KUSKUREN MAI AZUMI
KUSKUREN MAI AZUMIN SHAWWAL!!
-
"Babban kuskure ne gareka don kana yin azumin shawwal kazo cikin jama'a kana bayyanar musu dashi domin su yabeka, kaje cikinsu kana cewa wane kai ka fara naka azumin ne? To ni kuwa tuni ma na fara nawa, haƙiƙa wannan kafa ce wacce riya take iya shiga ciki, ba laifi bane don ka tunatar da wasu suyi wannan azumin, laifin anan shine kazo kana bayyanar dashi ga jama'a domin su yaba maka suna cewa kai na Allah ne, kayi ƙoƙari, kodai su yabe ka ta dukkanin hanyar da in an yabeka za kaji daɗi, to tabbas zaka iya sarayar da ladan azumin naka, idan kuma bakayi sa'a bama sai zunubi ya biyo bayan hakan"
-
"An sami ruwaya daga Abu Hurairata Allah ya ƙara masa yarda yace: lallai Manzon Allah ﷺ, yace: haƙiƙa Allah ta'ala yace: lallai nine mafi wadata daga shirkar masu shirka, duk wanda ya aikata wani abu ya haɗa ni da wani acikinsa, to zan barshi da shirkarsa"
أخرجه مسلم برقم (2985)
-
"Riya tana cinye ladan aiyukan bawa fiyeda yadda wuta take cinye karmami da zarar ta haura kansu, kayi a hankali da ladan azumin shawwal ɗinka, zaka iya gama shi ma ba tareda kowa ya san kayi shi ba, domin ai daman ladansa kake nema a gurin Allah buwayi, to menene naka sai ka bayyanarwa jama'a cewa kana yin azumin sittash shawwal?"
Comments