QALUBALE GA RAYUWAR 'YAN MATA

 📝  ✍️ ISMAIL HUSSAINI ADAM SMART DAN AREWA


   ******* GABATARWA *******

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu mai karatu.

       Zanyi wannan rubutunne don nuni zuwaga yan uwana maza, domin kusan wa zaku auro ku kawo cikin gidanku, amatsayin abokiyar zama. Mata kuma su san dawa zasuyi qawance don gudun faďawa akomar halaka. Inda hali kutsaya kukaranta gabaki ďaya, domin zaka/zaki k'aru kuma inshaa Allahu zaku rabauta da waďannan zantuka nawa.

      Ina bukatan addu'arku Allah ya haskaka qabarin mahaifina, dana mai karatu idan kuma suna raye, Allah yasa mugama dasu lafiya yakuma basu rabon cikawa da imani. Allah ka albarkaci rayuwar lahaifiyata da ayyukan alkhairi daku mumaďin gabaki ďaya.


******** 'YAN MATAN JAMI'A ********

   Allah sarki rayuwarsu gwanin birgewane, saidai kuma abin tausayine awani bangaren, tayadda zaka samesu mafi yawancinsu akwai tsaftar jiki dana tufi. sannan sun san yakamata matuka, Saidai wasu acikinsu suna son yin aure kuma Suďin sun kame kansu. amma rashin dama takansa wasu acikinsu afkawa izuwa ga zina, Allah yakare.

   Hakan yana faruwane don rashin samun dama daga iyayensu. Zasu fidda gwani amma sai suce sam sai kin kammala karatu, sun manta da wasiyyar manzon Allah (s.a.w).

  Wasu kuma suna sheke ayarsune kawai tahanyar biyan bukatarsu ga maza, aduk sadda sha'awarsu ta motsa. Wasu kuma na fama da jimamin rayuwa tayadda suke fama da fuskantar barazanar lecturers lalatattu, da yunkuri batamasu tarbiyya da fansar jarrabawarsu da mutuncinsu. Iyaye ayi hattara zaku iya shiga wuta akan hakkin 'ya'yayenku don rashin sadaukar musu da hakkinsu daya rataya akanku.



********** 'YAN MATAN LUNGU **********


   Idan akace matan lungu: sune mata masu talle akan titi, dakuma lungu da sashen unguwanni da sakokin ma'aikata, da shaguna (Kwantinan) kasuwanni. irin wadannan matan, idan basu sami kulawar tarbiyyaba sunfi kowasu mata sharri. Domin awani bangaren sukan 'boye kamarsu suyi kama da mutanen kikrki amma sam bahakan bane azahirance.

  Kuma mafi yawanci acikinsune ake samun masu sace_sace, da bin maza bayan sunyi aure. domin sun saba da rike kudi masu kauri ahannayensu, ayayin budurcinsu.

  Hakazalika wasu acikin sunma suna saida budurcinsu kafin aure, a son zuciyarsu kokuma ara'ayin iyayensu mata. Ko uwayen goyensu na bariki.

tayadda sukan taradda wulakanci agun mazajensu, dalilin rashin budurci bayan sunyi aure, hakan yake tursasu fita karuwanci bayan aure, ko sata wa mazansu na aure.



********* 'YAN MATAN BARIKI *********

   Irin wadannan matan basuda mutunci. wanda su kansu sun yadda da hakan, kuma suna iya furtawa da kansu cewa su marasa kunyane amma daga fitsararrun cikinsu.

Irin wadannan matan sukan tasone aguri mai lalacewar tarbiyya.

    A gunda iyayensu ke zaune babu tarbiyya kuma iyayen basu kulawa da tarbiyyarsu. kuma babu addini agunda suke zaune. Saidai holewa da sha'anin duniyanci dakuma ta'ada, da muta kabbaranci. Ga uwa uba rashin dattako don ko waye 'yar bariki zata zaki asalinsa ko da kuwa shugaban unguwarsune ko sarkin gari. Wadannan matan ko acikin garine shigarsu daban take sune Manzon Allah (s.a.w) yayimanz ishara dasu acikin hadisi ruwayar bukhari da muslim '' Akwai wasu nau'in mutane da Annabi baigansuba amma zasuzo anan gaba yake fadawa sahabbansa. Yace dasu dukkan wadannan mutane 'yan wutane.

'' na farko dai shugabanni azzalumai yake nufi kokuma masu hukunci da zalinci. 

nabiyu kuma yace; wasu matane zaku gansu da kaya ajikinsu amma tsaraicinsu na waje suna tafiya suna karairaya jiki, sa'annan kawunansu kamar tozon rakumi, yace kuma bazasu shiga aljannaba, kuma bazasu ta'ba jin kanshin aljannah ba. Domin awani qaulin anajin kamshin aljanna a tsahon tafiyar shekaru dari biyu ko dari biyar.''

Allah kakare 'ya'yanmu da 'ya'yan 'yan uwanmu daga Gurbacewar tarbiya.


 

******** 'YAN MATAN ASALI *******

  Allah sarki wadannan sune abin tausayi, kuma sune masu wahala, kuma sune masu rabauta duniya da lahira.

    Tayadda suke fitowa daga gida na mutunci, iyayensu nagartattune su kuma kamammune. Sukan rike budurcinsu iya jimawar da zasuyi gabanin suyi aure. dashi suke samun martaba da nagartar zamantakewarsu ta aure.

 Kuma kafin suyi aure basu koda cakuduwane cikin maza ballema suyi wani mummunr mu'amala da namiji, hartakai ga sun zubadda mutuncinsu da budurcinsu.

Suna matukar Kula ha hakkokin dake kansu na addini dana zamantakewar rayuwa. sune Allah ya ambacesu acikin Alqur'ani yadda yake cewa a Suratul_ahzab.

 surah ta-33 Aya ta:35

''Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu tawãli'u maza da mãsu tawãlĩu mãtã da mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata gãfara da wani sakamako mai girma.''


   Hakika mata masu addini sune mafi dacewa ga dukkanin wani ďa namiji musulmi. Kuma sune zakasamesu masu kyakkyawan hallayya dakuma tsaftatacciyar budurcin wanda babu kazanta acikinsa.

 Duk da cewar kwaciyar aure na rana daya tak, yana wanke dattin kazantar bariki, duk jimawar da akayi dashi. Amma kuma duk da hakan kazanta bariki, yakan sanya zargi atsakanin ma'aurata, Zargi na har abada. Musamman ma yazamanto shima mijin mutumin banzane. 

   Allah karabamu da danasanin duniya da hasarar lahira. Ameen 

Dukkannin wanda yakaranta wannan rubutun nawa ya sanya aransa shima zai bada gudun mawa wajen gyara yau da goben Al'umar mususulmi kusani acikin addu'arku dani da mahaifana. Albarkacin wannan wata mai albarka ta Raladhana.


Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage