SANIN COMPUTER DA SANA'O'IN CIKINTA

 Book 1 Daga Ismail Hussaini Alpholtawy Email 📧 hussainiismail257@gmail.com Nomban Waya📲 09047858802 Alpholtawy.Blogspot.com Ismaihussaini.code.blog Alpholtawy.Jw.Lt SANIN COMPUTER DA SANA'O'IN CIKINTA Gabatarwa Dukkan dangin Yabo da Godiya Sutabbata Ga Ubangiji Madaukakin Sarki ﷻMai kowa Mai Komai, Tsira da Aminci Su Tabbata ga Fiyayyen Halitta ﷺ Zababben Zababbu Mai Mukamin Ceto Abin Godewa Sha Yabo Annabi Muhammad (S.a.w). Da iyalan Gidansa Da Matayensa da Sahabbansa, da Masu binsa Cikin kyautata Ayyuka Har izuwa Ranar Sakamako. Ina Gode wa Ubangiji Daya bani Dama zan Wallafa Wannan Dan karamin Littafi, domin Amfanin al'uma Yakuma Zamo guziri Gamai Karatu Wannan Shine Littafi na Daya Zuwa Wani lokacin, Zan cigaba da Rubuta wani Makamancin Wannan Wanda Zai iya zama Cigabansa. ina Rokon Allah Yataimakeni. Ya Kasuwar Application Manhaja take Ita wannan kasuwar ta apps tana daya daga cikin hanyoyin samun kudi na zamani na digital marketing wanda ake samun kudi ta abubuwan da ba ganinsu a ke a fili ba. Haakan ne ya samu bayan yawan da wayoyin zamani sukayi yawa kamar amdroid da Iphone wanda biliyoyin mutane suke amfdani da su a kullum kuma suna bata yawancin lokuttan su musaamman matasa masu tasowa. A dalilin haka ne manyan kamfunnan wadanda suke da operating system suke cabaya sosai saboda babu wani wanda zai dora application dinsa a store dinsu face ya biya su kudin register. Baya ga haka kuma suna da wasu hanyoyin wanda zamu yi magana akan su suma a nan gaba amma yanzu ga bayani akan manyan kamfunnan da kuma aikace aikacen da suke yi a fadin duniya. Bari da farko mu fara dubawa akan wadannan kasuywannin da kuma abubuwan da ake daurawa kafin mu je ga yadda ake samu da su. Google Play Store Google playt store yana daya daga cikin sanannun kasuwar apps ko kuma ince daular application wanda suyka shafi operating system na android kamar wayar hannu ta android, agogon android, Tv da dsauran muhimman abubuwan da google suka hada. Google play ya samar da sana’oi sosai ga daukacin mutanen duniya musamman ma a kasashen da suka cigaba inda suke ba kimiyya da fasaha mahimmanci sosai. Hakan ya samu ne a dalilin yawaitar da android ta yi wanda ta kere abokiyar hamayyar ta wato iphone ta fuskar masu amfanin da manhajar android din. Kididdiga tana nuna cewar kusan kasi 80 cikin dari 100 na wayoyin da mutanen duniya suke amfani da su android ce sauran wadda ta biyo baya iphone da sauran opertaing systems na waya wanda suke biye a bayanta. Hakan ya samu ne ta dalilin kwazon da kamfanin Alphabet ko ince maka Google suka yi wanda tun bayan sayen android da sukayi a 2008 suka bada lasisin ta ga kamfunna kyauta. Kuma suka cigaba da aiki ba dare ba rana domin suga sun tabbatar da cewar sun inganta ta dama da sauran takwarorinta a fadin duniya. Karanta: Android Apps: Applications Biyar masu amfani na Kamfanin Google wanda suke da matukar amfani a rayuwar yau da kullun Abubuwan da ake daurawa a play store Manhajar Applications Litattafai Finafinai Games Wakokin da sauran kayan sauti App Store App store kasuwar application ce itama maallakar kamfanin Iphone wadda take dauke da biliyoyin applications a cikinta domin yin installing ga masu amfanin da abubuwan iphone kamar waya tab da kuma computer. Developers da dama a fadin duniya suna dora applications dins a kasuwar kuma suna samun kudi sosai musamman masu dorawa domin a saya. Saboda yawancin masu amfani da iphone a fadin duniya kamar yadda bincike yake nunawa sunfi saurin su kashe kudi fiye da wadanda ke amfanin da android. Dalilin hakan kuma shine saboda yadda ita kanta wayar iphone din take tsada kuma abubuwan su ana yawan kashe kudi sosai hakan yasa subscription da kuma sayya a store din yafi na androd sosai. Ga wasu daga cikin abubuwan da ake dorawa a cikin store din kamara haka. Abubuwan da ake daurawa a App store Applications Games Manhajojin Agogon iphone Fina finai da sauransu. Yadda zaka fara Idan kana da sha’awar ka zama developer wato mai kirkira apps kana dorawa a cikin wadannan kasuwannin akwai muhimman abubuwan da ya kamata ka sani wanda zasu taimaka maka wajen ka cimma burinka kamar haka wanda zaniyi maka bayaninsu kamar haka. Tunanin Kasuwar da Zaka fara A cikin duka wadannan wuraren da na ambata kafin ka fara yana da kyau ka tsaya ka natsu kayi tun ani sosai akan mi wace kasuwan kake son shiga. Shin kana son kayi target din masu android ne? koko masu iphone? kuma kayi tunani mai zurfi akan mi zakayi masu wanda zaka taka rawa sosai saboda akwai apps ko abubuwa da yawa yana da kyau kaga ina rauni yake inda zaka shiga ka taka rawarka wajen inganta abun. Ta hakan ne zaka gane inda zaka dosa tare da tsara yanayin kasuwancin yadda zaka yi shi sabaoda komai a duniya yana da bukatar a yishi a bisa tsari yafi tafiya daidai yadda ya kamata. Karanta: Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari