Posts

MUKULA DA AMANAR ALLAH

 BA'A ADDINI DA SON ZUCIYA  !!!         Ana addine da abinda yazo ashari'a    Shi Hidimar Addini ba irinta Siyasa bace. Dan Allah idan baka saniba kadaina kutse acikin lamarin.    Bana jin dadin irin wadannan abubuwan da mukeyiwa juna, Wallahil aziim idan wadanda ba musulmiba sukaga irin wadannan Musanya da Cin mutuncin da mukeyiwa junan mun,  dadi sukeji.            Idan kasan baka da ilimi awani zancen daka tsinkaya a Audio, na lamari addini ko A social media kada kace zakayi Raddi direct.    Nasan baza ka rasa malamin da ka yadda dashi ba ayankinka, kamata yayi kaje ya warwarema lamarin, inda kuskuren yake saikayi Contact da mai Wannan jawabin. kuyi magana ta fahimta dashi Agunsa zakasami karin bayani, daga nan sai ka sam hujja. Haka ake magance mummunar zance kuma in yanada kuskurema me iyuwa ya koma kan wannan jawabin nasa yayi gyara kokuma ya warware abinda yashigewa duniya duhu. Wannan ...

'YAN MATAN ZAMANI GA SA'KO

  'YAN MATAN ZAMANI KO 'YAN SON ZUCIYA? A duk sanda naji mata na kukan wahalar samun miji, ko aurensu na yawan mutuwa nakan girgiza kai na wuce kawai, domin kuwa hausawa na cewa" kowa ya sayi rariya yasan zata zubar da ruwa." Da zaka ce musu laifinsu ke janyo musu wannan matsala, da yawansu inkari zasu yi, koda yake ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai wacce kaddara ke fadawa, akwai kuma wacce ta hadu da abokin zama bana gari ba, amma dai mafi yawa laifin daga wajen matan ne. Duk wacce tace maka bata sami miji ba, kace da ita bata sami wanda take so ba kawai, domin Allah ya jarrabi matan wannan lokaci da son auren maikudi wanda za'a dinga buga misali a cikin kawaye, mafi yawan matan dake kokawa da rashin samun miji akwai mazan dake zuwa da niyyar aurensu wanda suke ganin kamar ba ajinsu bane, ta sanadin hakan sai mace ta kusan tsufa a gidansu babu aure, wasu Allah kan tarfawa garinsu nono su sami irin mijin da suke son aura, amma sai zaman auran ya gagara ayi ...

MAJOR DA MUQARRABANSA AN KYAUTATA MUSU ZATO

ASHE SUNE SANADIN HADA BANGARORIN BOKO HARAM YAKI DA JUNA Jama'a ku nutsu ku karanta wannan bayanan da kyau Tsarki ya tabbata ga Allah, rikicin bangarorin kungiyar Boko Haram abin boye ya fara fitowa fili, marigayi shugaban sojoji Janar Ibrahim Attahiru da shugaban leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaro na rundinar sojin Nigeria marigayi Birgediya Janar Abdulrahman Kuliya sune sanadin haddasa tsoho da sabon rikici tsakanin 'yan Boko Haram wanda ake kyautata tsammanin Shekau yayi mushe A cikin wani sabon rahoto wanda jaridar PR Nigeria ta wallafa jaridar da take da kusanci da rundinar sojin Nigeria, tace marigayi Birgediya Janar Abdurrahman Kuliya shine yake jagorantar tawagar mayaka sojojin kundunbala a lokacin da marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru yake matsayin babban kwamandan rundinar Operation Lafiya Dole a Arewa maso gabashin Nigeria Kafin a cire shi, a lokacin wasu tawagar mayakan Boko Haram sun tuba sun mika kai wato sun yanke shawaran ajiye makamansa wa run...

RAYUWA ABAR TSORO CE

  *BABU UZRI BAYAN MUTUWA* -  "Duk wani uzrin da bawa yake ƙunshe dashi a lokacin rayuwarsa ne kaɗai yake da ikon aiwatar dashi, yana mutuwa shikenan uzri ya ƙare, abinda mutum ya shuka shi zai girba" - "Bayan mutuwarka a lokacin da aka ɗauke ka izuwa makwancin ka, komai yana jin abinda kake faɗa ga masu ɗaukar ka, amma saidai su mutanen da suka ɗauke ka ɗin basa taɓa jin abinda kake faɗa" - "Ya kai miskĩni! Lallai ka sani cewa fa, a lokacin da ka mutu shikenan taka ta ƙare, bayan an ɗauke ka acikin makara babu wanda yake fuskantar halin da kake ciki balle ya karɓi ƙorafinka, face dabbobi ko bishiyoyi, sai kuma ubangijin taliƙai, to ka gabatarwa da kanka wani alkhairi wanda ba za kayi nadama ba bayan mutuwarka"

