YIN AIKI DOMIN ALLAH* {1}

*SHEIKH ALBANY DA'AWA GROUP* * Yaku bayin Allah, kusani cewa Allah ba ya karbar aikin bayi sai idan an yi aikin dominsa. Duk wanda ya aikata aiki ya yi tarayya da Allah a cikin wannan aiki, to Allah ya wadatu ga barin karbar wannan aikin, duk kuwa yadda wannan aiki yake da yawa. Allah yana cewa: ( إِنَّا أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ فَاعْبُدِ اللَّهَ مُخْلِصًا لَهُ الدِّينَ 2أَلَا لِلَّهِ الدِّينُ الْخَالِصُ3) [الزمر: ٢ – ٣]. *Haqiqa mun saukar maka da littafi da gaskiya, ka bautawa Allah Shi kadai kana mai tsarkake aiki dominsa. Ku saurara tsarkakakken addini na Allah ne”.* Hakanan yake cewa: (قُلْ أَمَرَ رَبِّي بِالْقِسْطِ وَأَقِيمُوا وُجُوهَكُمْ عِنْدَ كُلِّ مَسْجِدٍ وَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ29) [الأعراف: 29] *(Ka ce da su, Ubangijina ya yi umarni da tsayar da adalci. Kuma tsayar da fiskokinku a kowane masallaci. Kuma ku bautawa masa kuna masu tsarkake bauta dominsa).* Ya kuma cewa a wani wurin: (فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ14) [غافر: 14] *(Ku bautawa Allah kuna masu tsarkake addini gare shi, Shi kadai, koda kafirai sun qi).* Hakanan ya sake cewa: (هُوَ الْحَيُّ لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ فَادْعُوهُ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ65) [غافر: 65] *(Shi ne rayayye babu abin bauta da gaskiya sai shi. To ku bauta masa kuna masu tsarkake addini gare shi. Gudiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai).* Ya sake cewa, (وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاءَ وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ5) [البينة: 5] *(Ba a umarce su da komai ba sai su bauta wa Allah suna masu tsarkake addini agare shi. Kuma su tsaida sallah, su ba da zakka, wannan shi ne addinin miqaqqiyar hanya).* Yin aiki domin Allah shi ne, ka yi aiki domin neman yardar Allah ba ta tare da hada shi da wani ba. Ba riya, ba yi don a ji. Idan aiki ya zama haka, to ya lalace, mai yin aikin ma ya halaka. *الله تعالى أعلم* _*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_ *Telegram* https://t.me/joinchat/SoaVkBryqONVNGyU8dDpLQ DAKA *SHEIK ALBANY DA'AWA GROUP* GA MASU SAN SHIGA GROUP KO AIKO DA TAMBAYA ZASU IYA TUROWA TA WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA 08179713163 Alpholtawy

Comments

جزاك اللهُ‎ جزاك اللهُ‎

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Things That Can Increase A Woman’s Chances of Conceiving Twins