Koyon Ilimin kirkira Abu na gaba kuma mai mahimmaci shine ina zaka samu ilimin abunda zaka kirkira ko kuma idan ka iya taya zaka cigaba da kwarewa yadxda ya kamata domin kayi ficce. Mafi yawancin wadannan kasuwannin ana dora apps ne a cikinsu ko dai Andoid Application kom kuma Iphone Application to dole sai ka koyi yadda zaka yi su shin da programming ne koko ba da shiba. A baya nayi magana akan yadda ake hada android application kana iya duba shi da kuma shi kanshi koyon programming na com[puter baki daya. Karanta: Abubuwan aiki da ya kamata ka samu kafi ka fara hada android app da Programming Abubuwan aiki da ya kamata ka samu kafi ka fara hada android app da Programming Hada kasuwancinka Abu na gaba kuma bayan ka samu ilimin hadawa ka hada ko ka kirkira abunka to sai kuma kayi kokarin maida yanayin kasuwancin zuwa kamfani yadda abun zai cigaba da tafiya. Da haka ne turawa suka zarce mamu a cikin abubuwa da dama da kuma sauran kasashen da suka cigaba kullun suna kokarin kirkiro sabbin kamfunna saboda da haka ne za’a rage zaman banza wanda in kayi kokari zakaga mutane da dama suna aiki a kalkashinka. Bunkasa kasuwancin A karshe kuma shine sai kayi kokari kaga cewar idan ka fara samun kudi ta hanyar kasuwancin ka ka bude kamfanin ka koda karami ne to ya zaka bunkasa shi. Daman bambanci tsakanin manyan kamfunna da kuma kananu shine bunkasawa wanda daga cikin hanyohyin bunkasa kamfani sun haada da yawan talla, kara zuba jari mai yawa da kuma kara aikace aiukacen wanda zasu habbaka kasuwancin da kuma kara samaun hanyoyin samun kudin shiga. Mi ake nufi programming na Computer? Idan akayi magana akan shi ana nufin tsara yadda zaka ba na’ura mai kwakwalwa wato computer yadda zata rinka aiwatar da wasu aika-akace wanda kammalallen tsarin shi ake kira da software. Software ita tana aiki ne a cikin computer ba ka iya taba ta amma zaka iya ganin abubuwanta a cikin screem na na’urar ka imma computer, waya ko kuma duk wani na’in naura mai kwakwalwar sarrafa kanta. Wadanda suka iya yadda zasu ba computer umurnu ana kiransu programmers wato yan tsari, sukuma wadanda ke kirkire kirkire na manhajojin da suke da amfani ga alumma ta hanyar warware masu matsallolin yau da kullun ana kkiransu developers ko kuma software engineers. Ina ake koyon programming na Computer? Tabbas mai karatu zai yi mamaki yayi kuma wannan tambayar inane ake koyon programming, kuma yadda abun yake musamman ma ga wadanda ba daliban computer ba wadanda suke karanta computer a matsayin course a babbar makanta ko kuma jami’a. Akwai hanyoyi da dama na koyon programming amma ga wasu daga cikin muhimman da suke taimaka ma mutum wajen cimma gurin shi. Ta Hanyar Koyo da Kanka Kasani cewa musamman a zamanin yanzu idan kana son koyon computer ko kuma ka koyi wani abu wanda ya danganta da Internet(yanar gizo), akwai hanyoyi da dama wanda zaka ji wasu mutane suce su suka koya ma kansu. A duniyar yanzu musamman dalilin cigaban da aka samu na yanar gizo koyon abubuwa ya zama sauki a wajen mutane daban daban a fadin duniya wanda ta hanyar wayarka zaka iya neman bayani koda hausa na idan ka tambayi Google ko kuma abubuwan nema na internet masu kama da shi. To kame da koyo da kanka musamman programming kana iya ziyartar shafukan yanar gizo masu bayani akan haka, kalon bidiyoyi a youtube da kuma tambaya a shafukan tambayoyi na tattauna abubuwa musamman wadanda suka shafi programming din. A hanyar ka ta koyo zakaga cewa kana makalewa ko kuma wata matsala tazo kawai kaje manyan forum kamar su Quora.com da suransu da ka tambaya ba dadewa inshallahu zaka samu amsa. Bisa ga haka kuma suma kafafen sada zumunta na zamani kamar su facebook, twitter, Instagram da sauransu suna taimakwa sosai zaka karu kuma iidan ka yi tambay zaka samy amsa domin akwai wahala wani abu ya shige maka a duniya kayi tambaya a ki amsa maka. karanta : Koyon Internet da Abubuwan da Suka Shafe ta Ta Hanyar Training Wannan hanya ta biyu ita ce ta hanyar training a kaginku ko kuma unguwar ku amma ka sani cewar koda ka samu training a unguwarku ku sai ka hada hada a hanya ta farko wadda itace hanyar kara koyama kanka ta bincike. Yawanci wai kaje makaranta a koya maka baka cika kwarewa sosai ba idanb baka yin abunda ka iya a makarantar aikace, gashi kuma shi prigramming yana da bukatar ta kasance kana yawan yinshi a aikace ta hanyar kirkira mafita a dama a kan wasu matsaloli. Amma hanyar training ian kana yin abun a aikace yana taimakawa sosai saboda ga malami a kusa da kai ita inda take da karin amfani kenan kuma ga abokai wanda kullun suke kara harzuka ka a kan abun. Ta Hanyar Karantar Computer Hanya ta gaba kuma itace ta hanyar karanta computer a makaranta a jami’a ko kiuma sauran manyar makaranta a matsayin abun yi. Shima hakan yana da kyau kuma yana taimakawa matuka amma yana kyau ka rika binceka kuma ka karanta ta da niyyar ba wai kawai a yi a wuce wurin