Posts

AL'UMAR MUSULMI AYI HATTARA

AL'AMARIN SA'IDU MAIKWANO MAI DA'AWAR 'YAN BAZATA ABIN TSORO NE      Daga Datti Assalafy  Allah Ya jarrabi Musulunci a Nigeria da wani irin Malami mai suna Sa'idu Aliyu Maikwano wanda yake da'awar wai Salafiyyah a Gusau jihar Zamfara, yana kafirta Manyan Malamai tare da bidi'antar dasu, yana kuma jifansu da kalmar khawarijanci, wato halasta zubar da jininsu Na saurari tsokacin da Maikwano yayi akan Khadimul Qur'an Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu (Rahimahullah) da kuma su Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar Izala na duniya Sa'idu Maikwano ya kafurta Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu, har ma ya soki Sheikh Abdullahi Bala Lau don ya yiwa marigayi Sheikh Isyaka Rabi'u addu'ah na samun rahamar Ubangiji Sa'idu Maikwano yace Sheikh Isyaka Rabiu kafuri ne, kuma mushriki, wai Sheikh Isyaka Rabiu yayi hidima wa kafurci da shirka ne kafin ya mutu, wai bai kamata Izala ta masa addu'ah ba Na girgiza matuka da jin wannan munanan kalamai da suka ...

NASIHA

  KA ZAMTO TAMKAR BAKO A DUNIYA. - "Duniya ba gidan dauwama bace ita gidan ci-rani ce, kada ka bari ruɗun cikinta ta yaudare ka yakai ka ga saɓawa Allah maɗaukakin sarki, domin lallai duk soyayyar da duniya take nuna maka a yanzu, to wallahi watarana sai ta sake ka" - "Kullum kada ka sake ka mayar da wannan duniyar tamkar wata madauwamar ka, babban mai hankali shine wanda yake yiwa duniya tamkar gidan ci-rani, wato gidan wani ɗan zama ne ƙan-ƙani ba mai dogon lokaci ba, da zarar ka gama rayuwarka sai ka tafi ka barta"  - "Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya bamu shawara da cewa "mu zamto a wannan duniyar tamkar baƙi ko kuma masu ƙetarar hanya" wato irin mutanen da basa sakankance wa a duk inda suka je burinsu kawai suyi abinda ya kawo su su koma inda suka fito, to mu kuma bautar Allah ce ta kawo mu duniyar, da zarar rayuwar mu ta ƙare zamu koma ga mahaliccin mu Allah"

TARIHIN SHEIKH IBRAHIM INYAS

 Tarihin Shehu Ibrahim Inyas  Daga ✍️Ismail Hussaini Alpholtawy    Dafarko dai Mai Karatu Zanfara da sunan ALLAH ﷽ Mun manta da tarihi Saikawai Labaran Duniya dakuma Kallace_Kallacen Film, Har wasu daga cikin Daliban Wannan bawan Allah din Sheikh Ibrahim Inyas mabiyansa Na Tijjaniyya Da Faidha. Basusan Tarihin Nasaba Saidai kawai Sunsan Littattafansa Wadanada yarubuta Kamarsu Kashiful Ilbasi, Dama Dawawinu_Ssittah. dama Sauran Littattafansa na Abyat.                              ﷽ اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ‎ Dafarkodai Sheikh Ibrahim inyas dai Asalinsa dan kasar Sanganiyane Agarin Kaulaha. Bayan Rasuwar Mahaifinsune alokacin da Sheikh Amadu Tijjani yazo yimasu Ta'aziyya, Sai Yanemi da da abashi dakin Soro domin Larabawa basa juran Zafi.      Yayansa Muhammadu Khalifa wanda Shine Magajin Mahaifinsu a fannin Khalifanci na Wannan Zawiyyan, Sai yace dashi ga ...

