai, danganeda Harkokin Addini Basusan komai ba Sai musu da Cinzarafin Malamai.
Akowace aqeeda akan iya Samun masu mummunar manufa da Kuma Son zuciya. Babbar matsalar rayuwa Shine aiki da Jahilci, dakuma Son Zuciya.
Mu Janye Gaba da juna danganeda bambamcin aqeedah. Meyin hakan Bai fahimci addini ba, Son duniya da Son zuciya Shiyake sa Mutum yakasa Barin Mummunar Aqeeda da Mummunar halaye a rayuwa da Addini.
Addinin mu yatanadar mana komai, Bamu Bukatar wata hujja ko Ra`ayin Malam wane, idan Nassi ya inganta kawai Mu`aiwatar. Maluman mu nada da Yanzu Sun mana gata.
daga Matsala ta Kunno kai Sai mubude littafi. Idan muka Zauna Kushe littafan mu, da muzantashi. Zamu wayi gari Muna Qauracewa a gareshi. Har yazamto mun Halaka kamar Yahudu da Nasara.
Idan Munji gyara Muntabbata gyara ce to yazama wajibi mugyara, Kada Mutsaya Sauraron Ra’ayin Wane ko Matsayar wani Malami, Kowani ‘Dan adam ajizine, Malam Wane Ba Annabi bane Yakan iyayin Kuskure Ko Qarancin Tunani.
Addini dayace Sa’bani Sharri ce kuma fitinace, Hanyar gujemata Shine bincike da Neman Ilimi. Da Gujewa Rudin Duniya dakuma Komawa ga Allah ﷻ.
Idan kai ba malami bane kadaina katsalandan aharkar Fatawa ko Matsayar malamai, Yin hakan Shike janyo d’alibi yaraina Hatta malamin dake karantar dashi.
Malamai Su hada kansu Domin kaucewa yawan Sa’bani, Rashin Zantawa da juna shikesa malamai Sa’bani wani abinma labari kakeji daga ‘Dalibanka wani kuma Baka gama jin Kammalallen saba. Yazama dole Dole muyi Bincike.
Idan kasabawa Maluman dakake tare dasu kadauka kaine akan Kuskure, Ko baka fahimcesuba Kuma kana kyutatamasu zato amma ayimaka gamsasshiyar bayani. Amma idan Kaki kuwa, Shaid`an Zai Rinjayeka Ko da akan Gaskiya kake. Domin Kura ma takan Cinye Dabbar da ta Ke´bene.
Laifin Wani baya shafan wani agun mu mu ‘Yan adam, Kada Wani wanda ba aqeedarku daya ba yayi magana kayanke hukuncin Dukka aqeedar haka suke. A`a Shidai haka yake amma akwai Wasu nakirki acikinsu.
‘Dalibai Mudunga Girmama maluman mu, Munemi ilimi ba Son shaharaba. Babu amfanin ilimi idan bai zamo hanyar Tsirarmu ranar Lahiraba.
Idan wani yahalaka Sanadinka kana da Kaso cikin Sakamakon da za’a Qaddamar masa.
Idan Hasashen Mutane gaskiyace! Tabbas akwai wadanda ke kar’bo kwangila domin ‘Bata Addini. Amma kuskurene muyi Jam’i, Dole akwai wadanda da gaske suke Kuma Sunada yaqinin Tabbatuwar su akan Gaskiya Suke.
Dole ne Mu martaba Magabatan mu, Idan Munga kuskurensu mu nema masu gafara. Mudaina Tonan Silili ga ‘Yan uwanmu, Idan za’ayi tonon silili wa kowa Babu mai tsira Gaban Allah, Yawaita Nasiha Itace Mafita.
Munbar koyarwar addini, Mundauki Al’adar yahudawa, Amaganganun Mu komai yazo furtawa Muke babu Tantancewa. Muna da Laifi amma hangen na wasu yahanamu neman Afuwar Namu.
Muyo ‘Da’ah Cikin umarnin Annabi nadaga abinda yazo cikin Alqur’ani da Hadisi, Muhanu daga abinda ya tsawatar, Mubautawa Allah cikin Koyarwarsa ﷺ.
Kada mu yarda da Munanan kalaman da ake furtawa ga Sahabbansa رضی الله عنهم ورضو عنه, Hakan zai iya taba darajarsa ﷺ, Mud’auka Cewa Ma’kiya addinine Suke Kokarin raba kawunan mu.