ba kawai ta hanyar sha wato craming akamr yadda yan boko ke cewa. To karantawa ta hnayar iyawa da fahimyar abunda aka karanta shine yafi saboda yadda zaka hada wani abu da ka iya wanda hakan zai taimaka maka wajen samun kudi kamar yadda na ambata a farko masu irin wannan ilimin siuna samu. Sassan Programming Abu na gaba da ya kamata ka sani shine shi kanshi masu programming suna da sassa ta fannin abubuwa ko kuma mahajojin da suke hada ma al’umma wanda ake biyansu ko kuma su samu kudi da su kai tsaye. Ga su a nan kasa zan lissafa su tare da bayaninsu sai kaga wane fanni ne kake da sha’awar shiga ciki ka taka rawa ko kuma ya kasancema hanyar sana’a ko kuma samun kudi. Fannin Shafin Yanar Gizo Fanni na farko shine na kirkira shafukan yanar gizo ta hnayr tsara shi, yimashi kyalliya da kuma abubuwan da ya shfi inganta tsaron shafukan yadda abun zai kasance mai amfani ga masu ziyarta. A wannan fanni idan kana son ka iya shi akwai yarukan da suke da m atukar amfani ka iya kafin ka iya kirkira shafin kamar su: HTML wannan yare ne wanda zaka hada abubuwan da ake gani na shafukan internet wanda ya hada da rubutu, abubuwan latsawa, akwatutuka da sauran abubuwan da wanda zai ziyarta zai iya gani a cikin computer din shi ko kuma waya. Css sHI kuma yare ne wanda za ka koyi yadda zaka yima shafukan da ka hada da html da mukayi magana a sama kwalliya yadda zasu burge mai kallo da kuma taimaka mashi wajen fahimtar shafin. JavaScript: Shikuma wannan yare ne da ya dogara da abun da ya shafi abubuwan motsi na shafin tyanar gizo duk yawancin motsin da zaka ga shafin yanar gizo na yi to da wannan tyaren ake yin shi. Php: Wanna fanni shikuma ya danganci server wadanda akwai yaruka da dama wanda ba dole sai wannan ba kamar su python, ruby dama sauransu amma shi dai wadannan fannin yarukan sune na server wanda zasu taimaka maka wajen amsar bayanai na wanda ya shiga. Ana hada shi da abunda ake cema database inda zai zama wata ma’adana ta abubuwan rubutu hotuna, da ma sauransu. Fannin Manhaja Fanni na biyu kuma shine fannin manhaja wanda shi kuma a nan zan raba shi zuww gida biyu kusan wanda sun hada da. Manhajar Waya Manhajar Computer Manhajar waya Wannan fanni shine ake kira da app developers wanda suke hada application na waya irin androi ko kuma wayar iphone. Ga wadanda suke son kirkira manhaja ta android suna da bukatar iya proggramming languge kamar irinsu java, kotlin, C++ da sauransu duk daya daga cikinsu da mutum ya iya yana iya amfani ya kirkira mahajar android. Sai kuma a fannin wayar iphone shi kuma akwai wani programming da ake kira da swift wanda da kafinshi ana amfani ne da wani yare wanda ake cema action script to iya daya daga cikin su kana iya fara hada apps na iphone. Manhajar Computer Abu na gaba kuma shine hada mahajoji wadanda suke aiki a computer wanda su irin wadannan mutanen ake kiransu da software develkopers ko kuma injineers. Su aikin su shine su kirkia manhaja wadda zata iya gudanar da wani aiki a computer kamar ta rubutu gyaran bidiyo da sauran abubuwa da computer ke yi. Akwai yaruka da dama da ake amfani da su wajen hada softwayoyi na computer wanda wasu daga cikinsu sun kunsi wadanda muka ambata a baya kmar na website ana hada su su zama na software ta kasa sune, HTML, CSS da Javascrip, ko kuma irinsu Java, C++ da sauransu. Ita mnhajar computer ana iya kirkira ta da yarukan computer da dama wanda idan kana son cikakken bayani kana iya kara cikakken bincike akan hakan. karanta: Yadda ake bude YouTube Channel Kammalawa Kamar dai yadda na ambata a baya computer programming yana da matukar mahimmanci kuma hanya ce wadda mutum idan ya dage yana iya dogara da kansa saboda yadda ake samun kudi da ta tana daya daga cikin fannonin computer da ake samu da su. Ma’anar Internet(Yanar Gizo) Internet wato yanar gizo na nufin jerin gwanin wasu computoci wanda suka hadu a fadin duniya ta yadda suke musayar bayanai a tsakaninsu. Babu waanda a fadin duniya zai iya bugun gaba ya cema wai shi keda yanar gizo shi yake da komai ba haka abun yake ba ta kowa ce manyan computocin nike magana a sama inda na bada abuda take nufi wato servers kenan a turance. Su wadannan servers din suna watsa bayanai na shafukan internet ne wato websites a duk fadin duniya yadda kowace computer zata iya samu kamar waya da sauransu kaga daga wata babbar computer wadda ta rike bayanai zuwa kanana to shine ake nufi da yanar gizo. Rabuwar Shafukan Internet Shafukan internet sun rabu da yawa amma ga wasu manyan fannoni guda ukku wanda na tantance domin saukin fahimta ga maia karatu. Search Engine Idan aka yi magana akan search Engine ana magana ne akan manema ta Internet wanda wasu na’uin shafuka ne na yanar gizo da zaka ziyarta domin neman bayanai akan wasu abubuwa. Misalansu sun hada da Google , YouTube , Bing da sauransu su dai kawai aikin da suke yi shine ka nemi wani bayani ko da turanci ko kuma da hausa