TARIHIN SAHABBAI Kashi na daya 001

  TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR SADDIK ALLAH YA YARDA DA SHI, (manzon Allah S. A. W) "yace ya Abubakar kai ne farko wanda zai shiga Aljanna daga al'umma ta" Sayyidina Abubakar shi ne Abdullahi dan Abu kuhafatu " usman" usman dan Amir dan Amir dan ka"abu dan sa"adu da taimu dan murratu dan ka"abu dan lu"aayu, bakuraishe. Bataime. Nasabarshi ta hadu da manzon allah ta wajan murratu dan ka"abu kakansu na biyar. Sunan shi a lokacin jahiliya "Abdul ka" aba" daya musuluta sai manzon allah ( S. A. W) yakara shi "Abdullahi" An yi mishi alkunya da Abubakar saboda riganyenshi wajan dabi"antuwa da kyamara halaye. Kuma an yimasa lakabi da saddik sabo da saurin bayar da gaskiyar shi ga dukkan abunda manzon allah (S. A. W) ya fada kuma manzon allah (S. A. W) yakara shi da "Atiku" shine mutumin da yafara musuluta a manyan. Shi ne mutum na farko, da ya fara kira zuwa ga addinin musulunci. Bayan manzon Allah Annabi Mu...

MATSALAR AQEEDAH

 GASKIYA AKWAI MATTSALA!!!! Sau nawa kake zama domin Bincike ko sauraron Yadda zaka gyara Ibadarka?????          Sau dadama idan na kadaita sai nayita tunani dan ganeda lammarin gudanar addini agun wasun mu. Zakaji mutum nakiran kansa musulmi amma farillan alwala ma bai sani balle in ta 'baci ya gyara farillan sallah ma bai saniba balle inyayi Rafkanuwa yagyara. Ko na wanka ballema ilimin gyaransu.     Wayyoooni duniya ina zaki damune kowa kagani abinci kawai yake nema kokuma yadda zai huta ko yadda zaiji dadin duniya gaba. Saidai kash itakuma tafiyarnan da take gaban mu batta da rana. Kawai zuwa take kwatsam kara zube ba zato ba tsammani.     To taya zamu tara guzirin komawa ga mahaliccin mu domin samun hujja garemu aranar sakamako?     Ansa     Mukoma munemi ilimin addini mugyara ibadu da mu'amalarmu kafinnan musami hanyar tsira. Wani abin ban takaici shine yawanci mukan jahilci lammarin addini bawai don rashinsaba ...

MUSULMI GA SAKO

 MUSULMI ATASHI AKAFA DAULA DAN SAMUN INGANTACCEN RAYUWA inji Shahararren malamin salafiyyannan Sheikh Muhammad Adam Albany Zaria.    Hakika shugaba yayi wadannan maganganu da shawarwarin agurare Ma bambanta da majalisai dadama. Domin nuni garemu ga hanyar tsira. Dakuma koyi da magabata. Don samun rayuwa Mai inganci, da zamantakewar rayuwa Mai tsafta. Ba kamar yadda wasu ke daukar zancen awata mahanga. Da tunani irinta miyagun mutani ba.  Ga zancen malam;  Tsokaci kan batun malam:     Saidai haryanzu banji wani shahararren mutum daga cikin malamai ko shugabanni daga cikin musulmiba wanda ke karfafa Zancen. Duk da cewar maganan maganice na ciwon dayake damun musulmin duniya baki daya. Saidaima wasu daga cikin miyagun mutane dasuke fassara zancen da wani salo nadaban, tayadda suke kokarin cire ma'anar maganan na hakika su shigoda wani al'amari nadabam.      Gadai Maganan da malam yayi; Mal. Yace ''Yakamata musulmi su kafa daula Dan gujewa ...

QALUBALE GA RAYUWAR 'YAN MATA

 📝  ✍️ ISMAIL HUSSAINI ADAM SMART DAN AREWA    ******* GABATARWA ******* Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu mai karatu.        Zanyi wannan rubutunne don nuni zuwaga yan uwana maza, domin kusan wa zaku auro ku kawo cikin gidanku, amatsayin abokiyar zama. Mata kuma su san dawa zasuyi qawance don gudun faďawa akomar halaka. Inda hali kutsaya kukaranta gabaki ďaya, domin zaka/zaki k'aru kuma inshaa Allahu zaku rabauta da waďannan zantuka nawa.       Ina bukatan addu'arku Allah ya haskaka qabarin mahaifina, dana mai karatu idan kuma suna raye, Allah yasa mugama dasu lafiya yakuma basu rabon cikawa da imani. Allah ka albarkaci rayuwar lahaifiyata da ayyukan alkhairi daku mumaďin gabaki ďaya. ******** 'YAN MATAN JAMI'A ********    Allah sarki rayuwarsu gwanin birgewane, saidai kuma abin tausayine awani bangaren, tayadda zaka samesu mafi yawancinsu akwai tsaftar jiki dana tufi. sannan sun san yakamata matuka, Saidai was...