Inmunga Matsala a Alaqarmu ta Aqeeda Muzauna Muwarware mukoma ga Allah musamu mafita. Na tabbata rayuwar mu zata Sauya.
Bissalam Nine naku Ismail Hussaini Alpholtawy
***SA’KON FA’DAKARWA GA AL’UMAR MUSULMI ****
**lokaci yaquremana**
Idan Har a kullum zamu dinga Nisantar Wa’azine dan ana fad’an abinda Yasha Bamban da Ra’ayinmu to Tabbas Zamu Rinqa Nesantar Haske muna Tutsa kanmu cikin Duhun Jahilci, da kafirci,
Idan Har Sai abinda yayi daidai da Da Ra’ayoyin Mutane Za a Ayyadar aduniya, Tabbas da Wuta ba ayitaba Sai Aljannah inkuwa anyisuma Ko da anzo Duniya babu mai bin Allah.
Yawancin Mutane Tunatarwa takan Zakke Musu, yayinda Suka tuno da Me zasu tarar a Filin hisabi, Sai imaninsu ga Allah yaqaru, Inkuwa ankoma Shagalin Duniya Kuwa, Allah ma Wasu mantawa suke da Wujudinsa.
Idan har Zamuce Wai dan Malami yafadi Sabanin Ra’ayin mu, yazamo mutumin banza to Tabbas imani a azuciyar mu zatai wahalar dasuwa. Domin ayyukanmu munana sunfi Yawa, Sukuma Malamai burinsa mu rage.
Bai zamo dole ace wai Dukkan abinda Zuciya ta natsu dashi yazama Alkhairiba Iyakar Allah shine abinda yahana, koman Jahilcin Dan Adam, daga yashigo Da’irar Allah ta Haramci, na abinda yaqetare iyaka, Yasanta Saidai ya zakkemata domin Son zuciyarsa.
Kamar Kid’a ma aiya haramta amma muna Saurara kuma yanayi mana dadin ji. Ammafa haramunne. Kuma ma na sanyamu Shagala da Barin Aikin Alkhairi.
Kowani dadi inhar zai hanamu, ko ya nesantamu da jin dadin Lahira Allah kamusanya mana Shi da Mafi alkhairi, Kaine masanin Sirrin asirin Sansanin Sararin Sababin Alkhairan Duniya da Qiyama.
Mun manta da Yunqurin Shaid’anu akanmu, Muyi nazarin hakan cikin Rayuwa: Sau dadama abinda Allah yahanemu
Zuciyar mu tafison Mu’aikata, Bisa Rud’i da Rinjayar Shed’anun duniya.
Bai zamo Lallai ba ace; ko Wani abinda Yayi mana dadi Yazama shine halal ba, Tabbas Halal shine abinda yazamo akwai yardar ubangiji acikinsa Babu Shakku bare kokonto.
Yawan Fad’a da gaskiya yanasa Qeqashewar zuciya, Tabbas idan kaji Gaskiya koda abakin Abokin gabankane, yi kokari ka Kar’beta amatsayinta na Gaskiya, Inkuwa kaqita kuma kana so ka mayar da ita abin ‘kyama, to Tabbas Zaka Sha Mamakin duniya, Domin Sunan Allah kake yaqa wato Al_Haqqu.
Ai koda ma Ace zaka Qaryata Gaskiyar MA ayarjemaka bisa yadda kake da iko cikin mutane, daga baya Idan gaskiya tabayyana zakasha Kunya, Idan ma Allah yasoka da Shiryuwa ne Saika gyara, inkuwa bakada da rabon haka, Kamutu Ayimaka Hisabi na ‘Batar da Mutane dakuma Aikata Mummunar aiki.
Dama habaicinnan damuke yawanyi wa juna, da Zagin Juna A Social Media, Amatsayin Sa’banin Ra’ayi ko aqeeda, Da ayoyin Qur’ani muke yad’awa haka da babu ayar da zaka Duba baka Sametaba a Internet. Ko Hadisan Annabi.
Muyi Tarayya daku wajen yada ilimi na Addinin Musulunci musamu lada, sa’bani bazai ta’ba qarewaba A Addini matukar zamu dawwama cikin yiwa juna Raddi da Jahilci. Muyawaita yiwa junar mu NASIHA.
Wai ko Munmanta da Cewar mu Musulmai ne, Akwai Ranar fa dazata zo Zamuyi Kewar inama adawo damu Duniya Muyi koda Tasbihi guda dayane Mumutu, Dakuwa Munso hakan. Amma babu dama ankulle kofar Nadama da Aiki, Sakamako kawai ake ba Qaqqautawa.
Kamar Misalin Jarabawar Duniya ce; Sai Ranar raba Result Saikace Ka manta Maths da English baka karasa Amsawa ba, Dan haka abaka dama kaje ka gyara aikuwa lokaci kam yakure.
Allah ka Albarkaci Rayuwar mu da ayyukan Nagarta Dakuma zuciya mai imani da dawwama a imani Har mu samu Rabo Aranar Sakamako. Allah kajikan iyayenmu matattu.
Naraye Allah ka qara Masu Lafiya da imani da Tabbatuwa Akan imanin Har Mu samu rabo na Lahira Mu dasu Muyi Tarayya cikin Samun kyakkyawan Sakamako anan duniya da Gobe Qiyama.
** KYAWUN FATANA GA AL’UMAR MUSULMI**
Nayi nazari cikin tsarin Rayuwar Malumanmu na Musulunci, acikin Kyautata zatona danayi Garesu da kyakkyawan Fata sai na hango Maluman mu na Najeriya acikin Da’irar Son Ma’aiki ﷺ da kishin Sahabbansa da Iyalan gidansa Allah yaqaramasu Yarda.
Inda Lissafin yatiqe dai Munrabene Cikin aqidu Domin Nuna Kishi ahalarar Soyayya,
Tayadda ‘Dariqu Suke jaddada Soyayya da Girmama waliyyai da Shehunai da Sharifai da Sufaye Domin kasancewarsu Masoya kuma dangi Jinin Fadima Yar Ma’aiki ﷺ.
Sukuwa Ahlussunnah kishinsu ya Ta’allaqane Akan Hidimtawa wa ADa’irar Ibada bisa Tafarkin Sunnah da gyara Ibadoji da kiyaye hakkin Annabi da Alqur’ani da Kore Shubuha a Addini, Bisa Yaqi da Bidi`a da Munanan aqidun cikinsa.
Haka masu jaddada kishin Ahlulbaiti (Ahlul Kusa’i) Suma dai Soyayyace Ragamar su cikin Nuna Hidimtawa wa Sayyada Fadima ‘Yar Ma’aiki ﷺ da Zuri’ar Gidanta Abangaren Sayyadina Ali Allah yakaramasa Yarda.
Tabbas gida d’aya Muke karkashin inuwa guda Muke, Matsalar dake faruwa acikinmu itace wasunmu na aiki da Jahilci da kuma Son zuciya bisa Siyasar Masu Neman Duniya da gurbata Addini. Masha Allah, Malamai na ya’kar tsarin da salon tsarin Tabbatar da Sunnah gami da kore Shubuha da qarfafa Shari’ar Musulunci, Muma muzamto wakilan Musulunci kada musanya ido haka kurum muna kallonsu Kamar Telabijin, Ayi muji dadi dan anyi Nasara Akan Ma’kiya Muyi dariya,
Idan an kore Kazantar wasu To mu abinda yakamata Muyi shine ina datti yake ajikinmu muma Muyi kokari mu wanke, Dan kuwa Malumanmu Tabbas zasu Shud’e kuma Duniya na kara Gur’bata ga kuma Mummunar nufin Yahudawa da Nasara. Muyi Kokarin gyarawa kuma mu ankarar da juna danganeda Zamantakewa da Ibadoji.
Tabbas Malamai gatarin sarane agaremu kuma tsanin hawane mai qarfi bisa hanyar tsira da Digar tono asiran ma’bb’bugar Alkhairai. Inhar mukayi sakaci suka Shud’e bamuda Masu maye Guraben su Tabbas Munyi Kuskure Mafi girma, Ina mukeda yaqinin Tabbatuwa, Yaushe Za’amaimaita Kamarsu Sheikh Ismail Idris da Kuma Ja’afar da Albani.