akan wani abu ka samu suna bada amsa wasunsu a rubutu, bidiyo da kuma hotuna wasu kuma bidiyo zalla kamar yadda nabada misali da youtube a nan. Amfani da irin wadannan search din yana da sauki saboda cigaban kimiyya a yanzu yakai kana iya rubuta masu da kusan kowane yare su baka amsoshi da dama. Yadda zaka nemi abu a Search Engine kamr su Google. Farko ka shiga cikin browser wadda kake da ita chrome ko opera amma chrome ta fi ita ce ta kamfanin sai ka rubuta duk abunda kake nema da kowane yare zakaga shafin amsa. Sai ka rsaya ka kula wane kake so Rubutu ko bidiyo sai ka zaba Da ka shiga sai ka natsu kaga idan ka samu abunda kake nema in kuma baka samu ba sai ka fito ka kara nema. Shafukan Rubuce- Rubuce Sai kuma a fanni na biyu akwai wasu shafuka wanda sukuma zakaga rubuce rubuce zaka samu a cikinsu wadanda a turance ake cema su blogs. Su shafuka ne wanda search engine wadanda mukayi bayaninsu a sama suke bada amsar abunda suka rubuta da sauran shafuka masu alaka da su kamar da kafafaen sada zunta, Su kawai zaka samu rubutu ne akan wata kasida misali kamar yadda kake karantawa a yanzu to haka abun yake. Kna iya duba post da kasa munyi bayani akan yadda ake bude wenbsite na blog tare da makan da ake bi dala- dala. karanta : Yadda zaka bude karamar website na Blogger | Lesson 1 Kafafen sada Zumunta Kafafen sada zumunta wani launi ne na shafukan internet wanda suke taka muhimmiyar rawa a rayuwar alumma wanda ake watsa hotuna bidiyoyi dama sauransu. Kuma ana amfani da su wajen habbaka kasuwanci tallata kasuwanci dama sauransu saboda yawan mutanen da suke a ciki kuma da yanayin yadda ake saurin watsa bayanai da samun shi cikin hanya mai sauki batare da wani bata lokaci ba. karanta: Bayani game da tallar da facebook ke ma yan kasuwa da yadda zaka fara tallata hajarka Kasuwanci: Yadda ake fara kasuwanci da karamin jari kammalawa Kamar dai yadda nayi bayani ita internet kafa ce wadda take da amfani ga rayuwar alumma kuma ana karuwa da ita sosai musamman ga wadanda sukayi amfani da ita a hanyar da ya dace. Kuma yanzu zani ya canza duk abunda kaga ya shigema to ka tafi internet ka nema kada ka ce dole saida turanci a’a koda yarenka na hausa lafiya lau daka tambayi google ko irinsu youtube inshallahu zaka samu amsar abunda kake nema a cikin sauki. karanta : Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a Abubuwan da ke taimakawa wajen zaman Hardar Qur’ani Yadda ake koyon Computer da kuma Bayani akan Ilimin Computer Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su SOFTWARE DATA KAMATA KA/KI MALLAKA Akwai softwayoyi ko in ce manhaja da yawa wadda ake hada android app da ita amma sananiya wadda kamfanin google ya fi ba mahimmanci ita ce android studio. Karanta : Applications biyar masu matukar mahimmaci Yadda ake Hada Android App Yadda Zaka samu kudi a Internet Android Studio Android studio babbar manhaja ce ta android wadda ake hada android app da ita da yaruka na programming irinsu java, c++, kotlin da sauransu wadda tana nuna maka/ki abunda kake a cikinta. Tana da saukin aiki ga yan koyo a wani fannin kuma tana da yar rikitarwar ta amma ba wani abun wahala bane ba sosai, to ina ba wanda zai fara shawara da yayi amfani da ita kusan ma dole ce ga wadanda zasu amfani da yaren java. To ga link dinda zaka yi download din android studio a computer Bayan ka dauko ita wannan software ta android studio to akwai aikin da zakai mata shinea zaka sa data ka ida sauran matakan intalling dinta a cikin computer dinka. Yana da kyau ka sani cewa ita wannan software ta android studio kafin ka daidaita ta domin ka fara hada android application ka tabbata computer ka tana da karfi wanda shine ya kasance kana da ram kamar 2GB haka da kuma isasshen hard disk a cikinta. Karanta: Abubuwan da zaka Kula dasu kafin sayen computer Wane Ilimi Nike Bukata idan ina so in fara Hada Android App? Dangane da ilimin daya kamata na programming languages wadanda ake hada android application dasu suna da yawa amma daga cikinsu akwai java, kotlin, c++ da sauransu. Amma dai a nan tunda na baka shawara kayi amfani da android studio kana ka iya java ko kuma kotlin duk wanda ka zaba a cikin su to lafiya lau. Da farko dai zaka koyi java ko a cikin sati ukku ko biyu sun isa ya danganta ga kokarinka, sai ka tafi akan yadda ake amfani da framwork na android wato yadda ake android programming kenan. a nan zaka cigaba da hada android apps to. Ta wace Hanya zan koyi java da Android Programming Akwai hanyoyi da dama da zaka iya koyon java kana iya koyon su a youtube ta hanyar kallon youtube videos, inshallah zaka iya indai ka sa kwazo a ciki. Da farko kaje ka koyi yadda zaka saita java a cikin computer dinka sannan ka koyi yadda zaka yi installing din android studio a cikin computer dinka. Sannan kuma ka ringa yin browsing a cikin computer dinka na website a cikin computer dinka inda ake koyar da hada application da kuma