Posts

Showing posts from August 9, 2021

AL'UMAR MUSULMI AYI HATTARA

AL'AMARIN SA'IDU MAIKWANO MAI DA'AWAR 'YAN BAZATA ABIN TSORO NE      Daga Datti Assalafy  Allah Ya jarrabi Musulunci a Nigeria da wani irin Malami mai suna Sa'idu Aliyu Maikwano wanda yake da'awar wai Salafiyyah a Gusau jihar Zamfara, yana kafirta Manyan Malamai tare da bidi'antar dasu, yana kuma jifansu da kalmar khawarijanci, wato halasta zubar da jininsu Na saurari tsokacin da Maikwano yayi akan Khadimul Qur'an Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu (Rahimahullah) da kuma su Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar Izala na duniya Sa'idu Maikwano ya kafurta Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu, har ma ya soki Sheikh Abdullahi Bala Lau don ya yiwa marigayi Sheikh Isyaka Rabi'u addu'ah na samun rahamar Ubangiji Sa'idu Maikwano yace Sheikh Isyaka Rabiu kafuri ne, kuma mushriki, wai Sheikh Isyaka Rabiu yayi hidima wa kafurci da shirka ne kafin ya mutu, wai bai kamata Izala ta masa addu'ah ba Na girgiza matuka da jin wannan munanan kalamai da suka ...