TARBIYYA A SHARI'ANCE

 Gabatar da Tarbiyyar Musulunci Da sunan. Allah mai yawan Rahama mai yawan jinkai, bayan haka:Saninku ne iyaye, malaman makaranta, da masu damuwa da gyara da kuma ci gaban al’umma cewa Tarbiyya ita ce tubalin ginin dan adam, ko dai tubalin gini, ko kuma tubalin toka. Duk wata tarbiyya da ba ta musulunci ba, ko wadda ta ci karo da ita, to tubalin gininta na toka ne, ko ba jima, ko ba dade sunanta rushashshiya, tarbiyyar musulunci ita ce daki-bari, kadaura babbar inuwa, kowa ya rabe ta sai ya huta, ballantana wanda ya tashi a cikinta. TO (1)Me ake nufi da Tarbiyya a Musulunci? Tarbiyya a Musulunci tana nufin “Gina cikakken Mutum Sannu a hankali; don bin umarnin Allah da na manzonsa, da neman yardar Allah, da samar masa da nagarciyar rayuwa duniya da lahira, bisa tsari irin na musulunci” (2)Menene hukuncin gina yaro Akan tarbiyyar Musulunci? Gina yaro akan tarbiyyar musulunci wajibi ne, kuma hakki ne daga daga cikin hakkokin yaro akan maifansa (ko walliyansa)Dalilai akan Haka: 1. Daga...

GUZIRINMU AYAU

  MU LE'KA MAKABARTA )> . AWANNAN GURIN- Wasu Rahama Suke Sha, Wasu Kuma Dũkan Tsiya Suke Ci. . AWANNAN GURIN- Wasu Sun 'Kosa A Tashi Alqiyamah, Sabo da Ni'mar da Suka hango A Gidansu Na Aljannah. Wasu Kuma Roko Sukeyi Kada A Tashi Qiyamar Sabo da Azabar da Suka Hango Tafi Wacce Suke Ciki Bala'i, . AWANNAN GURIN- Mutanan Kirkin da Ke Cikinsa dana Banzan dake Cikinsa, Suna yin Nadamar Lokacin da Sukayi Hasarar Sa, . NA KIRKIN CUKINSU: Suna Yin Nadamar Ina ma Ace Gaba daya Lokutansu Sun Qarar dashi Akan Bautar Allah, Sabo da Sakamakon Alkairin Aikinsu da Suka fara Gani. . NA BANZANSU KUMA: Suna Yin iihu, da Kururuwa, da Cizon Yatsa, da Takaicin Qarar da Rayuwarsu da Sukayi Akan Aikin Banza. . NI, DA KAI AYANZU- Zãbi ya Rage Agremu, ga Irin Rayuwar da Muke Son yi Bayan Mutuwar Mu, . Ko dai Mu Zabi Rayuwar da Mala'iku Zasu yi ta Jibgan Mu, Kunamu da Macizai Suyi ta Saran Jikin Mu. Ko Kuma Mu Zabi Rayuwar da Zamu Samu Nishadi da Natsuwa Acikin Qabarin Mu. . Kada Dai...

NASIHOHINMU AYAU

 YADDA IYAYE ZASU MAGANCE MATSALAR DAUKE DAUKE DA YARA KEYI TIN SUNA QANANA NASIHA (2022) A Babi na Tarbiyya Duk Abin Da Yaronki Ya Dauka Idan Bai Tambayeki Ba Sannan Bake Kika Bashi Ba To Ya Ajiye Abin Kuma Idan Da Wani Yaro a Kusa Ki Dauka Ki Bashi Shi Yaronnaki Ya Haqura Sai Wani Lokacin Kuma Sannan Ki Tuhumeshi Dan Meyasa Na Aje Abuna Ka Dauka Baka Tambayeni Ba ? Ki Nuna Rashin Jin Dadinki Akan Hakan Sannan Ki Ladabtar Dashi . Hikimar Hakan Malaman Tarbiyya Sukace Don Kada Ya Tashi Da Wannan Dabi'ar Ta Dauke Dauken Kayan Mutane Basu Bashi Ba Wadda Idan Ya Ginu Akan Wannan Dabi'ar Idan Ba Kuyi Wasa Ba Sai Iyayensa Sun Zubar Da Hawaye Saboda Munin Dabi'ar Da Suka Gagara Datse Masa Ita Tin Yana Qarami  Jama'a Kun Fahimta............?RAYUWAR AURE BA HUTU DA JINDADI BANE KAWAI HAQURI YAFI YAWA NASIHA (2020) Karku Dauka Rayuwar Aure Hutune Zalla Da Jindadi a'a Duk Wadda Ya Fahimci Haka Toya Fahimci Lamarin a Baude Aure Ibadah Ne Da Kuma Haqurin Da Yakai Qololuwa Don A...