downloading din littafi mai koyar da hakan Kammalawa A karshe dai abunda zance shine duk abinda kake son yi ya kasance kana son shi yadda zaka jure kuma ka sani duk abinda wani yayi tofa kaima kiana iya yinsa duk wahalarsa ko rintsi kawaio dagewa ce ake so dakuma kokarin bincike da habbaka kai musamman abubuwa irin wadannan Wadanne Hanyoyi ne ake bi a hada Android Apps Bari mu dauki Android mallakin kamfani Google saboda tafi yawa a duniya kuma anfi amfani da ita musamman a nahiyar mu ta Africa fiye da ace Iphone ko windows phone. Idan kana son ka fara hada Application dinka na Android ko kuma ka hada Application na kasuwancin ka to yana da kyau kasani #hanyoyin sun rabu gida biyu, zamu lissafa su tare da yin bayani gameda su. Hada Apps Batare da Programming ba Wannan sananniyar hanyace wadda ake amfani da ita wajen hada Android application a cikin sauki. yadda abun yake shine ana amfani da wasu websites na online wanda suka tsara software ta online domin ta hada ma mutane application din ta hanyar hotuna, rubuto ko kuma videos dinda suka daura. wannan hanya mafi akasari na biyane amma suna bada damar gwaji ko ka hada na free kafin ka je zuwa matakin biya wasu daga cikin websites da suke irin wannan aiki sun hada da Andromo , Thunkable da kuma Appypie . Wadannan suna daga cikin sanannu Ta Hanyar Programming Kashi na Biyu shine hadawa ta hanyar programming languages wanda kusan shin yafi, a wannan sashe zaka samu ilimin programming language wato yaren da ake amfani da domin ba computer umurni. Amma sananniyar hanya da mutanen duniya suke bi shine su iya yaren kotlin ko java sai su tafi wajen android API din wanda zasu yi amfani da software wadda ake cema android studio su cigaba da kirkira application a ciki. Kuma ka sani yana Bukatar kana da Computer mai karfi da sauri ba saboda babbar softwarea ce karanci 4GB RAM. Karanta: Muhimman Abubuwan da zaka Lura dasu kafin sayen Computer Akwai yaruka da dama da ake amfani dasu wajen hada android application gasu kuma kamar haka. Yarukkan da ake amfani dasu wajen kirkira Application na Android Java JavaScript C++ C# python da sauransu Shawara Gareni Idan zaka hada android apps ta hanyar programming language to ka tafi ga abubuda mutane suka fi iyawa shine yaren java ko kuma na Kotlin. Su yi Download din Software wadda ake cema Android Studio su cigaba da hadawa. Muna nan muna kokari hada Littafin PDF wadda zamuyi maka bayani dalla- dalla da hotuna akan Yadda ake hada Application tareda Bayanin hanyar da zaka samu kudi da abun Ku cigabada da kasancewa da Abubuwan Lura kafin sauke software Yana da kyau kafin ka safke wata softaware a cikin computer dinka ka lura da wadannan muhimman abubuwan da zan lissafa su a kasa: Wane kalar Operating System gareka Ina zaka samu software din ko kuma ka samo ta Nauyinta kamar nawa ne Shin ta kyauta ce ko kuma ta kudi Bayani game da su daya bayan- daya Kamar yadda muka ambata su abaya to ga takaitaccen bayani gameda su. Wane Irin Operating Sysyem gareka Kafin ka safke wata software ya wajaba dolene kasan wane opearating system kake amfani dashi wanda zaka safke ita manhajar software din a ciki. Domin idan ka dauko ta wani kasama wani baza ta yi ba, misali ka dauko software ta Windows ka sama Linux baza tayi ba kwata-kwata dole sai ta windows din kuma ta irin processor din misali akwai x64 da x32 bit domin ka gane samfarin operating system da abubuwan da suka shafi computer dinka a windows kawai zabi computer ko this pc sai ka danna options sai ka zabi properties zaka gani. Ina zaka samu software din ko kuma ka samo ta Yana da kyau kasan cewa kafin a safke software ana taka tsantsan da don tsoran cutarwar virus na wai ko daga ina ta taho na kawai ka samo ka daura ma na;urarka, kuma yana da kyau ace kayi installing na wata manhaja wadda take yakar Virus wato Anti-Virus Software. Sa wannan yana taimakwa wajen ko ka samo mai illa ta nuna ma ka cireta, to a fannin inda zaka samu ita sopftaware din kuma ya danganta yawanci kwara kaje shafin ita manhajar software din kayi Downloading. In kuma ba haka ba to kana iya samun wanda ka yadda dashi ya tura maka wanda kuma shima lafiya lau computer dinshi take. Nauyinta kamar Nawa ne Yanna da kyau sosai kasan nauyin software kafin ka safke ta kuma kaima kana da wuri a cikin computer dinka. Bama a nan abun ya tsaya ba kai har ma RAM dinka ya kamata ka san ita nawa ne kamar take bukata ga manyan softwares kai kuma nawa gareka. Domin in manya ne wasu ko kayi Downloading sai suyi ta tsayawa ko ma su jamaka matsala wadda zata iya lalata maka computer dinka gaba daya. Shin ta kyauta ce ko kuma ta Kudi Wannan ma wani abun dubawa ne Daomin idan wasu softwayoyin wadanda suka yi su kyauta suke watsa su ba tare da an biya ko sisi ba. To wasu fa na kudi ne kuma gaskiya yawsancin softwayoyi na kudi ne ba na kyauta bane wato shine ake cema licebse in ka ji kana iya saye kana