Nasiha Zuwaga Yan Mata

"TSAYA KI JI ƘANWATA

      GA SHAWARA


Ƴan mata nasan tabbas kina da masaniya cewar a duniyar da muke rayuwa ta zahiri ba ta Facebook ba, mazan aure sun yi ƙaranci saboda tsarin Allah na yawaitar mata, tsadar rayuwa da kuma talaucin da muke ciki. To ki rufawa kanki asiri kar ki ɗauki zugar "kar ki auri wanda ba zai barki ki yi karatu da aiki ba". Mai kulawa da addinin da zai bayar da abinci uku da kulawa daidai gwargwado kaɗai a ke nema. In kin ƙi kuma, to akwai wata magana. Biyo ni ki ji batu.

Akwai ƴan banzan maza waɗanda ba auren za su yi ba, amma suna yawon rage zafin balaga da yara irinki. Ƙanwata kina da zaɓin tsayawa ki kame mutuncinki, ki yi addu'ar samun me hankali da rufin asiri ko da zai hana ki karatun boko da aiki, ko kuma ki ci gaba da zaman benci a gidanku tare da rage gafin balagarki kema da balagaggun yaran can masu tara suma da gaisuwar "ya kike"!

Ya ke ƙanwata ki dubi gidajen unguwarku kaf ki ƙirga ƴan matan kowane gida. Fara daga ƴan shekara 14 zuwa 20, sannan daga 21 zuwa 30/30+. Nawa ne suka gama Sakandire? Nawa ne a koleji? Nawa ne a jami'a? Nawa ne suka gama jami'a? Nawa ne ke neman miji da aiki? Nawa ne kullum ke zance cikin mota me tint ko a ke kawo su gida a irin wannan motar? Nawa ne kuma lalatattun da kowa ya gane lalatattun ne?

Ƙanwata a duba waɗannan sannan se ki duba yiwuwar ɗaukan waccen shawara. Amma, a haƙiƙanin gaskiya duk sharaɗin da ba na Allah da Annabi (S) ba, to wannan sharaɗi ɓatacce ne. Gindaya wa manemin aurenki sharuɗɗan karatu da aiki kafin aurenki saɓa wa Allah ne, domin ba sa cikin sharuɗɗan aure a Addini. Amma babu laifi ki roƙe shi kan haka in ba me ra'ayin hakan bane. Ku tattauna sosai. In ya amince zai barki sai ki godewa Allah. In ya ce bazai bari ba, to sai ki duba ki yi Istikhara, ki nemi shawarar manya, kuma a duba samunsa, nagartarsa, in kin aminta sai ki aure shi. Muna miki fatan alkhairi!

Ki buɗe idanunki da kyau don tantance abokan shawara, ko waɗanda zasu faɗi zance ki ɗauka. A sha'anin aure, babbar ƙawarki ta zamto mahaifiyarki, babbar yayarki, ƴar uwar mahaifiyarki ko mahaifinki, ƙawar mahaifiyarki ko malamarki ta addini me shekaru ba yarinya ba kamarki. Kar ki yadda da wani namiji ya zo ya ce ga shawara sai dai in ɗan uwanki na cikin gidanku ne, ko ƙanin mahaifi ko mahaifiya, ko wani malamin addini me shekaru ba yasayyadi ɗan saurayi ba.

Mas'alar aure na da wuyar sha'ani. Ƴan uwanki da ke kewaye da ke sune suka san halin da kike ciki ba wani ko wata a social media ba. Daga nesa ba a tantance zahirin al'amuran aure duk bayanin da za a yi wa me bayar da shawarar. Don haka ki nutsu ƙanwata ka da ƴan social media su hana ki aure, ko su kashe miki auren da Allah ya yi miki ni'imar samunsa.

Na barki haka. Sai na dawo kan sha'anin aiki. Kar ki zata zan haramta shi. Noooo! Wallahi halal ne ga duk wacce zata kama mutuncin kata domin azamani manzon Allah(S.A.W) Ansamu mata masu aiki don rufawa junansu asiri hardama aikin gona. Amma dai ina da shawara kan yanda ya kamata ki nemi izinin mijinki ko wanda zai aure ki a kanshi. Kuma duk abinda na faɗa ba kawai ɗauka za ki yi ba. Tattauna da manyan masoyanki na gida a kan haka tukunna. Sai anjima."

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage