RAYUWA ABAR TSORO CE
*BABU UZRI BAYAN MUTUWA* - "Duk wani uzrin da bawa yake ƙunshe dashi a lokacin rayuwarsa ne kaɗai yake da ikon aiwatar dashi, yana mutuwa shikenan uzri ya ƙare, abinda mutum ya shuka shi zai girba" - "Bayan mutuwarka a lokacin da aka ɗauke ka izuwa makwancin ka, komai yana jin abinda kake faɗa ga masu ɗaukar ka, amma saidai su mutanen da suka ɗauke ka ɗin basa taɓa jin abinda kake faɗa" - "Ya kai miskĩni! Lallai ka sani cewa fa, a lokacin da ka mutu shikenan taka ta ƙare, bayan an ɗauke ka acikin makara babu wanda yake fuskantar halin da kake ciki balle ya karɓi ƙorafinka, face dabbobi ko bishiyoyi, sai kuma ubangijin taliƙai, to ka gabatarwa da kanka wani alkhairi wanda ba za kayi nadama ba bayan mutuwarka"