iya saye ta shafin yanar gizon manhajar shikenan. Yadda zaka yi Download da Install A nan zamu koya wanda zakayi download a cikin sauki wanda website din in kaje suna gane da wane operating system kake amfani, misali kamar a nan mun dauki chrome Browser ga kuma matakan da zaka bi. Shiga Browser Software a cikin comfuter ka sai ka danna Download sunan software din misali ni anan nasa Download Chrome Browser. Bayan ka rubuta ka danna enter to zakaga ya kaika shafin zaba a Doogle din to a nan mafi yawanci website ta sama ita ce ta sofware din inda ake samun ta. To sai ka danna ka sihiga. Daga nan kuma daka danna zakaga ta fara sai sai kabari ka ida. Da zaran ta Ida sai ka shigaDownloads folder a cikin computer dinka sai ka danna ok in kuma oermissin tace sai ka sa allow, daka yi haka sai kayi accept license sai kuma next har ka gama shike nan sai ka bude ta. Muhimman Abubuwan akan Rubutun Littafi Littafi yana daya daga daga cikin muhimman abu ko kuma ince jigo wanda musamman dalibai suke tunkaho da shi kuma kuma yake da matukar amfani a garesu. Kai bama kawai ga dalibai ba littafi shine jigon da ya ba,mbambanta tsakanin jahili da kuma mai ilimi ta kowace fuska a rayuwar dan Adan. Masu yawan katranta littafi sun fi kima a idon mutane saboda ilimin da suke kwasa su kuma masu rubuta lkittafi sun zarce su saboda su suka yi bincike suka rubuta litattafan da ake karantawa. Ka rubuta litafi koda daya ne a rayuwar ka yafi babu saboda abu ne mai matukar amfani koda ba don ka samu kudi ba balle idan kayi abunda ya dace ma har kudin sai ka samu. Yadda zaka fara Rubutawa Mfi yawancin mutane suna ganin gamar rubuta littafi abu ne wanda ba zasu iya shi ba su rubuta shafi da yawa tsammanin su shine marubutan littafi a lokaci daya suke rubuta shi wanda ba haka abun yake ba kwata-kwata. kaima zaka iya rubuta naka ay da kadan ake farawa zuwa da yawa ga kuma wasu muhimman matakan da za ka bi wanda zasu taimaka maka wajen rubuta littafinka. karanta: Manhajoji masu amfani ga masu rubutun littafi kamar Hausa Novel Tsarin Rubutawa Da farko zaka tsara yadda zaka rinka rubuta littafinka misali kullun zakayi shafi daya ko fiye dxa hakan burinka dai shine kana so a ce nan da wata 3 misali kasa da haka ko kuma sama da hakan ka gama. Ya danganta ga yadda zaka iya rubutawa koda shafi daya ne duk kullun ba matsala kuma kar ka samu damuwa kaga wani wajen bai yimaka ba kana iya gogewa ka kara ko kuma ka rage abunda kake so. Yana da kyau ka sani cewar ko suma manyan marubutan littafi suna yin hakan su kyara inda keda kyara ko kuma su rage ko kuma kari ya danganta ga yadda halin ya kasance. Bincike akan Fannin Rubutunka Abu mai mahimmanci wanda yake daga cikinmatakan da marubuta suke bi shine yawan bincike da kuma karanta litattafai masu alaka da da wanda suke rubutawa. Hakan na da matukar amafani kuma yanaa taimakawa sposai saboda ta hanyar hakan hakan ne zaka ga basira da hikimar da wancen marubucin yayi amfani da ita ka sa a cikin naka. Kuma baya ga hakan zaka kara samun ilimi sabaoda yana da kyau ka sani cewar kafin kayi rubutu akan wani abu cikin littafi ka tabbatar ka sana abun abun saboda wadanda zasu karanta bayan ka kammala littafinka suna iya fahimtar idan kana da kwarewa akan abunda ka rubuta a littafinka ko kuma babu. Binceke akan Rubutun Littafi Idan kana son ka zama kwararre a fannin rubutun litattatafai to yana da kyau ka rika ywaita bincike akan marubuta da yadda suke rubutunsu. Tare da gano hanyoyin zamani da kuma kayan aiki na zamani da zasu taimaka maka wajen rubunka saboda kamar yadda yadda na fadi a fannin sana’aoi shi bincike yana da amfani a koda yaushe. Domin ta hanyar bincike ne zaka fahimnci cerwar ga wani sabon abun ya zo ya zaka tafi da shi dai dai da zamanbi yadda zaka samu karbuwa a wurin jama’a sosai yadda ya dace. Lissafin su Ga su a nan kasa zan lissafa maka su tare da bayani akan kowace kamar yadda na fahimcesu da ayyukan da ake samu da ita. Blender Sweethome 3d Inkscape Wps Olive Blender Blender wata software ce wadda ake amfani da ita wajen hada zanuka na modelind wato ana hada zanuka abubuwa yadda zaka gansu kamar da gaske. Da wannan software din ce kamfanoni da dama suke amfani musamman na kere-keren manyan engina da kanana da kuma sauran kayan aiki, wanda ake spon ganin taswirarsu a 3d. yadda zan yi maka bayani kja fahimta shine a zani muna da na’ui kala biyu 2d da 3d. 2d zane ne wanda zaka ganshi normal wanda baida na;i biyu ko ukku kawai zaka ganshi hakanan. Shi kuma na 3d zakaga kamar yana da na’i duda ukku wanda zakaga zanen ya fita kamar dagaske. To ita wannan software tana yin dukan su 2d da kuma 3d din amma anfi saninta da 3d din tafi shahara a nan. SweetHome 3d wannan software din ta kyauta ce itama wadda ake amfani da ita wajen zanen gida da fidda yanayin awon shi. Yawancin masu zane wasu suna amfani da irin wannan software din saboda tana da kayan aiki sosai