Ya za’ayi Duniya tamance da ginshiqannanan namu watau Khulafa’Urrashidun, Ina za’ayi jagorori Kamarsu wadanda burinsu Kullum cigaban Addini. Akwai ire_irensu Wadanda ban ambata ba Ammafa Sun Shud’e Wadanda sukayi hidima ajanibin Ma’aiki ﷺ da Halarar Tsaftace Al’uma daga Jahilci da Duhun kafirci.
Saidai kuwa Jimamin mu Kullum Shine; Gamu karkashin inuwar Rumfa guda amma Wasu na Kokarin Jijjige rumfar ga barazanar Abokan Gaban dake tunkaran mu, hakan na faruwane ta silar Wasu wawayen cikin mu bisa Siyasar Masu Son zuciya da marasa hankalinmu.
** Mecece mafita?**
Mafita agaremu Shine komawa ga Allah dakuma hadin kai wajen aikin Alkhairi da ya’da Addini da bawa Addinin kariya takowace ‘Bangare tareda aiki da ilimi da tsoron Allah wajen Yad’a ilimin, Malami kuwa Yatsaya amatsayinsa na Fannin dayasani. Allah ne Masanin komai, Ba aikin Musulmi bane Yanke hukunci da Jahilci ko Son zuciya.
Wani Tunani dake Zuwa cikin zuciyata Mai cikeda mamaki gamida Amsarta, Itace;
Anya Kiristoci? Yaya Sukeji ko kallon Al’amuran mu na yawan Sa’bani?
Kwatsam Saina amsa da cewa, Ai mu Munada yaqinin munakan Gaskiya Saidai binta yayi mana wahala bisa Rinjayar Shed’anu da kuma kasawa ta Dan Adam. Su kuwa kullum wa Duniya kadai Sukewa hidima, Sunbar Addininsu ba tsari Matansu Na fita yawo tsirara ba Mutunci Kamar rayuwar dabbobi, Mukuma Kullum burinmu Ya’kar Irin Wadannan tsarikan mukeyi, Mamakin danake garesu Kullum Shine Rashin Kulawa dasukewa ‘Ya’yansu Tayadda Suke Shigar banza Kamar Basu da Addini Na Tabbata Addinin Kiristanci bai karantar da hakan ba.
**Godiyar mu ga Allah Mu Musulmi **
Addinin mu yagamamana komai kuma mun riski ilimi da Dukkan wata falalar rayuwa da Tsarin Zamantakewa na ingantacciyar Rayuwa da tarbiyya dukkan mai akasin Kyawun hali da dabi’u tabbas yakauce ne wa koyarwar addinin mu Na Musulunci.
**Kira ga Dalibai matasa**
Yan uwana Matasa Dalibai!!! Murabu da malamai Abangaren wa’azantarwarsu Muzauna amajalisi akoyar damu Ibadoji da Tsaftace Rayuwa gamida tarihohin Shiryarwa Mugujewa Shagalar Rayuwa da rudin Duniya Munemi halali kurum akasuwancinmu.
Mukuma tayasu wajen Yad’a karatuttuka a Social Media tahanyar Recording and Sharing Audio da Video da Pictures quotes gamida Rubuce Nasihohi da Wallafa manhajoji da Websites da Rubuta Text wa ‘Yan uwa da abokan Arziqi. Domin sanya ilimin Addini cikin duniyar Network da yaqar Shubuhar mutane da wautarsu na Zagin Malamai da Hauka.
Sannan hakan zaisanya Mu tanadar da babban Guziri wa Yan baya, Domin kada Su iske Mu bamu bar musu kyakkyawan koyiba Sai tarin Shubuha gamida Sa’bani, hakan zaisa Masu raunin imani acikinsu Kokonta cikin imani dama Shakku a Addini matukar Basu tarar da abinda zai Qarfafesu na matsaya guda ba, Sannan Abin koyi garesu na Fahimta, Hakan zaisa su Rafkana.
Ya Allah Kaqaramana imani da Ikhlasi da Tabbatuwa Akan imanin Harmu sameka muna Sallamawa gareka Allah karabamu Da Riya da Son zuciya.
Allah kajikan Magabatan mu, Mukuwa Allah kabamu Shahada.
Daga ´Dan uwanku Ismail Hussaini Alpholtawy
ALLAH kajiqan Mahaifina kakara wa Mahaifiyata Lafiya, ALLAH Kasa mucika da Imani.
Comments