Posts

TARBIYYA Fitowa ta biyu

  MATAKAN TARBIYYA Daga. Alqalamin Ismail Smart Dasunan ALLAH Mai RAHAMA Mai JINKAI. Haqiqa tarbiyya dolece a addinin mu na musulunci musan man ma na iyalanka/ki Domin ALLAH MADAUKAKI yana cewa: ﷽ یا أیهاالذین آمنو قو أنفسکم وأهلیکم نارا وقودها الناس والحجارة Awannan aya ALLAH yayi umarni ga Muminai dasu Kare kansu da iyalansu daga wata wutta Wanda yakasance makamashinta mutane ne dakuma duwatsu. ALLAH UBANGIJI katsaremu amin ya RABBI. Awannan 'Bangaren Nakeson nayi rubutu domin yan uwa musulmai su anfana. ALLAH MADAUKAKIN SARKI ya dafamin MATAKIN FARKO (Neman Aure zuwa da yakai 5yrs) Dole Akan kowa Idan yazo neman aure Yanemi Mai addini Da hali nagari Da kakkyawar zuciya. Ba kawai kyawun fuskaba ko wani martaba ko nasabar Abokin zama ba. Kuma yazamto anyi auren tanasonsa yana sonta. Domin hakanne Zaisa suji dadin zamantakewarsu ta Aure Kuma hakan Zaisa yayansu sutaso dason junansu Da Bin doka ko umarnin Da akayi masu. Domin kada yazamto uwa tace fari uba yace...

SUWAYE AHLUSSUNNAH

 MAFAKAR SUNNAH AYAU!!!         Haqiqah Babu batun Sonkai, Salafawa da 'yan izala sune ke da'awar sunnah Haqiqanin ta zallar madarar sunnah babu gauraye.  Dalilin wannan rubutu nawa: Shine nuna mecece koyarwar aqeedar sunnah. Da manufar Izala da Salafawa akan sunna dakuma mecece asalin haqiqanin aqidar sunnah    ********MECECE AQIDAH******** Aqidah:  amahangar Arufai (Malamai)_ wata hanyace wacce mutane suka kebance yadda zasu yi addini karkashin wata mazhaba bisa fahimtar magabata na farko, Bugu da kariaqidah takasance abace wacce take a aikace da furincin baka banda qudirin zuci. Ma'ana Azuci ni musulmine kuma nayarda da dukkan shika_shikan musulunci ina aikatasu amma bisa mazhabar malikiyya. To idan hakane madogarata bani da Ikon tilasta maibin mazhabar shafi'iyyah ko  ko hanafiyya. Bani damar cewa sai sunbi Hambaliyya  Idan mukayi duba danganeda yanayi nayanzu yadda rayuwa tashige rudani yadda Ake kawo abubuwa daban daban aciki...

HUKUNCIN AURE TSAKANK WANDA SUKAYI MUMMUNAR MU'AMALA KAFIN AURE

  Assalam alaikum warahamatullah Allah ya taimaki malam ya saka michi da taimakon da yake ga al'umma musulmi. Malam wani abokina ne suke son yin aure da wata to sun kusanci juna yanzu ya tambayi wani MALAM ya ce michi babu aure tsakanin su sai ita ta ce ta tambayi wani malam ya ce mata indai sunka bari har sunkayi wata uku bu su kusanci juna ba auren su ya halata to MALAM mine ne gaskiyar al'amarin?   AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Aure tsakanin Mazinata, Malamai basuyi sa'bani game da halaccinsa ba. Amma aure tsakanin Namiji Mazinaci da Macen da bata zina, ko kuma tsakanin Mazinaciya da Namiji wanda ba ya zina, shine wasu Maluman (Kamar Imamu Ahmad) suka ce bai halatta ba. Amma su Mazinata zasu iya yin aure atsakaninsu mutukar dai ita Macen taje tayi Istibra'i. Wato zata zauna tsawon jini uku ko kuma jini guda (inji wasu maluman). Bayan ta kammala wannan za'a iya daura musu aure. Amma dai zaifi kyau garesu su tuba daga wannan mummuna...