indai na fannin zana gidaje ne. A zanen da kayi kana iya fidda shi a bidiyo, a hoto ko kuma ka fidda shi a yanayin littafin pdf domin nuna ma wanda kayimawa. kuma kana iya printing din aikin da kayi a cikin hanay mai sauki kamar yadda na fadi itama wannan software din kyauta ce ba sai ka biya ko sisi ba. InkScape Idan ana magana akan software ta kyauta wadda ake zane da ita sosai to da kazo wajen inkscape zaka samu abunda kake so da yardar Allah. Wannan software din ta kyauta ce wato open source kana iya download din ta kayi install a cikin computer dinka ba tare da ka biya ba. Daga cikin muhimman abubuwan da zaka iya yi da ita shine kana iya zane kala kala kuma ka fidda shi a format dinda kake so kamar su png da kuma format na svj, kusan ita a svg take aje format dinta. Kuma tana yin zanuka maya irin na isomerism wanda zaka ga sunyi model sosai kusan kamar yadda zanen 3d yake. Daga nan kuma sai manhajar software ta gaba kuma ita ce. Karanta : Fannonin computer wanda ake koyo da aka fi samun kudi da su WPS Office Wps software ce daga kamfanin kigsoft na kasar china wadda take da matsayin office suit software. Yadda zan yi maga bayani ka fahimci office suit software shine wasu irin manyan softwayoyi ne wanda suke ayyuka kala daban daban na office. Daga cikin abubuwan da suke sun hada da rubutu a fidda shi format kala daban daban kamar text da kuma pdf. Sai kuma akwai fannin spreed sheet wato excel inda ake hada data base wato rumbun ajiya na bayani wadda zaka iya amfani da ita kamar microsoft office. Karanta : Rubutun Littafi: Manhajoji masu amfani ga masu rubutun littafi kamar Hausa Novel Abu kuma na gaba shine akwai fannin presentation wanda zaka hada slide wanda zaka iya sawa a projecter domin bayani a gaban taron mutane ko kuma ga masu koyawa musamman lectures kana iya hada presentation da ita. wps softaware ce ta kyauta wadda kana iya printing da sauran abubuwa kuma tana da wajen ajiya na cloud storage wanda zaka iya adan files dinka a yanar gizo. Karanta : Yadda Ake Fara Kasuwancin Printing da Photo Copy Olive Kamar yadda mukayi bayana a baya akan youtube abubuwan da ya shafe shi da kuma kayan aikin mai youtube. To ita dai wannan software din ta kyaran bidiyo ce kana iya sa bidiyon da ka dauka ka gyara ta. Karanta: Kayan aiki da mai YouTube Channel ke Bukata Daga cikin muhimman ayyukan da take sun hada da yanke bidiyo, kyara ta da sama ta effects, sanya waka ko kuma sauti, sanya rubutu da ma sauransu. Ku cigaba da sancewa da mu domin samun post na sana’oi da abubuwan amfani kuma inshallah ba da daewa ba zamu fara koya abubuwa ta hanyar bidiyoyi Mi ake nufi da manhajar kasuwanci? Idan akayi magana akan wannan batun ana nufin yin amfani da aikace aikacen naura mai kwakwalewa na cikinta domin habbaka kasuwanci. Kmar dai yadda ma’anar software take abu ne wannda ba’a gani a fili sai cikin computer amma zaka iya amgfani da shi ya gudanar maka da wani aiki. To a nan muna magana ne a fannin kasuwanci ina nufin wadda take amfanarwa a fannin kasuwa ba wani fanni na daban ba kuma. da farko dai ya kamata ka sani a kayan aikin da muke amfani da su na na’ura aikin manhaja ya rabu zuwa gida ukku kamara haka. Manhajar da ke aiki a wayar hannu ko kananun na;ura Manhajar da ke aiki a computer Manhajar Online Karanta : Yadda ake hada Android Application Rabuwar su a fannin kudi A kuma yanayin kudi ko ace farashi yadda zakayi aiki da su sun rabu gidaje kamar haka, wanda kafin kayi amfani da wata yana kyau ka fara fahimtar wannan bayanin. Ta kyauta free Software ta kyauta a turance ana kiranta da free software wadda manhaja ce wadda kamfanin da yayita suka kirkira ta a matsayin mutane suyi aiki da ita kyauta babu wata bukatar su b iya kudi zasi iya sauke ta. Irin wadannan manhajojin yana wani lokacin kamfanonin da suka hada su suna samun kudin shiga ne ta hanyar tallafawa ko kuma ta hanyar kara ma software wani abu ta bayan fage wadda zai kara mata aikace aikace. Ya danganta suna iya cewa su kadai zasu hada abun karin aikin ko kuma sunba hada sauran mutane damar yin hakan. Ta saye lokaci daya Ta biyu kuma ita ce wadda ta saye ce sai ka biya kudi za’a baka kayi amfani da ita a kasuwancinka ko kuma wani abunda kake son kayi da ita. Irin wannan manhaja ita kuma yadda kamfanonin da suka yi ta suke samun kudaden shiga shine ta hanyar sayar da ita. Ya danganta suna iya cewa baka iya download kayi install din software dinsu sai ka biya ko kuma su baka wasu yan kwanakin da zaka dan tosa ka jaraba su rike kayansu Ta Biya bayan lokaci lokaci Ita kuma ta gaba ita ce wadda ake biya bayan lokaci lokaci ko kuma zango bayan zango ya danganta wadda ake kira da subscription based a turance. Ita wannan kawai zaka cigaba da biya da zaran ka bari to zasu hana ka aiki da abunsu in ka dawo ka cigaba da aiki da ita wannan yawancin manhajojin online dsunfi amafani da tsari. Kuma mafi akasari zakaga irin