Posts

HA'DIN KANMU HARYAR TSIRARMU

HADIN KANMU HANYAR TSIRARMUN   Rayuwa ta ishemu Wa’azi Malamai kuji tsoron Allah wajen Karantarwa kada kusa Son Zuciya. Domin tsira da mutuncinku aduniya da tsira da imani aran Qiyama. Dalibai muji tsoron Allah, Mufahimci junananmu Yayin Sa’bani, Kada Muce komai Malam  wane yafada Gaskiya ce, Binciken Yafi Sauraron Mu yawa. Muyi riko da Tsarin Allah Mugirmama junan mu kada Murarraba, Rabuwa A Al’uma fitinace, Yawan jayayya yanasanya Masu Son zuciya yad’a ‘Barna kuma yakan sa Wasu gaba da juna Bisa Rashin Dalili. Mukula Da amanar junan mu gun jaddada Sa’bani, Muyawaita zantawa da juna domin warware Sa’bani mukula da Wadanda ke son tada fitina a Addini Sud’in wawayene kuma jahilai, danganeda Harkokin Addini Basusan komai ba Sai musu da Cinzarafin Malamai. Akowace aqeeda akan iya Samun masu mummunar manufa da Kuma Son zuciya. Babbar matsalar rayuwa Shine aiki da Jahilci, dakuma Son Zuciya. Mu Janye Gaba da juna danganeda bambamcin aqeedah. Meyin hakan Bai fahimci addini ba, Son dun...

MATASA!!! MUKOMA GA ALLAH

 `YAN UWANA MATASA!!! MU KOMA GA ALLAH Rayuwar Matashi abin tausayine, Kana fama da Quruciya Ga kuma bakin Al`uma akanka. Idan za`afadi Damuwar Al`uma dubu, Kaso ´Dari Tasa da Hamsin (950) Na Matasa ne. Qalubale Garemu Matasa, Ban cire kainaba domin nima cikin Quruciya nake. Tabbas Muna Fuskantar Qalubalen rayuwa daga ´Bangaren zamantakewa, Har da Ibada. Saidai Raunin zuciya kuwa ya danganta da Yadda mutum yataso, Wahala ko Qunci, Tarbiyya ko Akasin hakan (Garari), Riskar iyaye da Rai ko Tashin Maraici. Idan Kasamu yin Makaranta Fani'ima (Haka akeso) In MA bakasamu ba Kaidai kada Kabar Neman ilimin Addini Domin Shidin Yalwatacce NE. Ako Ina akwaishi Amma kayi Takatsan_tsan Maluman da Kake Saurara. KADA kabi Maison Zuciya. Dukkan Wadannan Matsololin Rayuwa ce, Kirata Agaremu Shine, Mugane inane hanyar tsira kuma mecece mafita ta rayuwar mu, Ina Muka fito, Ina Zamuje, Me zamu Riska, Ina Tafiyar zata Tiqe? MATASA BAYIN ALLAH NE Kada Mushagaltu da Rudin Rayuwar ...

HA'DIN KANMU HANYAR TSIRARMU

HA'DIN KANMU HANYAR TSIRARMU Fitowa ta Hudu (¡v) Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy Yau zanyi maganane danganeda tasirin Aqidu acikin Zuqatan Mabiya, Lokaci Yanausa Abubuwan Sun Gur'bata Amma kowa gani Yake Shine Akan Tafarkin Gaskiya Dukda Cewar Wasu Abubuwan Mun Tabbatar dacewa Kuskurene Tsantsa, Amma Ginuwa Akan Aqidar damukayi, Shi yahanamu Hawa Kan Shari'ar Asali, Duk dacewa Itace tafi Zama Matsera garemu A Lahira. Misali; Zuwan Izala tafito Da gyararraki A Addinin Musulunci Sosai, Amma Ganin cewa idan Munbita Menene makomar Iyayenmu Shiyasaka Dayawan mu Suka Kauracemata, Saidai kuma Ana Samun Masu Son Zuciyar dasuke Jifanta da Munanan Qazafi, da Isgili, (da Sunan Cewa Anzo da Sabon Addini) Wadda Azahirin Gaskiya Bahakan bane, Alkawarin ALLAH ne Yazo Nacewar Duk Sadda Lokaci Yayi Nisa ALLAH Zai Tada Wani Wanda Zai Jaddada Koyarwar Addini Yakuma 'Dabbaqa Shari'ar Masoyin Sa Annabi Muhammad (s. a. w). Tabbas Dukkan Wanda yazo da Sabon Al...

