HA'DIN KANMU HANYAR TSIRARMU
HA'DIN KANMU HANYAR TSIRARMU
Fitowa ta Hudu (¡v)
Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy
Yau zanyi maganane danganeda tasirin Aqidu acikin Zuqatan Mabiya, Lokaci Yanausa Abubuwan Sun Gur'bata Amma kowa gani Yake Shine Akan Tafarkin Gaskiya Dukda Cewar Wasu Abubuwan Mun Tabbatar dacewa Kuskurene Tsantsa, Amma Ginuwa Akan Aqidar damukayi, Shi yahanamu Hawa Kan Shari'ar Asali, Duk dacewa Itace tafi Zama Matsera garemu A Lahira. Misali;
Zuwan Izala tafito Da gyararraki A Addinin Musulunci Sosai, Amma Ganin cewa idan Munbita Menene makomar Iyayenmu Shiyasaka Dayawan mu Suka Kauracemata, Saidai kuma Ana Samun Masu Son Zuciyar dasuke Jifanta da Munanan Qazafi, da Isgili, (da Sunan Cewa Anzo da Sabon Addini) Wadda Azahirin Gaskiya Bahakan bane, Alkawarin ALLAH ne Yazo Nacewar Duk Sadda Lokaci Yayi Nisa ALLAH Zai Tada Wani Wanda Zai Jaddada Koyarwar Addini Yakuma 'Dabbaqa Shari'ar Masoyin Sa Annabi Muhammad (s. a. w).
Tabbas Dukkan Wanda yazo da Sabon Al'amari, Haqiqa Yana Fuskantar Qalubale, Musamman Yadda Izala ta Kawo Ababen da suka ci Karo Da Aqidun da Ta Tarar, koma Suka Sha ban_ban Da Abinda Ta Tarar akeyi, Na watsi da Karantarwar Addini, dakuma Kama Wasu Labaran Mafarki da Wadansu Ababen da Dakajisu Inkai Mai Tunani Ne, Zakasan Cewa Wadannan Wasu Tatsuniyoyine Masu Dadin Sauraro Ammafa Ba Ashari'ah bace Kuma bata Ma Dace da Shari'arba, Balle Suyi kamanceceniya da Gaskiya.
Hakazalika Izala ta Tararda 'Bur'bushi da Iddi'a'i na Wasu Masu Shirin Rusa Hadisan Annabi, Da Kafirta Sahabbansa Wadda Azahirin Gaskiya Hadisai Sune Shari'o'inmu Na Adalci Tareda Alqur'ani Wacce Muke Fassara Wasu Sassan Alqur'anin daga Hadisan Batareda Mun Bibiyi Littafan Yahudawa ba ko Nasara (Christian) Akan hakan Sahabbai Suka Dogara kuma Akan Tafarkinnema Suka 'Daura Mabiyansu Watau Tabi'ai, Kuma Dukkan Mai Neman Shari'ar Adalci da Hukunci Tsaftatacciya Idan Yabar Alqur'ani da Hadisai, To Yawuce Shiriya Ya Afka Halaka ALLAH Katsaremu.
Zanci Gaba Inshaa ALLAHU
Comments