MUGUJI CIN BASHI
*ILLAR MUTUWA DA BASHI.*
-
"Hausawa sukance wai ai bashi hanji ne kuma yana cikin kowa, ni kuwa sai nace lallai wannan maganar hakane, amma kuma tana da illa ga cikin nasa matuƙar baiyi ƙoƙarin biya ba tun gabanin mutuwarsa"
-
"An sami ruwaya daga Abu Hurairata Allah ya ƙara masa yarda yace, lallai Manzon Allah ﷺ, yace: ran mumini tana rataye da bashin sa har sai an biya masa"
Sunan Ibn Majah (2413)
-
"Wato shi musulmi wani lokacin bashi yakan zama illa da kuma baranaza ga lahirarsa, bashi babbar masifa ce a gareshi, idan ya mutu da bashin wani a wuyansa, to haƙiƙa yana rataye ne da wannan bashin har sai sanda wani ya biya masa sannan za'a warware masa wannan ƙuƙumin bashin da ake binsa a duniya"
-
Comments