MUKULA DA AMANAR ALLAH

 BA'A ADDINI DA SON ZUCIYA  !!!         Ana addine da abinda yazo ashari'a    Shi Hidimar Addini ba irinta Siyasa bace. Dan Allah idan baka saniba kadaina kutse acikin lamarin.    Bana jin dadin irin wadannan abubuwan da mukeyiwa juna, Wallahil aziim idan wadanda ba musulmiba sukaga irin wadannan Musanya da Cin mutuncin da mukeyiwa junan mun,  dadi sukeji.            Idan kasan baka da ilimi awani zancen daka tsinkaya a Audio, na lamari addini ko A social media kada kace zakayi Raddi direct.    Nasan baza ka rasa malamin da ka yadda dashi ba ayankinka, kamata yayi kaje ya warwarema lamarin, inda kuskuren yake saikayi Contact da mai Wannan jawabin. kuyi magana ta fahimta dashi Agunsa zakasami karin bayani, daga nan sai ka sam hujja. Haka ake magance mummunar zance kuma in yanada kuskurema me iyuwa ya koma kan wannan jawabin nasa yayi gyara kokuma ya warware abinda yashigewa duniya duhu. Wannan ...

'YAN MATAN ZAMANI GA SA'KO

  'YAN MATAN ZAMANI KO 'YAN SON ZUCIYA? A duk sanda naji mata na kukan wahalar samun miji, ko aurensu na yawan mutuwa nakan girgiza kai na wuce kawai, domin kuwa hausawa na cewa" kowa ya sayi rariya yasan zata zubar da ruwa." Da zaka ce musu laifinsu ke janyo musu wannan matsala, da yawansu inkari zasu yi, koda yake ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai wacce kaddara ke fadawa, akwai kuma wacce ta hadu da abokin zama bana gari ba, amma dai mafi yawa laifin daga wajen matan ne. Duk wacce tace maka bata sami miji ba, kace da ita bata sami wanda take so ba kawai, domin Allah ya jarrabi matan wannan lokaci da son auren maikudi wanda za'a dinga buga misali a cikin kawaye, mafi yawan matan dake kokawa da rashin samun miji akwai mazan dake zuwa da niyyar aurensu wanda suke ganin kamar ba ajinsu bane, ta sanadin hakan sai mace ta kusan tsufa a gidansu babu aure, wasu Allah kan tarfawa garinsu nono su sami irin mijin da suke son aura, amma sai zaman auran ya gagara ayi ...

MAJOR DA MUQARRABANSA AN KYAUTATA MUSU ZATO

ASHE SUNE SANADIN HADA BANGARORIN BOKO HARAM YAKI DA JUNA Jama'a ku nutsu ku karanta wannan bayanan da kyau Tsarki ya tabbata ga Allah, rikicin bangarorin kungiyar Boko Haram abin boye ya fara fitowa fili, marigayi shugaban sojoji Janar Ibrahim Attahiru da shugaban leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaro na rundinar sojin Nigeria marigayi Birgediya Janar Abdulrahman Kuliya sune sanadin haddasa tsoho da sabon rikici tsakanin 'yan Boko Haram wanda ake kyautata tsammanin Shekau yayi mushe A cikin wani sabon rahoto wanda jaridar PR Nigeria ta wallafa jaridar da take da kusanci da rundinar sojin Nigeria, tace marigayi Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya shine yake jagorantar tawagar mayaka sojojin kundunbala a lokacin da marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru yake matsayin babban kwamandan rundinar Operation Lafiya Dole a Arewa maso gabashin Nigeria Kafin a cire shi, a lokacin wasu tawagar mayakan Boko Haram sun tuba sun mika kai wato sun yanke shawaran ajiye makamansa wa run...

RAYUWA ABAR TSORO CE

  *BABU UZRI BAYAN MUTUWA* -  "Duk wani uzrin da bawa yake ƙunshe dashi a lokacin rayuwarsa ne kaɗai yake da ikon aiwatar dashi, yana mutuwa shikenan uzri ya ƙare, abinda mutum ya shuka shi zai girba" - "Bayan mutuwarka a lokacin da aka ɗauke ka izuwa makwancin ka, komai yana jin abinda kake faɗa ga masu ɗaukar ka, amma saidai su mutanen da suka ɗauke ka ɗin basa taɓa jin abinda kake faɗa" - "Ya kai miskĩni! Lallai ka sani cewa fa, a lokacin da ka mutu shikenan taka ta ƙare, bayan an ɗauke ka acikin makara babu wanda yake fuskantar halin da kake ciki balle ya karɓi ƙorafinka, face dabbobi ko bishiyoyi, sai kuma ubangijin taliƙai, to ka gabatarwa da kanka wani alkhairi wanda ba za kayi nadama ba bayan mutuwarka"