HUKUNCIN AURE TSAKANK WANDA SUKAYI MUMMUNAR MU'AMALA KAFIN AURE

 Assalam alaikum warahamatullah Allah ya taimaki malam ya saka michi da taimakon da yake ga al'umma musulmi.

Malam wani abokina ne suke son yin aure da wata to sun kusanci juna yanzu ya tambayi wani MALAM ya ce michi babu aure tsakanin su sai ita ta ce ta tambayi wani malam ya ce mata indai sunka bari har sunkayi wata uku bu su kusanci juna ba auren su ya halata to MALAM mine ne gaskiyar al'amarin?

 

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Aure tsakanin Mazinata, Malamai basuyi sa'bani game da halaccinsa ba. Amma aure tsakanin Namiji Mazinaci da Macen da bata zina, ko kuma tsakanin Mazinaciya da Namiji wanda ba ya zina, shine wasu Maluman (Kamar Imamu Ahmad) suka ce bai halatta ba.

Amma su Mazinata zasu iya yin aure atsakaninsu mutukar dai ita Macen taje tayi Istibra'i. Wato zata zauna tsawon jini uku ko kuma jini guda (inji wasu maluman).

Bayan ta kammala wannan za'a iya daura musu aure. Amma dai zaifi kyau garesu su tuba daga wannan mummunan laifin da suka aikata, in dai suna bukatar samun albarka cikin auren nasu.

Malamai suna bada Misali da wani abinda ya faru azamanin Sayyiduna Abubakrin (rta) an kama wasu Mazinata saurayi da budurwa. Bayan anyi musu adadin bulalar da shari'a tace, to Sai Sayyiduna Abubakrin (rta) ya daura musu aure.

Da wannan ne Malamai suke kafa hujjar halaccin aure tsakanin Mazinaci da Mazinaciya.

Ya Allah ka karemu daga zina da dangoginta. Ka tsare mana dukkan ga'bbanmu daga aikin sa'bonka.

WALLAHU A'ALAM.

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage