NASIHOHI DAGA NA 2024 ZUWA NA 2026

MU DINGA NAZARI AKAN TAIMAKAWA ADDININ ALLAH NASIHA MUHIMMIYA (2026) 
 Kayi Nazari Dakyau Tinda Kake a Rayuwa Wanne Taimako Ka Taba Yima Addinin Allah Wadda Ko Bayan Ranka Zai Iya Zama Sadaqatuj Jariya Gareka Kuma Kaci Gaba Da Taimakawa Gwar Gwadon Iko Idan Kuwa Ka Bin Cika Kaga Babu Tofa Har Yanzu Kana Da Sauran Dama Wadda Baza Kayi Nadama Ba Sai Kayi Qoqari Ka Ginawa Kanka Alherin Dazai Bika a Qabari Wadda Zai Yalwata Makwancinka Saboda Haka Muyi Qoqari Mu Ginawa Kan Mu Alherin Dazai Bimu Qabari Ta Fuskar Yawan Taimako Zuwa Ga Addinin Allah Da Kuma Mabuqata Da Sannu Allah Zai Isar Zuwa Ga Mizanin Mu Amma Sai Munyi Haquri Mun Kuma Kawar Da Kayi Da Hudubar Shaidan Ta Fuskar Talauci Da Yake Bijiro Mana a Yayin Taimako Kafin Mu Iya Taimakawa Addini Har Mu Sami Ingantaccen Masauki a Qabari Jama'a Mun Fahimta..........? GATAN DA ADAN ADAM YA SAMU SHINE KASANTUWARSA DA YAYI A RAYE NASIHA [2025] Babu Shakka Duk Wadda Allah s.w.t Ya Barshi Yini Daya To Ba Qaramin Gata Yayi Masa Ba Sannan Ya Qara Maka Yini Daya Har Dai Wasu Adadi Na Satikai Ko Watanni Koma Shekaru Haqiqa Ba Qaramin Gata Yayi Maka Ba Domin Babu Wadda Yasan Gatan Da Mai Rai Yake Ciki Sai Wanda Ya Mutu Kai Da Kake Da Rai Baza Kasan Gatan Da Kake Dashi Ba Sai Ranar Da Akace Ba Mutum Sannan Yake Tina Cewa Rayuwar Da Allah Ya Bashi Lalle Ba Qaramin Gata Yai Masa Ba Zaiyyi Burin Inama a Dawo Dashi Duniya Yayi Sallah Koda Raka"a Biyu Rak a Mayar Dashi Watakila Ta Amfaneshi Domin Dazarar Dan Adam Ya Mutu Tofa Magana Ta Qare To Amma Da Yake Shaidan Yayi Rantsuwa Cewa Bazai Kyale Dan Adam Yasami Wannan Rabautar Ba Shiyasa Ita Kanta Duniyar Ta Kowacce Irin Fuska Rudi Takeyi Kuma Babu Wadda Zai Biyemata Face Yayi Nadama Don Manzon Allah Ya Razanar a Hadisi Cewa (Fattaqu Duniya) Wato Kuji Tsoron Duniya Kamar Yadda Malamai Sukace Shine Kuji Tsoron Fitin Tinun Da Dunuyar Zata Riqa Shigowa Da Sabbin Ababe Ta Fuskar Fasadi Domin Halamu Ne Na Dake Nuna Yuwuwar Tashin Qiyama Fatan Mu Dai Shine Allah s.w.t Yasa Mufi Qarfin Zukatan Mu Daga Aikata Dukkanin Wani Fasadi a Ban Qasa AminMUYI RIQO DA SUNNAR MANZON ALLAH S.A.W DOMIN ITA KADAI CE JIRGIN CETO NASIHA (2024) Sunnah Annabi s.a.w Itace Jirgin Ceto Wadda Zatasa Dan Adam Ya Rabauta Duniya Da Lahira Kamar Yadda Hadisin Dara Qudiniy Ya Tabbatar Manzon Allah s.a.w Yace (Man Tamassaka Bi Sunnati Dakalal Jannata) Annabi Yace Duk Wadda Yayi Riqo Da Summata Zai Shiga Aljanna . Baya Ga Haka Ingantaccen Hadisin Bukhari Shima Ya Tabbar Da Cewa Cikakkiyar Biyayya Zuwa Ga Manzon Allah s.a.w Yana Gadarwa Dan Adam Shiga Aljanna Kamar Yadda Hadisi Ya Tababtar Annabi Yace (Man Tamassaka Bi Sumnati Dakalal Jannata) Baga Ga Haka Nassin Qur'ani Ya Tabbar Da Cewa Cikakkiyar Biyayya Zuwa ga Allah Da Manzonsa Suna Gadarwa Dan Adam Shiga Cikin Aljanna Wadda Qoramu Ke Gudana Wadda Ya Bijire Kuwa Ubangiji Zai Azabtar Dashi Azaba Mai Radadi Kamar Yadda Nassi Ya Tabbatar Dauki Koda Suratul Alfath Aya ta {17)} Wannan Ya Tabbatar Mana Da Cewa Duk Wani Addini Daza a Danqatashi Da Addini Idan Bai Dace Da Sunnar Manzon Allah s.a.w Bidi'a Sunansa Kuma Babu Abin Dake Gadarwa Dan Adam Face Halaka Jama'a Mu Kiyaye Allah Ka Fahimtar Damu Sunnar Manzon Allah s.a.w Ka Bamu Ikon Binta Da Gaskiya, Amin.

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage