ILLOLIN SANYA HOTO GA ƳA MACE A SOCIAL MEDIA
___________________________________
•
Haƙiƙa babu Mace mafi Girman Kuskure kamar macen da zata Ɗauki Surar jikinta sanye da Kaya masu Bayyana Tsiraicinta sannan ta ɗorashi a Social Media, Mace mai irin wannan Tabbas ta kuka da kanta matukar bata daina ba Akwai Ƙalubale da zai rinƙa fuskantarta da Sannu zata Gane hakan daga Ƴan Iskan Samarin Social Media.
•
•
Mafi Ganganci mace ita ce Wacce Take yin Post na Hotunanta ko wane kalan Mutum yaga Hoton da Abinda zai furta na Albarkacin Bakinsa, wani yace kinyi Kyau, wani kuma ya Tsine miki Albarka, ke ana yabonki a ganinki Kyakkyawace kina Washe baki ke Gaki mai Tarin Followers to ki sani duk abinda kika Ɗora da Hannunki Wallahi sai Ubangiji yayi miki Hisabi a Kansa.
•
•
Yana daga cikin Illolin Ɗora Hoton Mace a Social Media shine, a yayin data Dora duk wanda yaga Post ɗin da Hoton dake jiki idan Abin ya bashi Sha'awa yakan yi Save a Wayarsa, daga nan ne zai samu yayi Post na Batsa da iskanci ya ɗora Hotonki a zuwan kece kuma duk Duniya su gani, Shin me hakan ya Amfanar Dake?
•
•
Ba zaki san Illar Ɗora Hotunanki a Social Media ba sai lokacin da kika so yin Aure, ke a Tunaninki kina Shiga Tik tok, Instagram, Snap da Twetter, haɗi da Facebook kina Fallasa Surar da Allah yayi miki a hakan kike tunanin Mutumin Arziki Nagartacce mai son nemawa Ƴayansa Uwa Tagari zai yi Sha'awar Aurenki?
•
•
•
A Matsayinki na Bazawara zata iya kasancewa kaddara ce ta fito dake daga Gidan Mijinki, Wani Mijinta Mutuwa yayi, matukar kina Nemawa kanki mutunci da Daraja sannan kina son samun banbanci tsakanin Zawarawan da suke Rashin Mutunci a Social Media to ki riƙe Mutuncinki, Sakin Hotuna barkatai ba naki bane, domin wani idan ya buƙaci Aurenki da Gaske kuma yaga irin abinda kike ko yaji labari komai zai iya Faruwa.
=
=
ALLAH ka tsare mana Mutuncinmu da Martabarmu Duniya da Lahira ءامين يارب
=
=
Mujahedeen Magaji Abubakar✍🏻
14-08-1443AH.
15/04/2022
Alpholtawy

Comments