KAWA TAGARI

 KA KYAUTATA ZATO GA ALLAH!

-

"Rashin kyautata zato ga Allah ba ƙaramin sharri bane ga al'ummar musulmi, domin haƙiƙa hakan na iya haifarwa bawa saɓon mahaliccinsa Allah"

-

"Shi ɗan Adam gaggawa ke gareshi, kullum burinsa da zarar ya nemi abu, ya same shi nan take, da zarar ya samu jinkirin biyan buƙatarsa, sai kaji ya fara riya mummunan zato acikin zuciyarsa, kuma wannan lamarin har akan ubangijinsa yana riya hakan"

-

"Sau da yawa bayan kayi addu'a, ka roƙi Allah biyan buƙatar wani abu, a dalilin jinkirin amsuwar ibadar taka, sai kaji tamkar addu'ar taka bata amsu ba a gurin Allah buwayi, sai kaji tamkar ma ka haƙura ka ɗebe tsammani daga samun nasara a addu'ar taka, amma baka sani ba, Allah shine yasan daidai gareka, kuma yana amsa addu'ar bayinsa ta hanyoyi masu yawa, a kuma lokacin da yaso, sannan wani lokacin kuma abinda kake roƙonsa ɗin ba alkhairi bane gareka, sai ya sauya maka da mafi alkhairi gareka fiyeda abinda ka roƙeshi ɗin, to ka kasance mai kyautata zaton ka ga Allah, kuma kayi haƙuri abisa abinda kake nema a gareshi, lallai tabbas shi Allah baya taɓa tozarta masu nema daga gareshiƘAWA TAGARI ITACE ƘAWA.

-

"Zaki iya tara ƙawaye masu tarin yawa a rayuwarki, kuma ki kasance tamkar wacce bata da ƙawa matuƙar acikin ƙawayen naki babu guda ɗaya wacce zata dinga gyara miki kura-kurenki"

-

"Rayuwar ɗan adam dole sai da nasiha don gudun zamewa, matuƙar kuma akace mutum bai sami mai yi masa nasihar ba, to haƙiƙa zai gudanar da rayuwarsa ne cikin tafka kuskure"

-

"Zaki iya yin dace ki tara ƙawaye dubu a rayuwarki, amma sai kinyi babbar nasara ne sannan zaki sami guda ɗaya wacce za take ɗora ki akan hanyar daidai da zarar kinyi kuskure kin zame daga kan ɗabi'ar musulunci, ƙawa tagari itace ƙawa, ƙawa tagari itace mai ɗoraki akan hanya da zarar kin zame daga kan hanyar daidai kin bin ta kuskure"

Comments

Popular posts from this blog

7 throwback photos of President Muhammadu Buhari as young man who loved his family and job

10 most Religious Countries in the World by Perception

Read Why Muslims Wear White Ihram Clothing During Hajj Pilgrimage