WASIYAR WANI MAI HIKIMA GA DANSA A ZAMANIN INTERNET:

Yana cewa a cikinta: Lallai Google da Facebook da Twitter da Whatsapp da dukkan tsare-tsare (Platforms) ɗin sadarwa: Rafine mai zurfi, halayen mutane sun bace acikinsa. Hankulan Matasa sun gushe a cikinsa! igiyarsa ta tafiyar da kunyar yan mata, Jama’a da daama sun halaka! Ka kiyayi yawo a cikinsa, Kazama tamkar ƙudan zuma a cikinsa, kada ka tsaya ashafi sai mai kyau, domin ka amfanar da kanka dashi sannan ka amfani wasu. . Yakai Dana: Kada ka zama kamar ƙuda, wanda ke tsayawa akan komaai, mai kyau da mara kyau, sai ya dauki cuta ba tareda ya sani ba. . Ya kai Dana: Lallai Internet kasuwa ce mai girma, babu wanda ke bada kayansa kyauta, kowa nason wani abu kafin ya bada kayansa. A cikinsu akwai wanda ke son bata halaye amadadin kayansa! Acikinsu akwai wanda ke fitar da fikira rikitacciya, cikinsu akwai mai neman shahara, acikinsu akwai na ƙwarai, don haka kada kayi wata mu’amala da Mutum har sai ka bincika sosai. . Yakai Dana: ina kashedinka da kunce ƙulle-ƙulle, domin wasunsu tarkone da dabara, kuma sharri ne mai girma, makircine da rusawa Imani. Ina kashedinga da yaaɗa labaran bandariya (Jokes) da munanan abubuwa, ka kiyayi copy and paste na haramtattun abubuwa, kuma kasani wadannan abubuwa ana maka kasuwanci dasu cikin kyawawa ko munanan ayyuka, ka zaɓi abin siyarwarka kafin fitardashi kasuwa, domin ba’a shawara da mai sayen kaya. Ya kai Dana: kafin kayi comment ko joining, kayi tunani meye Alaƙar abunda zakayi da addininka? Yakai dana: kada ka dogara da abotar wanda idanunka basu ganshi ba. Kada kai hukunci ga mutane ta hanyar abinda suke rubutawa, domin su masu makirci ne, fuskokinsu masu sassauyawa ne, hankulansu dunƙulallu ne, maganganunsu masu dadi ne, suna ƙarya da gaskiya. Nawane mutane masu addini (a zahiri) amma sune manyan wawaye! Nawane kyakykyawa amma shine mafi munin munana, nawane mai kyauta amma shine mafi rowan marowata, nawane jarumi amma shine mafi tsoron matsorata? Sai dai wanda Allah yawa rahmah, nawane Allah yawa Rahmah??? Ya kai Dana: ka guji sunayen aro, domin ma’abotansu basu yarda dasu aransu ba, kada ka aminta da wanda bai amintaba cikin ransa. Na haneka da aron suna, domin Allah yasan abindake fili da na boye. . Yakai Dana: kada ka soki wanda ya sokeka, domin kai kana nuna kankane shima yana nuna kansa, kai kana wakiltan halayenka ne ba halayensa ba, kowace ƙwarya da ruwanta take ado. Yakai ɗana, ka kyautata abinda kake rubutawa, domin kana rubutune mala’iku na rubutawa, Allah S.W.A na saman kowa yana hisabi kuma yana bibiya. . Yakai dana: lallai mafi tsoron abinda nake jiye maka tsoro a rafin Internet mai ban tsoro shine kallon haram, da abokantakar mutan banza da kaucewa hanya, ina Roƙon Allah kada ka samu kanka cikin wannan najasa. Kayi ƙoƙari ka amfane kanka da Al’ummarka, ka bada himma wajen yada addininka, Ya kai Dana: Mafi muhimmancin mashigar shaidan itace sakankancewa da sha’awa, kuma sune ginshiqan internet. Ka sani wannan abu ba’a halicceshi don sakankantar dakai ba sai dai don amfaninka, don haka kai amfani dashi kada shi yayi amfani dakai, kayi gini dashi kada kasashi ya rusaka, kasanyashi hujja gareka ba akanka ba. Muna roqon Allah ya Nuna mana Hanyar Gaskiya Ya kuma bamu ikon binta. Alpholtawy

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage