AL'UMAR MUSULMI AYI HATTARA

AL'AMARIN SA'IDU MAIKWANO MAI DA'AWAR 'YAN BAZATA ABIN TSORO NE

     Daga Datti Assalafy 
Allah Ya jarrabi Musulunci a Nigeria da wani irin Malami mai suna Sa'idu Aliyu Maikwano wanda yake da'awar wai Salafiyyah a Gusau jihar Zamfara, yana kafirta Manyan Malamai tare da bidi'antar dasu, yana kuma jifansu da kalmar khawarijanci, wato halasta zubar da jininsu
Na saurari tsokacin da Maikwano yayi akan Khadimul Qur'an Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu (Rahimahullah) da kuma su Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar Izala na duniya
Sa'idu Maikwano ya kafurta Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu, har ma ya soki Sheikh Abdullahi Bala Lau don ya yiwa marigayi Sheikh Isyaka Rabi'u addu'ah na samun rahamar Ubangiji
Sa'idu Maikwano yace Sheikh Isyaka Rabiu kafuri ne, kuma mushriki, wai Sheikh Isyaka Rabiu yayi hidima wa kafurci da shirka ne kafin ya mutu, wai bai kamata Izala ta masa addu'ah ba
Na girgiza matuka da jin wannan munanan kalamai da suka fito daga bakin wannan Malamin bogi, sai nake ganin kamar yana da matsala na rashin lafiya a kwakwalwarsa, wato ya kamata a killace, domin wannan Malami zai iya haddasa fitina
Na rantse da girman Allah idan za'a tara irin Sa'idu Maikwano dubu har su mutu ba zasu iya yiwa addinin Allah hidima irin wanda marigayi Sheikh Isyaka Rabi'u yayi ba
Sheikh Isyaka Rabiu Mahaddacin Qur'ani ne gangaran, Sa'idu Maikwano ba Mahaddacin Qur'ani bane, Sheikh Isyaka Rabiu har daren ranar da zai koma ga Allah Qur'ani yake karantawa da ka
Sheikh Isyaka Rabiu ya sadaukar da dunbin dukiyarsa wajen yiwa Qur'ani hidima, dubannin mutane Musulmi sun haddace Qur'ani a karkashinsa, bawan Allah irin wannan wai shi Sa'idu Maikwano ke jifa da kalmar kafurci, wa'iyazubillah!
Sa'idu Maikwano yaci mutuncin Manyan Malaman Sunnah tun daga kan su Sheikh Abdullahi Bala Lau, Sheikh Dr Bashir Aliyu, Sheikh Dr Sani Umar rijiyar Lemo, Sheikh Aminu Daurawa, Sheikh Professor Dr Mansur Sokoto da sauran su, bai bar duk wani babban Malamin Sunnah ba sai da ya bidi'antar dasu, daga karshe ya jefesu da kalmar khawarijanci da ikhwaniyanci
Wannan da'awar ta Sa'idu Maikwano da'awace irin ta 'yan bazata, wato Missionary, arnan da suke wzuwa kasashen larabawa su koyi addinin Musulunci su dawo suna kokarin bata darajar Malaman addinin Musulunci domin a cutar da addinin Allah, a halakar da jama'ar Musulmi
Ba shakka Sa'idu Maikwano annoba ne da yake fesa mummunan guba a cikin da'awar Musulunci a Nigeria, ba da'awar Salafiyyah yake yi ba, da'awar 'yan Missionary ne, ya sani ko bai sani ba
Sannan daga karshe na fahimci ya kamu da mummunan cuta na hassada da kyashi a cikin zuciyarsa, shiyasa Allah Ya kaskantar dashi, ba inda aka sanshi sai garin Gusau, yayi yayi a sanshi abin ya gagagara, shiyasa ya dauki hanyar 'yan bazata yana lalata darajar Malaman addinin Musulunci watakila ta hakane zaiyi suna, amma mummunan suna
Sheikh Bello Yabo Sokoto shine maganin wannan Malami mai da'awar 'yan bazata, Malam Bello Yabo Sokoto dama ya fada mana gaskiya har wasu ke jin haushinsa, yace Maikwano abokinsa ne, baiyi wani karatu ba sai na iskanci, da takardun bogi yaje Saudiyyah aka ganoshi aka koreshi daga Makaranta
Yaa Allah Ka tsare mana Malaman Musulunci daga sharrin 'yan bazata Amin

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage