MATAKAN TARBIYYA AKASAR HAUSA
MATAKAN TARBIYYA Daga. Alqalamin Ismail Smart Dasunan ALLAH Mai RAHAMA Mai
JINKAI. Haqiqa tarbiyya dolece a addinin mu na musulunci musan man ma na
iyalanka/ki Domin ALLAH MADAUKAKI yana cewa: ﷽ یا أیهاالذین آمنو قو أنفسکم
وأهلیکم نارا وقودها الناس والحجارة Awannan aya ALLAH yayi umarni ga Muminai dasu
Kare kansu da iyalansu daga wata wutta Wanda yakasance makamashinta mutane ne
dakuma duwatsu. ALLAH UBANGIJI katsaremu amin ya RABBI. Awannan 'Bangaren
Nakeson nayi rubutu domin yan uwa musulmai su anfana. ALLAH MADAUKAKIN SARKI ya
dafamin MATAKIN FARKO (Neman Aure zuwa da yakai 5yrs) Dole Akan kowa Idan yazo
neman aure Yanemi Mai addini Da hali nagari Da kakkyawar zuciya. Ba kawai kyawun
fuskaba ko wani martaba ko nasabar Abokin zama ba. Kuma yazamto anyi auren
tanasonsa yana sonta. Domin hakanne Zaisa suji dadin zamantakewarsu ta Aure Kuma
hakan Zaisa yayansu sutaso dason junansu Da Bin doka ko umarnin Da akayi masu.
Domin kada yazamto uwa tace fari uba yace Bahakaneba Baki yake. Bayan haka
Yazama dole asakawa yaro kakkyawar suna alokacin dayake jinjiri. Yazama dole ka
karantar Da matanka tsarin tarbiyyar addinin musulunci ko kasa akarantar da ita
Awannan sahar kokuma MA kafin wannnan lokacin. Ma'ana kafin ta sami d'a (yara).
Domin kaso saba'in Cikin Dari (70%) Na Tarbiyyar cikin Gida maqasudinsa na
uwace. Yazama dole takasance Mai Lura da Meke gudana me sukeso me yakamata suyi
ko so Bari duk wadannan uwace takeda hakkin koyar da yaranta. Dakuma koyardasu
Ibaadaat Kamar Sallah Azumi Dakuma koyamusu karatun Alqur'ani da tilawarsa dama
haddarsa. Har sukai 10yrs Kafin daga bisani Sai Aturasu Islamiya. Sucigaba da
karatu daneman ilimin addini. Hakan zaisa sutaso da ganin girman iyayansu. Dama
duk wanda yagirmesu tayadda basai ance ga malam waneba kafin sudaina abinda
sukeyi. MATAKI NA BIYU (Daga 5yrs zuwa 15 to 18yrs) Dolene akan iyaye su San
abokanan yayansu, Susan Kuma menene alaqarsu dasu Domin duk kyawun tarbiyyar
dakasamu agida abokai sukan wargazashi, matsawar dakayi abota da marasa tarbiyya
koda baka zama tamkarsu ba. Zaka rudu da wani hali acikin munanan halayyarsu.
Yazama dole iyaye su bawa yayansu tarbiyyar addini da wayewar rayuwa tahanyar
sanaddasu yadda zasuyi addini da hikimomin tsara rayuwa bisa kykkyawar tsari.
Kamar koyamusu dabarun kare kai da addu'o'in neman tsari da kariya. Da sanardasu
tarihohi Wanda zasu sami hikima da, wa'azozi acikinsa. Domin abinciken masana
kwakwalwar dan adam sun yarda akan cewa kwakwalwar dan adam takan bude da adana
bayanai alokacin da mutum yake dan shekaru takwas (8) zuwa Sha biyar (15) koda
haddane mutum yafi nutsuwa dashi awannan lokacin Inhar kaga yaro ya natsu
awannan lokacin to tabbas ana kyautata zaton shiryayye ne. Inkuma ya kangare
kuwa yanada wuyar shiryuwa Yakamata iyaye sudunga zama da yaransu suna zantawa
dasu domin suji damuwoyi da bukatunsu, Harsu san tahanyar da zasu bullo musu
gurin bada shawara ko kore musu matsalarsu tarayuwa. MATAKI NA UKU NAKARSHE
(Daga 15/18yrs. zuwa auraddasu) Yakamata iyaye su lura da yayansu su san menene
wane/wacce tafi/yafi kwarewa akai saisu dage gurin nema masu mafita ta hanyar
basu tallafi ko jari domin samun damar gudanar da harkokin rayuwarsa cikin sauki
batare da yana zauneba saidai kullum abashi. Domin hakan yana kashe zuciyar
mutum yazanto baya iya kafuwa da kansa balle ma har yagina wasu. Saidai kullum a
bani_bani sai kuma bin abokai da yawace yawacen banza da hofi, da bin bangar
siyasa, wadda daga karshe ke jawo mutum yakoma ta'asa da 'barna acikin al'uma
kokuma ma yakama shaye_shaye da bin mugaye mutane. Duk adalilin rashin aikin yi.
ALLAH ya tsaremu da zuri'armu baki daya. Rashin aikinyi na daya daga cikin
abubuwa mafi girma wanda suke lalata tarbiyya arayuwar mutane. Allah ka bawa
iyayen mu hakurin zama damu kasauke musu hanyar dazasu tarbiyyantar damu
tarbiyya ta Addinin musulunci, ALLAH kajikan maifina kahaskaka qabrinsa.
Comments