AL'UMAR MUSULMI AYI HATTARA

AL'AMARIN SA'IDU MAIKWANO MAI DA'AWAR 'YAN BAZATA ABIN TSORO NE      Daga Datti Assalafy  Allah Ya jarrabi Musulunci a Nigeria da wani irin Malami mai suna Sa'idu Aliyu Maikwano wanda yake da'awar wai Salafiyyah a Gusau jihar Zamfara, yana kafirta Manyan Malamai tare da bidi'antar dasu, yana kuma jifansu da kalmar khawarijanci, wato halasta zubar da jininsu Na saurari tsokacin da Maikwano yayi akan Khadimul Qur'an Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu (Rahimahullah) da kuma su Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar Izala na duniya Sa'idu Maikwano ya kafurta Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu, har ma ya soki Sheikh Abdullahi Bala Lau don ya yiwa marigayi Sheikh Isyaka Rabi'u addu'ah na samun rahamar Ubangiji Sa'idu Maikwano yace Sheikh Isyaka Rabiu kafuri ne, kuma mushriki, wai Sheikh Isyaka Rabiu yayi hidima wa kafurci da shirka ne kafin ya mutu, wai bai kamata Izala ta masa addu'ah ba Na girgiza matuka da jin wannan munanan kalamai da suka ...

NASIHA

  KA ZAMTO TAMKAR BAKO A DUNIYA. - "Duniya ba gidan dauwama bace ita gidan ci-rani ce, kada ka bari ruɗun cikinta ta yaudare ka yakai ka ga saɓawa Allah maɗaukakin sarki, domin lallai duk soyayyar da duniya take nuna maka a yanzu, to wallahi watarana sai ta sake ka" - "Kullum kada ka sake ka mayar da wannan duniyar tamkar wata madauwamar ka, babban mai hankali shine wanda yake yiwa duniya tamkar gidan ci-rani, wato gidan wani ɗan zama ne ƙan-ƙani ba mai dogon lokaci ba, da zarar ka gama rayuwarka sai ka tafi ka barta"  - "Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya bamu shawara da cewa "mu zamto a wannan duniyar tamkar baƙi ko kuma masu ƙetarar hanya" wato irin mutanen da basa sakankance wa a duk inda suka je burinsu kawai suyi abinda ya kawo su su koma inda suka fito, to mu kuma bautar Allah ce ta kawo mu duniyar, da zarar rayuwar mu ta ƙare zamu koma ga mahaliccin mu Allah"

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYAS

 Tarihin Shehu Ibrahim Inyas  Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy    Dafarko dai Mai Karatu Zanfara da sunan ALLAH ﷽ Mun manta da tarihi Saikawai Labaran Duniya dakuma Kallace_Kallacen Film, Har wasu daga cikin Daliban Wannan bawan Allah din Sheikh Ibrahim Inyas mabiyansa Na Tijjaniyya Da Faidha. Basusan Tarihin Nasaba Saidai kawai Sunsan Littattafansa Wadanada yarubuta Kamarsu Kashiful Ilbasi, Dama Dawawinu_Ssittah. dama Sauran Littattafansa na Abyat.                              ﷽ اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎ Dafarkodai Sheikh Ibrahim inyas dai Asalinsa dan kasar Sanganiyane Agarin Kaulaha. Bayan Rasuwar Mahaifinsune alokacin da Sheikh Amadu Tijjani yazo yimasu Ta'aziyya, Sai Yanemi da da abashi dakin Soro domin Larabawa basa juran Zafi.      Yayansa Muhammadu Khalifa wanda Shine Magajin Mahaifinsu a fannin Khalifanci na Wannan Zawiyyan, Sai yace dashi ga ...

TARIHIN SAHABBAI Kashi na daya 001

  TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR SADDIK ALLAH YA YARDA DA SHI, (manzon Allah S. A. W) "yace ya Abubakar kai ne farko wanda zai shiga Aljanna daga al'umma ta" Sayyidina Abubakar shi ne Abdullahi dan Abu kuhafatu " usman" usman dan Amir dan Amir dan ka"abu dan sa"adu da taimu dan murratu dan ka"abu dan lu"aayu, bakuraishe. Bataime. Nasabarshi ta hadu da manzon allah ta wajan murratu dan ka"abu kakansu na biyar. Sunan shi a lokacin jahiliya "Abdul ka" aba" daya musuluta sai manzon allah ( S. A. W) yakara shi "Abdullahi" An yi mishi alkunya da Abubakar saboda riganyenshi wajan dabi"antuwa da kyamara halaye. Kuma an yimasa lakabi da saddik sabo da saurin bayar da gaskiyar shi ga dukkan abunda manzon allah (S. A. W) ya fada kuma manzon allah (S. A. W) yakara shi da "Atiku" shine mutumin da yafara musuluta a manyan. Shi ne mutum na farko, da ya fara kira zuwa ga addinin musulunci. Bayan manzon Allah Annabi Mu...