MAJOR DA MUQARRABANSA AN KYAUTATA MUSU ZATO
ASHE SUNE SANADIN HADA BANGARORIN BOKO HARAM YAKI DA JUNA
Jama'a ku nutsu ku
karanta wannan bayanan da kyau Tsarki ya tabbata ga Allah, rikicin bangarorin
kungiyar Boko Haram abin boye ya fara fitowa fili, marigayi shugaban sojoji
Janar Ibrahim Attahiru da shugaban leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaro
na rundinar sojin Nigeria marigayi Birgediya Janar Abdulrahman Kuliya sune
sanadin haddasa tsoho da sabon rikici tsakanin 'yan Boko Haram wanda ake
kyautata tsammanin Shekau yayi mushe A cikin wani sabon rahoto wanda jaridar PR
Nigeria ta wallafa jaridar da take da kusanci da rundinar sojin Nigeria, tace
marigayi Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya shine yake jagorantar tawagar mayaka
sojojin kundunbala a lokacin da marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru yake
matsayin babban kwamandan rundinar Operation Lafiya Dole a Arewa maso gabashin
Nigeria Kafin a cire shi, a lokacin wasu tawagar mayakan Boko Haram sun tuba sun
mika kai wato sun yanke shawaran ajiye makamansa wa rundinar Operation Lafiya
Dole, to sai marigayi Birgediya Janar Abdulrrahman Kuliya ya bada shawara wa
babban kwamandan rundinar marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru shawaran cewa
a bar tubabbun mayakan na Boko Haram cikin sansanin Boko Haram, domin su zama
masu leken asiri wa sojoji, sannan ayi amfani dasu wajen haddasa sabani a
tsakanin Boko Haram Yana daga cikin dabarun yaki a ilmin tsaro, idan akwai
kungiyoyi cikin 'yan ta'adda ko 'yan bindiga, to idan har gwamnati ko hukumomin
tsaro tana so ta karya su, to sai tabi wasu hanyoyin sirri ta haddasa rikici da
sabani a tsakanin kungiyoyin, hakan zai zama sanadi na tarwatsewar su To a
lokacin Janar Attahiru ya amince da shawaran na Janar Kuliya, wanda hakan ya
taimaka sosai wajen gwara kawunan bangarori biyu na Boko Haram, wato bangaren
ISWAP na su Habib Muhammad Yusuf Al-barnawiy da Boko Haram na Abubakar Shekau
Bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya nada marigayi Janar Attahiru a matsayin
sabon shugaban sojojin kasa na Nigeria wanda ya maye gurbin Janar Buratai, sai
Janar Attahiru ya dauko Janar Abdurrahman Kuliya ya bashi jagorancin bangaren
Intelligence na rundinar sojin Nigeria domin su daura daga inda suka tsaya
lokacin da suke jan ragamar rundinar Operation Lafiya Dole suka gwara kan 'yan
Boko Haram Bai wuce sati biyu ba, rundinar sojin Nigeria karkashin jagorancin
Janar Attahiru ta canza sunan rundinar da take jan ragamar yaki da Boko Haram a
Arewa maso gabas daga OPERATION LAFIYA DOLE zuwa OPERATION HADIN KAI da manufar
samar da cikakken hadin kai tsakanin tubabbun 'yan Boko Haram da sojojin
kundunbala, marigayi Janar Abdulrahman Kuliya na daga cikin wadanda suka bada
shawaran canzawa rundinar suna Hakan yayi tasiri matuka a jejin sambisa, tun
daga rikicin raba man fetur da ya faru a tsakanin 'yan Boko Haram bangaren
Shekau da Al-barnawiy akan iyakar Kamaru da Nigeria suka gwabza yaki da juna, da
rikicin da ya haddasa Shekau ya kashe wasu Kwamandojin yakinsa guda hudu wanda
ya zarga da kokarin cin amanarsa wajen sanar da bangaren su Al-barnawiy
maboyarsa na sirri dake kan tsaunin dutsen mandara a yankin Gwoza Wanda hakan ne
ya taimaka wa su Al-barnawiy suka gano inda Shekau yake zuwa ya wuni suka
rutsashi a can, a zaman sulhu akace Shekau ya tarwatsa kansa da bomb ya hallaka
da wadanda ake zaman da su, kwana daya da ya fitar da audio wanda zakuji yana
fadin sakon cewa anci amanarsa duk da ya kashe wadannan kwamandoji guda hudu
nasa, amma su Al-barnawiy sun isa yadda yake, abinda ake tunanin yanzu haka
Shekau yayi mushe duk da dai har yanzu babu tabbaci Marigayi Janar Ibrahim
Attahiru da Birgediya Janar Abdulrahman Kuliya sune sanadin haddasa wannan
mummunan rikici tsakanin 'yan Boko Haram a jejin Sambisa wanda ake tunanin
Shekau yayi mushe ya zama abincin wutar jahannama, shin maciya amanar tsaron
Nigeria zasu barsu su wanye lafiya saboda suna ganin wadannan jarumai da gaske
suke zasu kawar da Boko Haram? Me yasa suka fado a jirgi lokaci daya suka mutu?,
anya kuwa..? Sai na yanzu nake tuna abinda ya faru lokacin da shugaba Buhari ya
cire su Buratai ya kawo su Attairu, babu wanda aka biya jaridu kudi aka masa
batanci kamar Janar Attahiru, tun daga hawansa, bai ma shiga ofis ba aka fara
masa batanci, a Nigeria ba'a biyan kudi a jaridu a bata mutanen banza maciya
amana, mutanen kirki ake batawa, jama'a ku tuna wannan Insha Allahu Nigeria sai
ta ga bayan Boko Haram ko da maciya amana ba su so hakan ba Allah Ka karbi
shahadar su Janar Attahiru Allah Ka maye mana gurbinsu da wadanda zasu zama
sanadin kawar da Boko Haram daga doro duniya Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum copied by
#Smart_Dan_Arewa
Daga 💬Datti Assalafy
Comments