wannan manhaja tana da inganci da kuma aiki yadda ya kamata sosai. To bayan haka abu na gaba sai mu tafi akan muhimman abububuwan da ya kamata ka kula da su idan kana son zaba ta kasuwancin da kake yi. Yadda zaka zabi wadda zatayi maka Ita hnayar samu ba abun wasa ba ce kafin ka zabi wadda taka yana da kyau ka kula domin kada gaba wata ,matsala ta kunno kai wadda babu mai son hakan. Ga kuma wasu daga cikin muhimman abubuwan da zaka kula da su kamar haka zan lissafa su. Wane irin aiki zakayi da ita Idan ka sameta ka duba kamfanin yana update dinta yana kyara ta lokaci bayan lokaci Shin suna bada support wani taimako koda ka shiga wata matsala gaba Ya customin ka zasu ji abun zai kyara masu ko kuma zai basu matsala Kai kana iya amfani da ita kana samun saukin aiki da ita koko Shin tana da lafiya ba tada illar virus in kuma ya kama ta akwai magani anti virus koko. Abubuwan da muka zayyana a sama sune abun lura don haka sai a kula a cigaba da kasancewa da mu ia WWW.HAUSAWA.COM.NG a koda yaushe. Karanta : Manhajar Software wadanda ya kamata ka koya domin dogaro da kai Yadda zaka samu subscribers Masu Yawa a YouTube Channel Blog da Abubuwan da ya Kunsa Fahimtar yadda shafukan yanar gizo suke aiki kafin ka koyi bude su Assalamu alaikum kamar yadda aka saba yau ma ni Ibrahim Buhari mu tare a cikin wannan posting din wanda inshallahu zai kara fayyace bayani akan yadda website ko blog yake wato a hausance shafukan yanaar gizo domin kafin ka bude su yana da kyau ace ka san hakan. Idan ba’a manta ba a baya mun koya yadda ake bude shafin website blog wato na kyauta a blogger ga yan koyo. Kuma inshallahu littafin Pdf na nan tafe acigaba na kan website dama sauransu a cigaba da kasancewa damu a www.hausawa.com.ng a koda yaushe don samun abubuwa masu amfani. Don kullun don amfanin al’umma muka saka wadannan musamman yadda aka bar hausawa a baya. To bari muga mi ake nufi da Shafin yanar gizo Website/Blog yana da kyau mai karatu ya natsu ka karanta duka in kana son ka gane. Mi ake Nufi da Shafin yanar gizo Website/Blog? Idan aka ce Shafin Yanar Gizo ana nufin inda ake shiga a samu bayanai kokuma a yi wani aiki a wajen wanda wannan ne yasa aka raba kalmar a turance gida biyu. Website Blog wadannan kalmomi suna da alaka kusan ma kamar duk daya ne amma kanatsu zaka gane banbancinsu. Minene Website? Website wasu shafuka ne wanda aka aje a wata babbar computer wanda ake cema server wadda aka hada ta da suna na domain irin .com, .com.ng da sauransu kuma tana iya yin wani aiki. misali ka dora wani abu ta bude maka shi kamar kasa mp4 video tayi maka convrting kuma misali mai sauki kamar Google neman abu kake to website ce da sauransu,. Minene Blog?a Blog to shima kamar website ce a server aka dora kuma an hada shi da domain kamar .com.ng misali hausawasite.com.ng wadda ita mafi yawanci inda ya bambamta da website kawai shine rubutu ake yi bayan lokaci lokaci labarai ko abubuwan amfani. Amma shima ana cemasa website shine babban sunan To tunda munyi matashiya akan wadannan abubuwa biyu bari mu tafi akan yadda su ke aiki da mai amfani da su. Yadda shafin yanar gizo Website ke Aiki Shafin yanar gizo an hada sune da programming language wanda ake cema HTML shine yaren da akayi amfani aka gina su. To filolin da aka hada da wannan yare duka folder itace website din duka ta kunsa. To inda ake aje wadannan filoli a wasu manyan computers ne wato na’ura mai kwakwalwa babba wadda ake cema server. Ita kuma server kullun a duniyar nan kunne take saboda kar a nemi bayani a rasa a kunna su wanda in akace internet yanar gizo duka ana nufin computocin duniya da suka hadu suna musayar bayanai. To kaji dai shi shafin an dora shi a computer to bari mu tafi akan yaya kake samun abun in ka rubuta a manemarka Browser kenanan kamar opera tunda a ciki zaka nemi shafin da kake son ziyara ko Abunda ke faruwa in ka rubuta addreshin website ? Da farko dakasa misali www.arewarmu.wapdale.com ka rubuta a manema browser to wayar dama ta hadu da ISP(internet service provider) kamar MTN suda suka hadaka da internet tunda post din ba kansu yake magana ba bari muyi gaba. To su zasu nemo maka server wadda take aje da files na www.hausawasite.com.ng wadda ka rubuta sai ita kuma ta taji ana neman shafin. Sai ta maido maka da wanda ka nema taba ISP daga nan ya shigo browser wadda ita zata fassara maka file din programming din dana ambata a baya. Kammalawa Godiya ta Musamman ga Allah Ubangiji Madaukakin Sarki Wanda cikikin ikonsa da Qaddarawarsa yanufemu da Kaiwa Qarshen Zangon Wannan Dan Qaramin Littafi Mai sunaSANIN COMPUTER DA SANA'O'IN CIKINTA Ina Godiya gareshi Daya sa Mu'amfana da Abinda Kuka karanta Yasa yazamo Mai amfani agaremu Duniya da Lahira Kuskurena Aciki Allah Yasa mufahimta Kuma Mugyarashi Muyi abinda Zai amfanemu. Bissalam Daga Ni naku Ismail Hussaini Alpholtawy .

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage